← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 114

Sashe 19

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 1 Ta dauki a kalla second ashirin tana kallonsa kafin ta bude gaban motar ta shiga ita kanta gabanta na faduwa kuma jikinta tamkar an zare mata laka, abu daya ne ta sani zata so ko a tarihin rayuwarta ta fadi ga yadda katangar makarantar yan hottest take Shiru ne ya dan ratsa mktar kafin ya kara kallonta ya shiga yi mata tambayoyi dangane da shin inda zasu ina dinta ne? Kwata kwata sai ta ki bashi gamsashiyar amsa, kai daga baya sai ta daina fahimtar mema yake fadi, ta afka tunanin hanyar cike da begen wajen a kasan zuciyarta Sun dauki lokaci sunna tafia a kadan sun kusan awa biyu har sai da ta fara tsarguwa gannin anguwar kamar sun fita daga gari kafin suke hawa wata shinfidadiyar kwalta Lumbuk take a saman hanyar, tamkar a yau aka yita domin sai walwali take, bata da tudu bata da rami rami a mike take ziryan A hankali suka hango wani gini mai tsayin gaske sai afkin camarori ta ko'ina, ga ginnin ba dai tsayi ba na andur ya dauki kalar gidin ruwan kasa lasho din A dan firgice ta kale shi jin ya ce" Wace hanya zamu bi kuma? " Karra kallonsa ta yi ta kuma maida dubanta wajen, a sanyaye ta nuna masa wajen muryarta na cracking ta ce" CiCiki zamu je " Karra kallonta ya yi ya ce" Ciki kuma? Ta yaya ? Ina Baje dinki ne?" Karra kura masa ido ta yi kamar yana mata yaren shainanci, Hannayensa ya watsa ya ce" ai in aiki kike a ciki kina da baje dinki na shiga, idan ba haka ba ai kin san ba zaki shiga ba ko? Ina fatan dai ba gannin wani bane kika zo dan bafa sa bari a shiga" Muneerath muryarta a sanyaye ainun ta ce" Yanzun sunna nan ciki? Da su din da masu basu horon harma da jiragen?" Birki ya ja a lokacin da suka kusa isa yana kallonta, sai ya fara yi mata wani kallo daban domin tambayarta ta bashi mamaki ainun da kuma shaku a kan kwakwaluwarta, waye bai san makarantar nan ba? Waye kuma zai yi tambayar idan har mutanen da masu basu horon na nan ciki? A hankali ya ce" Ina fata dai mai lafia na dauko ba ruwa biyu ba " Sai a lokacin ta dan gane abinda ta fada din, dan haka sai ta sakar masa dan murmushi ta ce" Dan Allah mu zagayeta mana makarantar mu ganta da kyau?" Fuskantarta ya yi da kyau ya ce" Yar budurwa, kin ga ko sunnanki ban sani ba, ni walahi kin yi min ne soyaya ce nake so mu yi da ke idan har ban takuraki ba, ina fatan kina fahimtar yarena?" Murmushi abin ya bata dan a yadda ya yi maganar zaka gane ya fara tsorata ne da ita, hakan ya sa ta masa murmushi na kirki kafin ta ce" Ka san meye, na jima ne ina son gannin makarantar nan, shine yau na samu mai kawo ni, bayan shi ba komai fa, dan Allah ka zagaya da ni sai mu zauna mu yi zancen fahimta da junna" Haka kawai ya ji ya yarda da ita dan haka ya kunna motar tasa ya tayar ya juya da ita a hankali sunna tafe tana kallon yannayin ginnin da irin camerar da ba'a yin doguwar tafia ba'a ga wata camerar ba A hankali ta kurawa wani waje ido, ba komai ya sakata kurawa wajen ido ba sai gannin wannan wayar mai kayoyin tsini a jikinta ta nan ta dagu sosai, kuma an yi wani irin katari da irin abin ginnin nan irin mai hawa hawa waje waje haka Kara kurawa wajen ido ta yi kafin ta ce" Dan tsaya a nan mu gani " Tsayawar ya yi kuwa yana kallon inda take kallo, sai gani ya yi ta bude ta fita daga motar Kara gyara zama ya yi yana bin bayanta da kallo a lokacin da ta juya ta nufi wajen katangar nan Kara gyara zamansa ya yi da kyau irin ya samu abin kallo din nan, sannan yana gannin irin yadda take ta aune aunenta shi dai bai kawo komai a ransa ba sai a lokacin da ya ga ta dauko wani busashen ice dan dogo haka sannan ta nufi wajen abubuwan nan kamar matatakala Dan kwalin kanta ta cire ta kara daure jakar dake bayanta a jikinta da kyau sannan ta kamo kasan rigar nata ta sakota ta tsakiya ta hade ta yarda cinyoyinta suka kusan bayana sosai ta daure su da kyau ta ci damara da shi sai ya yi kamar wandon indiyawan nan burkumeme Kara zubawa kwaurinta da wajen cinyarta da ya bayana ido ya yi lokaci daya yana shafa wajen kansa a hankali ya ce" Ke ko mahaukaciya ce zan yi manage, sai na auri biyu tashi daya da mai hankali da mai kayan kwonciyar hankali" Lokaci daya kuma ya shiga zarro idannuwansa sakamakon abin al'ajabin da idannuwansa suke gannin masa Da sauri ya bude motar a tsorace ya ce" Ke baki da hankali ne? Baki san sojoji ke gadin gidan nan ba idan fa suka zo harbe ki zasu yi kamar barauniya, sannan baki san karafunnan nan sunna hade da wutar lantarki bane? Yana taba ki fa sai dai gawarki a nan ko bakya ji ne?" Ya karashe da taratsun ihu gannin bata kula shi ba kara hawa take Bata kula shi ba da sauri ta kara kaimin hawan nata, wannan busashen icen ta saka ta shiga ture karfen nan, a firgice ta dan tsaya sakamakon kukan jiniyar da gaba daya wajen ya dauka sannan motocin da ta juya ta hango suka kara tsoratata, aman bata tunanin zata tsaya dan motocin nan da sauri ta karra ture shi sosai sannan ta haye saman katangar ta kuma juyowa tana kallon yadda dan saurayin buzun nan ke tafa hannu yana ta nuna masu yana magana aman cikin ikon Allah neman tsatsara shi da bindiga suke Da sauri ta zarro idannuwanta gannin an tsare shin sannan wani rufcece ya durfafo inda take da yaren freinch tun karfi yake fadin" Tsaya a inda kike, ki sauko ko na harbe ki!" Idannuwanta ta rintse cike da firgicin gannin kamar an zo kama gagarumin barawo ko za'a gabza yaki tsakanin yan boko haram da sojoji? Ihun da ake mata ya sakata rintse ido da baya baya ta juya ta shiga kokarin dirawa ta bayanta Da wani irin karfi suka kuma kwala kiran ta sauko hakan ya sa ta saki garun gaba daya tana ambatar Allah a ranta ta tafi ba tare da tunanin zata dira da ranta ko a mace ba Wani wahaltacen ihun ta saki a lokacin da ta ji wani irin abu shi ba wutar nepa ba shi ba wutar kiyama ba ya hade an jona mata a wajen wuyanta kiiiiiiiiii gaba dayanta karkarwa kafin ta zube kasa warwas tana wani irin abu tamkar ana jan wata jijiya a jikinta Ribom din dake kanta ne ya kwonce gashin kanta ya bayana mai baki sosai da kuma tsayi lumbuk da shi , ta kasa kasa take bin manyan takalman sojojin da suke nan tsaitsaye da kallo gaba daya kwakwaluwarta take jin zata tarwatse mata , bata taba jin azaba irin wannan ba, bata taba jin muguwar azaba irin ta yau ba, ta rantse da Allah ta saki fitsari mai zafin gaske dan bata san abinda ke jiranta kennan ba Bata shirya ba ta ji an kwasheta kiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii an saka a bayan motar nan sannan an kwace jakarta an saka abin detecten bom da dukan abu na cutarwa an tabatar babu a ciki sannan suka yi ciki da ita Tafia suka yi mai nisa kafin suke isawa office din nasu na bincike Kuma fitar da ita suka yi suka yi wani janta janta tafia tafia da ita suka kaita wani daki mai duhu suka jefata ciki suka rufo Da sauro ta dukunkune kanta cikin cinyoyinta gaba daya jikinta na bari ta kasa katabus sai karkarwa take kamar zata mutu A firgice ta dago kanta jin motso kamar a kusa da ita, Shiru ta yi sai kuma ta ji muryar namiji yana fadin" Walahaula wala kuwata ila bilahi yau me na aikata na dauko mahaukaciya yau na mutu na lalace Annata batama san na dauko motarta ba, wayo Allahna" Da sauri ta kai dubanta wajen duda duhun da dakin ya mamaye da shi , a hankali take ta ambaton sunnan Allah kafin da kyar ta ji wasu hawaye sunna fitowa ta cikin idannuwanta Wani dan haske ne ya bayana mai ruwan blue, wanda mutanen dake tsaye gaban Computer kama tun daga shugaban makarantar , da shugaban masu bada tsaron, da shugaba mai kare hakkin yara, da mai kare hakkin mata, da dai sauransu suka zubawa Alon madubin da ya raba dakin da inda suke sannan sunna sauraron amon muryoyin dake tashi Ido hudu Suka yi Muneerath da saurayin nan, da sauri ya ja baya cike da tsoron ganninta kafin da muryarsa sama sama ya ce" Ke wacece ke? Me na gaba maki da yau kika zabi shiga motata na kawo ki nan, cewa suke wai wa ya aiko ki dan girman Allah ki fada masu ni dai ban sanki ba a sakeni na tafi gidanmu wajen Annata" Ya karashe yana hade hannayensa yana fashewa da kuka tamkar ba shine dazun ya dauko yar mutane cike da shakiyanci da mugun nufin son samun lagonta dan ya far mata A tsorace itama take kallonsa kafin ta ce" Walahi walahi ni babu wanda y a turo ni, ka ga tun ina karamata burina na zama HOTTEST, ko a yau ni kaina ban yi tunanin zan shigo gidan nan, nama fa hakura da zama domin iyayena basu da halin biya min, kai ko kudin da zai kawoni nan ni bani da shi dan ka ce kana iya kawoni ne na biyoka muka zo, ashe haka gidan yake?" Da karfi ya ce" Kin kuwa kashe mu, wayo Allahna na shiga uku to kin san baku da halin biyan uban me ya kawo mu nan din? Gashi yanzun banma san a me suka dauke mu ba!" Kallon ogansu daya daga cikin masu bada tsaron ya yi
Chapter 19 · 0% Book details