Sashe 53
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
kasuwa, yaron dan nasu ne yake daga karfe dan rasin jin magana dama gashi gajere bashi da tsayi ga kuma daga karfe sai hannayensa suka yi wani irin jijiyoyi a tsaitsaye Tashin hankali irin na dan adam da baya gudun ta kife gaba daya sai Muneerath ta juyo ta sauke dubanta a kan fuskarsa dan baban abinda tas tantancewa shine idan bayan kansu iri daya ne da wadan gashi ne ke rufa masa asiri ko me,a daidai lokacin ne kuma abin ya tsaya ya bude .......a lokacin ne kuma ta sauke dubanta a kan sajensa da lebensa mai ja sosai..........haka kawai shari irin na zuciya sai ta kawo mata magana kama haka 'ji leben uwa na bakuwar karuwa'............. Daria ce ta kubce mata marar sauti aman kuma wace take daria domin dai du wanda ya kale ta dole zai ga daria ne take kafin lokaci daya ta gumtse dariar da take yi ta juya da sauri da nufin tafiarta kafin ya ci yan garinsu Bata san ta yaya ba, du irin saurin da ta kwasa sai ji ra yi ya damki hannunta a karrona biyu kennan ya juyata a lokacin da bata shiryawa hakan ba ya hade bayanta da jikin garun kofar dakin Mah kafin ya matsota matsewa irin ta gak da gak din nan yana mai bin color din dake cikin idonta dake yawo dan tsoro da firgici ya kasa tsayawa waje daya sai wulwulwul take kafin ta zarro ido sakamakon hannun nata da ya riko ya dago shi sama ya jinginar da shi a jikin kirjinta.....watau yau ita Muneerath yar gidan oga ce hannunta cikin na kato sannan a jingine a saman kirjinta wajen da mamanta suke, harma rabin hannun nasa na gigar cikinta........'Ta faru ta kare.............' a yanzu ta san babu mai rabata da abin kunya sai Allah, firgicin wannan ya sakata takarkarewa ta kwala ihun da ya saka Mah zabura ita da Iman suka yo waje domin ta dawo tana dakinta tare da Iman so take ta shiryasu tafi wajen likita duda Pah yace shi ba zai je ba Sunna fitowa basu ganta ba sai da Mah da sauri ta leka ta ganta kafin ta ga bayan Hanja , Muneerath a haukace take fadin" Wayo na shiga uku na lalace dama a hawai ya taba min hannu yanzu kuma ya rike min hannu a kusa da abin nan nawa Mah walahi shine, kur'ani shine innalilahi wa ina ilaihi raj'une dama idan ka ce kai zuwa zaka yi ka yi gaban kanka sai ka hadu da ikon Allah, yanzun idan oga ya gannni da katon ciki ina zan shiga da raina da gorinsu? Wayo Mah ki raba mu walahi daria ce ta kubce mini dan hannun nasa kamar ba na mutun ba shine ya ji haushi ya murde min hannuna haka ya shake ni a makarantarmu kuma ya shuna min zaki" ......Ikon Allah,walahi tunda mamansa ta haife shi kukan jirgi kawai ke masa ihu a kai kafin a saka yannayi na rashin ihu sai wannan yarinyar mai kama da mahaukata, Yanzu in ba rashin hankali ba shi zata kalla ta dare? To uban me ta gani a jikinsa?, Wai ta ganshi a accenseur ta shiga bata ko dar dar da shi? Kuma shine ta juyo ta fashe masa da daria, yanzun kuma tana cewa shine shine ya yi me? Shi fa yana ta kira kamar da wasa Mah ta ki daga masa waya ya saka shi zuwa gidan nan yau, idan ba dan wannan ba shi da ba wanda zai ganshi walahi shine wannan Bukekiyar ke neman haukata masa dodon kunne? Mah ta dora hannunta saman damtsen hannunsa zuciyarta cike da adu'ar Allah ya sa ra iya sasauta fushinsa dan har wata jijiya ta tsaya masa a gaban goshi a sanyaye ta ce" Khalb menene haka zaka ji mata ciwo fa kanwarka ce" Da sauri ya cika jikinta ransa a bace ya ce" Mah du kece,, du kece kika sa muka zo da ita gashi tana so ta hana min kwonciyar hankali, ni ban taba kai hannuna kan mace da nufin haka ba sai a kan yarinyar nan,ta bi ta adabeni sai da zuba min ido.....maida ita zan yi, ba zan iya ba idan ba haka ba kuwa karya mata wuya zan yi!" A tsorace ta yi bayan Mah gabanta na dukan tara tara a kasan zuciyarta tana alkawarin gabanan ba ita ba shi ko gaisuwa ba zasu kuma yi ba! Yana gama fada rai bace ya yi dakin Mah Daga Mah har Iman wani irin mamaki ne ke neman kashe su, kai ikon Allah bama iman da ta yi mutuwar tsaye cike da mamakin wannan lamarin, wai HANJA ne ke wannan fadan da haki dan wannan yar yarinyar ta tsankwale shi? Wai dama yana doguwar magana haka da rikicewa? Wai dama Hanja din da ta sani yana irin haka? Mah, Mah, Mah tama rasa me zara yi tunani, a hankali ta janyo hannun Muneerath tana kallonta da wani irin yannayi a hankali ta shafa gefen fuskarta a sanyaye ta ce" Ke tarihi ce, baba, Muneerath......ni na san ba banza ba kika shigo duniyata, Muneerath fada mini ta yaya hannunsa ya kai kan naki na farko da kuma na yanzu? Dan Allah daughterna ki fada min a nutse ta yadda zan gane komai kin ji?" Fiki fiki take da ido cike da tsoro tana kallon Mah da Iman kafin ta janye dan kwalinta daga kanta dan ji rake wani kaikayin eahala kamar mai kwarkwata ta shiga fadin " .................. Baban abin takaicin wasu gigitatun mazan shine ......basa son masu rarashinsu........su fa mataye masu haye masu ke kashe su, watau wasu mazan infa suke shan wahala a nan wahalarsu ke taruwa ta tsaya, da yawan wasu mazan sun fi so ki ja su a kada, ku kada aljihunsu, ki hauda masu hawan jinninsu, domin gani suke idan ba haka ba kikai masu gaskiya yawa ne, a tunaninsu a gaskiya mace bata mace sai idan ta ja su a kasa......a nan suke yarda cewar yes ke din wata hamshakiyarsu ce, giyarsu ce, lalumin zuciyarsu ce ........................ 11/14/21, 12:51 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*