← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 114

Sashe 10

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

6 Da kyar ta iya samun barcin da take son samu, da wuri wuri ta farka ta fada wanka , a gagauce ta gama shiryawa cikin shiga ta wani zumbulelen hijab mai ruwan madara ta dauki byro da convocation dinta na shiga aji da takardar shedar yar kasa ce ita da dan sauran cenjin da ya rage mata a jakarta ta makaranta Sauri take zubawa sosai domin a kafa take tafiar tana yi tana duba lokaci da kyar Allah ya taimaketa tana isowa ana ta kirate kirayen sunnate , harma an kirayi nata sunnan dan haka ta dakata a kofar ajin da zata gabatar da nata jarabawar sai da mai kiran ya gana kiran sunnan kowa sannan ya amshi convoction dinta ya duba sunnanta da number table dinta, gannin tana cikin wa'inda zasu shiga ya bata hanya ta shige Tunda ta shiga ta kurawa waje daya ido , gaba daya hankalinta take son kwontarwa a zaunen nan da take dan ta samu gabatar da jarabawarta cikin nutsuwa hakan ya sa ta shiga tunanin abinda zai sakata farin ciki, a sanyaye ta afka begen abin bege, cikin nutsuwa ta kama salati a kasan zuciyarta idannuwanta lumshe, a hankali take begen daha, dan aminatu sayadi, d'a ga abdulahi, sidi baban kasum, ya abul Ibrahim, shi dai Abul fatimatu zaharau, a hankali take dan motsa bakinta har wata dake bayanta ta dan tabota A hankali ta buda idannuwanta tana kallonta A sanyaye matar mai dauke da tsohon ciki sosai ta ce da ita" Kanwata lafia? " Kai ta gyada tana kallonta alamun eh lafia kalau Matar ta yi murmushi itama bata kuma ce mata komai ba Sunna haka aka fara shigowa sa takardun harabawar , Bayan malaman sun gama caje kowa da duba yannayin zama sun tabatar kowa na zaune a saman kujerarsa suka nuna masu camerar da aka saka dan su kula kowa ya yi aikinsa wannan rana bata kai ranar tsayuwa a gaban Allah ba aman itama kowa ya yi ta kansa ne, mulkin sabon shugaban kasarmu ya tsaya tsayin daka ya toshe dukan wata hanya ta sata a kasa komai kankantarta kuwa idan dubunka ta cika komai kusancinka da shi ba zai sasauta maka ba Takardun da aka raraba masu suka dukufa karantawa, sun fara ne da FRAN AIS dukan seri din da shi suka fara ba A ba D ba C domin shine yaren da kowa ke anfani da shi dan magana a makaranta watau school , shine yaren da nasariya ta kawo mana Tunda ta sada kanta kasa ta nutsu take rubutunta bata dago ba sai idan ta ji ta kage sosai take dan dagowa ta dan huta kadan sannan ta mayar da kan nata ta ci gaba da aikinta, lura da masu tsaron suka yi ita kanta bata damu da kallon wasu ba ya saka su yin cen ciki Cikin ikon Allah ba ita ta tashi daga zaunen da ta yi ba ko da ta kare ta ci gaba da biyawa sai bayan awa uku da mintunna kafin ta mike a hankali ta kai ta ajiye ta saka hannu a wajen saka hannu sannan ta fice a class din Tana fitowa ta nufi wajen masu siyar da abinci, dala arba'in ta bayar aka zuba mata dambu na dala talatin da biyar aka bata piyawata na biyar Cikin nutsuwa ta samu wajen zama ta kebe ta karya ta kora da ruwa, bata nemi komawa gida ba a nan ta zauna har ta shiga aji ta yi na yamma kafin ra kama hanyarta a kafarta ta koma gidansu .......................................... A ranakun nan da aka yi na jarabawa kwana biyar cif matar nan na hankalice da irin hankali da nutsuwar Muneerath, kasancewar ba wanda ya santa a ajin hakan ya sa lamarin dogari bai bayana ba har aka gama jarabawar lafia sannan suka je gida zaman jiran result A tsakanin ranar da jarabawar zata fito ta rasa gane kanta ita kanta, ta matsa da adu'a da tashin tsakiyar dare kamar yadda malaminsu ya basu adu'o'i tana fadawa Allah kan ya sa da rabonta a wannan jarabawa, kokari take, burinta ta wayi gari ta ga ta fado cikin masu sa'ar samun cin wannan jarabawa hakan ya sa take wuni da azumi sannan ta rike kafarta domin daga ita har kawar tata hankalinsu ba a waje daya yake a kwonce ba tunanin result ya saka su sun zama wasu shiru shiru da su sam basa iya anfanarwa kowa da komai bale kansu A yau kwana hudu kennan da gama exam dinsu kuma a yau suke tsaitsaye cirko cirko gaban manyan makarantar da suka zo daga wani garin dan gabatar da jarabawar sunna jiran jin sakamakonsu Idan ka dubi fuskar kowa a birkice take da tarin tsoro, ba mace ba namiji, ba mai kannanun shekarun ba datijo, sannan yawancinsu sun zo da masu rakiyarsu ne wasun iyayensu ne , wasun yayunsu ne, da wuya dai ka ga mutun shi daya kwal a irin wannan lokacin sai Muneerath kawai dake tsaye kafafuwanta na yi mata rawa A cikin zuciyarta maganar da ta rubuta ta shanye take maimaitawa kanta, kin ga Muneerath idan baki samu ba ba komai, haka Allah ya yi, kuma Dogari ba sai kina da BAC zai soki ba, kin ga muneerath ki kwontar da hankalinki burinki na son kasancewa HOTTEST ba dole a tashi daya zaki iya zama ba, idan kika jure a gabama sai ki ga an dace A hankali ta lumshe idannuwanta a lokacin da suka yi ido hudu da yayanta, tsayen yake shima kuma ya kurawa waje daya ido shima sakamakon yake jiran ji, 'Ko wa ya zo dubama?' Ta tambayi kanta a kasan zuciyarta sai kuma ta cire dubanta ta maida wajen masu fadin sakamakon a lokacin da suka fara bayanin sakamakon ta hanyar fadin adadin da suka fado Ecrit, da oral, da kuma adadin da basu samu ba A kashi dari 37% gaba daya suka samu , sauran nan sai dai su sake wata shekarar Nan fa ciki ya duri ruwa, iyayen yara da y'ayansu du suka shiga kama sunnan Allah, harta kiristocin sun rintse ido sunna tasu sallar "Wanda ya zo na farkon Centre, ya samu wannan kwali tare da mention TRES BIEN shine *ABDUL KARIM MUNEERATH*" Baban Jurry din ya fada wanda yake ba'adare ne, sai da ya fada ya dan saurari na kusa da shi da abinda yake fada masa kafin ya cenza maganar tasa cewa "TA MACE TA" (MACE CE DA YAREN ADARANCI), "TA Mace TA" A tsayen da take zata rantse da Allah a yau bata gane sunnanta ba, BAC jarabawa ce mai matukar wahala a kasar Niger, idan yaronka na yi kai hankalinka a tashe nasa a tashe, burinka ya samu jarabawar koda ita kadai dinta ne, ko a scnd grup ya fado akan yi maka barka bale idan ya fado a na farko, uwa uba ta zamana kaf school din ta dauke makin kowa, sai ita kanta ta kasa gaskatawa a lokacin da ake fada har ana maimaita sunnan a tsayen da take ta kasa wani motsin kirki bale ta iya gane da ita ake Da wani irin ihu ihu yayanta ya girgizata yana fadin" Ke muneerath kina ji kuwa? Kin samu fa" Idannuwanta da sukai mata nauyi ta lumshe da dukan karfinta ta bude a kansa, da kyar ta budi bakinta ta ce" Da gask........" Bata idasa fada ba ta tafi luuuuuuuuuuuuuu gaba dayanta zata jirkice kasa aka kakamata aka riketa cikin yan kamatan harda mai cikin nan kafin sojojin dake tsaye suka karaso suka amsheta suka nufi asibiti da ita da yayan nata domin sunna wajen ne dama dan hanna fada da dauke masu sume sume da matsar da masu ihun kuka Mai cikin nan ce ta mikawa yayan Muneerath wata yar farar takarda ta ce da shi" Dan Allah ka bata ta taboni idan ta ji sauki " Shi dai amsa ya yi ya soke a aljihunsa ya shige wuleliyar motarsu suka yi asibitin yana cike da jin dadin abinda ta samun, daga ball yake ya ce bara dai ya tsaya ya ga in da gaske karatun take, a rayuwarsa yana son karantun boko kamar me, shi yasa yake dan shiri da ita a gidansu, ba wani uwarsu daya ba uba ne kawai daya aman shi ba ruwansa ko wanda basu hada komai da shi ba idan ya ga mai ra'ayin karatu ne sukan dinke abinsu sunna shiri sosai Sunna isa aka amsheta bayan sun yi bayanin komai suka so ya bada number iyayensu, budar bakinsa sai ya nuna marainiya ce shi kadai ya rage mata, ba dan komai ba sai dan ya san idan ya bada din ba wanda zai zo ciki kuwa har mamanta domin shi kansa shaida ne ya sha jin sunna shewar wai ita ce ke yin bac ko wa zai bata? Dan haka sai ya ki badawa kawai ya zauna da ita aka shigar da ita wajen mararsa lafia dan a bata taimakon gagawa kasancewar asibitin gwamnati ce aka kawota ........................................ . Zaune suke su su uku, likitoci ne manya domin su dukansu doctarori ne, tataunawarsu ne suke cikin hira da raha kamar aminan junna , aiki suke sunna shiri tsakaninsu, kasancewar babu emergency ya sa suke zaunensu sunna hirarsu hankali kwonce Macen dake zaune itama doctern ce mai sunna Halima ta ce" To yanzu Moise kai ka yi hakurin ka aureta mana, kar ka ce dan ta kiya da farko yanzu ta dawo zaka kiya kaima" Moise din ya yi daria, da ganninsa Bashi da adinnin musulunci a tare da shi, bakinsa ya buda ya ce" Kya ji ki da wani lalatacen magana nan niya, ji ke an ce da ke ni din Doguwa ta min baki na da zan yarda mu koma da wancen makirar yarinya? Ni ai ba dan shagiya bana bale na yarda, ta je ta amri wanda taka so lumui nima na samo tawa lumui na amre abina mu yi zamanmu, ke ni nan da kika ganeni bana kara yarda da waral matata, zan samo bak'ata mu jesu zuwa mu yi amrenmu dan na gane wararen tunaninsu halitar na aljana aka zuba masu suke daga kawuna da su" Ba'adare kennan, cikin hausarsa ta adarawa ( *Ki ji wani banzan zance a nan wajen, an ce da
Chapter 10 · 0% Book details