← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 114

Sashe 90

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

5 Da sauri Muneerath ta zarro idannuwanta tana saurare da sauri ta gyara tsayuwarta tana karra nutsuwa Pah ya fuskance shi a dake ya ce" Dan ni na haifeka, kuma dan na isa da kai, haka kuma dan kai din SARKIN kasata ce ya zama dole ka dauki mulkinka!" Wani irin duka ya kaiwa kofar dake bude hakan ya sa ta bada wani kara mai karfin gaske muryarsa a kausashen nan ya ce" Kamar dole nake karanta a furucinka PAH! Me maganar da na karanta a page na Facebook din Royal Familly cewar ni HANJA na ajiye tukin jirgi baki daya?" Pah ya kuma Fuskantarsa shima da nasa jinnin dake gudu a jikinsa da kuma karfin hali da sannin cewa hakan na iya faruwa dama ya shiryawa hakan ya ce" Eh dole ne kake karanta, kuma ya zama dole ka bar bauta wa kasa ta wannan fannin ka kama naka bautar da Allah ya haliceka dominsa!, Lion u'r a king!, Plz ka yi aiki irin na saraki!" Gaban goshinsa ya dafe ya yi tafia baya kadan ya dawo gaba kadan Hannayensa ya hade ya jimke yana kallon mahaifinsa, fuskarsa ta yi ja hakama idannuwansa, hannayensa du sun tada jijiyoyi irin na bacin rai hakama gaban goshinsa ya tada wani irin jijiya dake bugawa dal dal dal muryarsa a cinkushe ya ce" Abui, ka sani daraja na mahaifina kake, hakan ba yana nufin zaka ringa min irin haka ba!, Ka dauke min ita dan ka hasala ni, ka nesantata da ni dan ka birkita ni, shin dan Allah ya baka dama a kaina ta uba shine kake son halaka ni?, A yanzu ka saka ni shiga abinda bana ra'ayi, sarauta ka ba dan uwanka mana? Idan yana so ya kona kasar matsalarsa ce muna iya bara masa kasar!, Shine zaka yi magana da sunnana kan cewa ni ne na yi wannan d cision din?, Sannan ka saka a rufe min kofa ina ihun a bude min sun labe banma gansu ba bale su bude min?, Plz tell me so kake ka ga na fadi kasa?, Tell me so kake ka halakani?" Pah ya lumshe idannuwansa shima da suka yi jan ya shiga fadin" Yaya kake magana kamar wanda yake aiki da son zuciya?, Yaya kake aiki da kalamai irin na jarumi bayan ka sako son zuciyarka gaba da komai?, Kana min maganar ya kona kasar watau idan na bara masa kasar ya gyarata ko ya konata baka da damuwa da hakan bayan kai shaida ne konatan shine abu mafi sauki da zai aikata daga bakin lokacin da zai wayi gari ba ni ba bayana?, Yaya kake acting kamar wani mai karfi kamar wani mai juriya bayan ka kasa fuskantar barazanar rayuwarka nutsuwarka duniyarka ka iya janyota ka ganar da ita halin da kake ciki?, Yaya kake son min rashin kunya bayan ni ubanka ne kuma ban baka tarbiya irin ta mai jan kunne ba duda na kasance mai jan kunnen?, HANJA ya zama dole ka hau kujerarka!" Da karfin Murya HANJA ya budi baki ya ce" Ban zan hau ba!, Abui ba zan hau ba!" A hankali juwa na kwasarta, cikinta na murda mata ba ji ba ganni da wani irin karfi, numfashinta na dauke mata tana janyo shi da karfi da kyar ta iya karasowa tsakaninsu mayafin abayarta na faduwa daga jikinta, zufa ta wanke mata gaban jiki, jikinta yai mata nauyi sosai da kyar ta iya budar baki cen ciki tana rike rigar Pah da dayan hannunta da dayan tana son kamo hannun Hanja domin a kusa da kusa suke sosai tana fadin" Please, i bg u da sunnan mahalincinmu plz ku saurara min haka, dan Allah ku daina fada a tsakaninku, Khalb nd Habiby ku....................." luuuuuuuuuuuuuuu ta tafi gaba dayanta ta fadi a kasa domin a tsakanin su biyun ba wanda ya kawowa ransa cewa kokarin shiga tsakaninsu da take ba dan ta raba su kawai bane , a cikinsu ba wanda ya san cewa a yau tun safe tana dan fama da ciwon cikinta A cikinsu babu wanda ya gane halin da take ciki wanda suke ciki ya fi dauke masu hankali har sai da ta kai kasa kan cikinta da goshinta gaba daya da karfi ta yi wata muguwar faduwa ya saka su juyowa a firgice inda wayar dake hannunta ta silale ta fadi kasa daidai lokacin da Muneerath ta rintse ido sakamakon jin karar faduwar wayar sai jin muryoyin dakarun mazajen da suke fada tamkar zasu ciji junna sun shiga kiran sunnan mace daya kwal dake saka su nishadin rayuwa cikin ihun murya inda daya ya ce" ALEESA!," dayan kuwa ya furta " MAMAH" A DAKE KUMA TA JI WANI RATS RATS RATS sakamakon saukar kafar daya a cikinsu a kan wayar sai daukewar kiran ya biyo baya wanda ya sakata sakin tata wayar daga tsayen da take ta fadi kasa lokaci daya tana jin wani irin faduwar gaba da ya ziyarceta wanda ta ji wata irin juwa ta kwasheta ta aniya yin luuuuuuu zata kifa da sauri Mahaifiyarta ta tarota tana ambatar sunnan Allah da sunnanta tana girgizata da tambayar meye menene ya faru? Duka a firgice hakama kawarta aminiyarta a rude ta dauki wayarta ta shiga maida kiran aman cikin ikon Allah a swt offf take amsa amo hakan ya karra rikita su domin kuka ne ta saka ta shiga fadin ta tabata wani mugun abu ya faru, kuma a kan Mah ya faru, kar dai a je ciwonta ne? Ko kuma fadansu ya saka ta summa ? Sosai yamnayin da ta shiga ya ba mahaifiyarta mamaki sannan ta dauki soyayar da yarta ke yiwa matar nan da girma da mahinmanci A saman kujera suka taimaka mata ta zauna gaba daya jikinta na wani irin rawa na tsoro da firgici, Gaba daya sai ta ji idan ba ganninta ta yi a Palace ba ba zata iya samun nutsuwa ba, harma ta furta hakan inda mahaifiyarta da mamaki ta ce" Muneerath, Ingila fa kika ce?, Waye zai baki damar zuwa Ingila a yanzunnnan ke kuwa?, Awani ake yi na tafia fa, bayan wannan duda kin ce kina da Visa kuma ke din Hostesss ce ai ba koda yaushe ake da jirgin tafia Ingila ba, sannan ni gaskiya kin ga aikin nan naki har yanzu ba wai na yarda da zan iya barinki komawa bane, kuma ba zan iya barinki tafia Ingila ke kadai ba, me zai hanna ki yi ta yi mata adu'a na tabata koma menene zasu kire ki domin da alama su dinma sun damu da ke tunda har MATAR ta kiraye ki" Daidai Oga ya shigo kennan daga anguwa da manyan kayansa ya karaso yana kallonta yana son tambayar lafia ita kuma wannan?, Sai ya ji Munnerath din ta riko hannun Mamanta ta ce" Mamanmu, dan Allah ki bani dama na je na gani ko zamu samu jirgin da zai tashin, dan Allah mamanmu ki taimakeni kar zuciyara ta buga, walahi na san yanzu sunna cen wani abin ne ya faru dan Allah ki bani dama mamanmu idan akoy jirgin sai mu tafi tare gaba daya har ke harma Oga idan kina so, akoy kudi a acct dina kuma ina da damar gayatar du wanda nake so domin takardar yar kasa ce da ni, ina da alfarma na masarautar Ingilar, ina iya kai tsaye na sa a min takardar gayata na je da ku" Saudat dake ta gwada kiran layin ne ta shiga kiran layin sir Attahir Ringin take ta yi aman bai daga ba hakan ya sa ta dauko wayarta ta shiga kiransa da wayarta domin bata san me ya hada shi da Muneerath ba kwana biyu kennan ba kabarinsa kwata kwata Ta ci sa'a ya daga, hakan ya sa a dan gagauce ta shiga sanar masa cewa Muneerath ce na waya da Mah ta ji alamun kamar wani abu ya samu Mah din ko Sir Hanja, shine gatannan tana ta kuka wai ko zata samu jirgin da zai tashi to Ingila?, Walahi muma muna jin alamun ba ma dadi bane ka san kuma irin karamcin da sukai mata shine nace bara na tambaya ko akoy damar hakan?" Sir ATTAHIR ya lumshe idannuwansa cike da jin wani abin da yake ta yaki da shi kwana biyun nan dan ya nisanta kansa da ita , da kyar ya iya hadiye abin yana sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Subahannalah to ta kirayi number HANJA din mana ba sai ta ji ba idan bata samun Mah din, bayan wannan baki san tana da damar sakawa a tashi da jirgi da ita ba koda kuwa ita daya ce? In dai akoy jirage a kasa ko na wata kasar ne tana da wannan damar ku je a roport din kawai bara na yi kira na daidaita maku komai" Da sauri Muneerath ta mike jin abinda ya fada, ta kai dubanta kan iyayenta da mamaki ke neman kashe su Oga ya ce" Wai tsaya Jirgi fa na ji an ce?, Ingila dai ingila ko wani gari ne ake yiwa kiranyen nan?, Shi wannan din da kuka yi maganar da shi waye shi?, Kuma waye Hanja da Mah?" Maman su Muneerath ta girgiza kanta tana kallon Muneerath din da ta matso da sauri ta rike hannunsa tsakaninta da Allah kuka take tana fada masa cewar su din iyaye ne a wajenta , Hanja kuwa tamkar yaya yake a wajenta Baki ta tabe ta ce" Ya damu da sannin me hakan yake ciki ko kin ga alamun ya damu da damuwar wani ne a duniya bayan tasa?" Oga ya ce" idan kuwa kina jin tsoron Allah ba zaki ce ni oga ban damu da kamarin yar oga ba, koda na yi rashin damuwa da rayuwar wani banda ta yar oga, ki ci gaba da min irin wulakancin nan, duniya ce" Da sauri mamansu ta ce" In sha Allah alkhairin duniya zan tainta na kuma gama da ita lafia tunda ban cuci dan kowa ba!" Da sauri Muneerath ta fashe masu da kuka ta ce" Dan girman Allah kar ku yi, yau dai kar ku yi fadan nan, ku taimake ni ku raka ni, idan bakwa zuwa ku bani dama na je na gani, walahi ina cen ta yi rashin lafiyar da ta daga hankalin kowa har
Chapter 90 · 0% Book details