Sashe 114
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
masa a dukan yinkurinsa, dan Adam yana da daraja ko wanene.......da wannan nake da burin Allaah ya dafa mani mu kasance a sauratar mulkin HANJA" Tafi aka kwasa hakan ya saka Muneerath kara wangale baki da mamakin shikenan hala?, To kuma shikenan su sun gamsu?, Murmushi ta yi itama ta tafa dan kuwa ta gama yarda jan mutun na yarda da kalaman baki ba tare da an gita masa rantsuwa ba, ba kuma sai an nuna masa alkur'ani ba, haka kawai sai mutun ya ce da kai ya rantse da kan babansa ka yarda Sosai ya ringa gaisawa da manyan kasar sunna masa barka, sai dai sam bai basu damar su kai kansu wajen matarsa ba, domin a yanzu baya jin in har zai iya hakura yana kallo wani ya rungumar masa hannun mata ko ya nemi hade kirjinsa da nata, sai a yanzu yake gannin lalle Pah yanaa gaskiya, a da sai ya ringa gannin kamar PAH din na wani irin abinda bai dace ba, aman a yanzu sai ya samu kansa dumu dumu da gudun hakan wa iyalinsa Sun dauki dan lokaci kafin su nufi gida a mota daya gaba dayansu, inda HANJA ke rike da hannun Muneerath yana dan shafawa a hankali haka kuma gefensa na hagu Mah zaune cikin kyakyawar shigarta ta abaya baka sidik mai kyan gaske marar kyalkyali A hankali Mah ta ce" Son, sai nake gannin kamar kana abu irin na mai kishi bayan kai ka ce ka waye baka san kishi ba" Da farko yi ya yi kamar bai jita ba, sai kuma ya yi dan murmushi kasa kasa ya ce" A da ban san menene so din ba, haka kuma ban san darajarsa ba, a yanzu kuma bana jin zan iya kawar da ido a kan matata Mah, ina sontaa kuma ina kisshinta sosai" Ko da suka isa gidan wata tarbar suka samu Sai dai a yanzu kiri kiri Muneerath ta kalli HANJA a lokacin da ta kula da irin kallon da Iman ke masa ta ji wani irin abu na mata yawo a kai kamar zata hau bori da kakausar murya kasa kasa ta ce" Walahi ba gaisuwar larabawa ba, ko ta su waye kar ka yi da mataan dake wajen nan, ka ga karma ka rike hannayensu HANJA, idan kuwa ka yi in ban je na gaishe da wancen bodyguard din naka ta hanyar rungumeshi ba ni ba yar oga bace, ai gaisuwa ce ka yi na yi kawai" Dan bakin nata da take maganar tana murmushi chau chau da shi ya kurawa ido kafin ya dago ya kafe sauran matayen dake masa oyoyo sunna jiran lamari na runguma ga kuma abinda mai shi din ta fada Sai kawai ya hade hannayensa da nata ya yi mata murmushi ya ce" Na zabi kowa kar ya yi, dan bana son farkon fara aikina na ba Tgr naman mutun ta ci, wannan ba adalci bane" Sai da gabanta ya fadi ta kale shi a zabure ta ce" Tgr, tana ina? Hala da kai take barci? Ni walahi ba zan iya kwonci da ita ba, idan kuma mukaa raba daki ai abin wancen fa da muke yi fa?" Daria ta kubuce masa har ya so ya kasa hanna kansa kokarin rukunkumeta , sai dai gannin da gaske yake ta tsere gefen Mah ta kama kujerar Mah tana dan turata sukai ciki ta barshi da bakinsa _______________________________________ Sarauta yake yi da nasa salon da tsare tsarensa cikin aminci da kwonciyar hankali inda mahaifinsa ke gefensa yana taimaka masa da dukan abubuwan bukata, Mah dinsa na gefe tana karra talafa masa da shawarwari da adu'a, sannan matarsa na gabansa tana bashi dukan kulawar da ta dace Karra kame kansa da yi , ya daina harkar biye biyen mata sai ya karra wanzar da lamari na shayi, da tsoron haye masa, harma da yawa kan masa ikirari da sunna *DUTSE AJIYAR ALLAH, KA FI KARFIN GARA* Iman ta kama kanta, ta kwatanta har ciwo ta yi sai dai fahimtar da ta yi ba yarenta yake ganewa ba, matarsa kuwa ta mayar da ita taamkar mahaukaciya domin har tsokanarta take tana kuma bata tsoron cewa zafa ta fada masa ita ta fada mata maganar mata, sai kwata kwata ta nemi danganaa ta yafawa kanta harma ta fara ba samari damar zuwa wajenta dan ta fitar da gwaninta tunda zamtowa sarauniyar ingila ya gagareta kiri da muzu Tashin hankali aka sha na rigimar aikinta Sosai ta tayarwa da kowa hankali har sai da aka sadata da Oga da Mamanta inda Oga ya ja doguwar rantsuwa ya dire kan cewa idan ta tagawa sarki hankali a kan rabe raben kayan abinci a cikin jirgi in ba sai ya biya jirgi da aljihunsa ba ya zo ya ci yan garin babarta ba Allah ya sa kar ya ci zaben zama mai anguwar anguwarsa da yake nema, idan kuma wasa take gannin yake ga babarta ta fada mata Ai kam mamantamaa maimakun ta saurareta sai ta rufe ido ta dora daga inda ya tsaya ta ce bataa cikin wannan shirme, Gannin dai zasu karra rikita masa abarsa bayan rarashinta yake, lalabat yake kamar kwai,, domin tunda Mah ta kwatanta masa ba ita daya bace haka kuma kar a yi ta sani dana kar ta hanna kanta sukuni duba da haki zanen rai sai ya mayar da ita abu mai darajar daa ya fi tatalawa fiye da komai a duniyarsa,, baya wasa da laamarin yar Oga, baya wasa da soyayar yar oga , itace ta farko kuma yana fatan ta birne shi Dan haka ya riko abinsa ya rungume a jikinsa sosai a sanyaye ya ce" Kin ga aiki ne da ni a nan, idan na ce zan bari na bijirewa Pah na koma tukin jirgi yaya kike so na gama da duniya ne? Ko har yanzu bakya sona bakya so na gama da duniya lafia ne?" Da sauri ta girgiza kanta tana karraa cusa kanta a wajen wuyansa a sanyaye ta ce" Hanja ina sonka fa " Idannuwansa ya lumshe dan jin dadin kalamanta, ta sha fada masa aman idan yana aikata mata aiki mai lada, a haka garas sai dai idan kubce mata maganar ta yi, A hankali ya ce" Muneerath ina son ki sosai" Dan murmushi ta yi a hankali ta ce" Shikenan ba zan kuma aikina ba?" Yana shafa mararta yana karasawa kusa da gadonsu ya dan haya sama da hannunsa wajen abinda yake son cinma ya dan shiga lailaya a hankali ya ce" Zaki yi, idan kina tafia da mijinki sai ki bani ruwa na sha, ki bani abinci na ci, sannan ki dafan bujenki........" Da sauri ta rufe masa baki tana jansa saman gadon suka fada da karfi sannan ta ja masu labulen jikin bed dinsu gannin ina tata son lekawa Daga wannan na kawo karshen labarina mai sunna DUTSE a page 70 Alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah *YAH ALLAH KA YAFE MIN KURA KUREN DAKE CIKINSA, KA BANI LADAN DAKE CIKINSA ALLAHNA* DUKAN MAI SON CI GABA DA KARANTA LABARAINA YA GARZAYO YA BIYA KUDIN NASA WATAU *WATA KOKOWAR* A NAIRA DARI BIYU KACAL TA HANYAR YIN TRENSFER KO TURO KATIN MTN IN SHA ALLAH GA NUMBER NAWA 93811618 SAJIDA Times New Roman Times New Roman !%),.:;>?]} $([{ SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office feb552545ac147cc990c126f9a7baf37