← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 114

Sashe 105

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
6
Ba EDDITING
Da gagawa ya fito ya shiga mota aka kai shi
A lokacin da ya shiga docter ce ta tarbo shi tana farin ciki ta masa jagora ba tare da ta ce da shi komai ba
A lokacin da suka shiga suka tsaya a gaban gadon Mah tana kwonce ne, sai dai ba irin kwoncin da yake tardota kulun ba
A hankali ya ce" me yake saka ki farin ciki Docter?"
Likitar ta ce" Ta motsa kafarta da hannunta, ta buda idannuwanta harma mun cire mata abin bugun zuciyar "
Da wanin irin farin ciki ya karasa kusa da gadon a hankali ya duka ya dora hannunsa a saman nata ya jimke ba da karfi ba
Muryarsa a sanyaye yake fadin" Ki farka kin ji? Ki farka ki tarbi sarakuwarki da kanki, zan je a daura auren yaronki, ina so idan ya zo da matarsa rungume a jikinsa kema na rungume ki mu kwonta tare mu yi barci cikin nutsuwa, na so ma tura wani daurin aurensa, sai gashi Allah ya nuna min koda bana nan idan Allah ya yi zaki tashi zaki tashin ne, plz ki yi kokari kin ji? Ki kara kokari a kan wanda kike yi, ki tashi na fa hasken farin idannuwanki khalb"
Doctern waje ta fita cike da shaukinsu a zuciyarta, haka kuma zuciyarta cike da farin cikin kotsawar Mah
Pah bai kama hanya ba sai da ya tabatar tsaro ya wadaci wajen Mah haka kuma kula ta wadaceta, sannan ya umarta cewar bayan awa biyu da tafiyarsa a bada sanarwar za'a daura auren HANJA da matarsa Muneerath a africa kasar niger a yau, sannan a yada a social media
Tunda sakon Oga ya samu mama take zaune a tsakar gida bayan dawowarsu daga asibiti ta yi shiru tana kallon ikon Allah da kuma jiran gannin ikon Allah
Kasa kasa ya yi maganar cewa za'a daura auren Muneerath, bai bata damar fahimtarsa ba ya katse kiran, ga kuma Muneerath din da suka dawo daga asibiti da ita a falo a kwonce idannuwanta rufe ba irin yadda Saudat bata yi ba kan ta yi magana ta ki ta yi karshema sai ta shiga alamu na barci take yi bayan idannuwanta biyu,
Haka Hanja har cikin falon ya kaita a hannunsa a rungume ya shinfideta kafin yake tafia gida sarki bisa kira da ya samu wanda ya tafi da gagawa inda ahalin gidan da na anguwar suka samu damar sintiri sunna son gane me ake ciki ne wai?
Iyalan gidan kam sun yi fadan, sun yi masifar, sun yi yafe yaden maganar sun dawo yar zurru sunna kallon kallo kowa da abinda yake cikin cikinsa kuma yake son a bashi amsa aman maman Muneerath ta masu kunnen uwar shegu ta ba mahaukata ajiyarsu, hakama yayanta da ya zo gefe suka koma da mamanta ta masa bayanin abinda yake faruwa ya samu kansa da mata kallon anya kuwa tana da tabacin abinda take fada? Dan haka sai kawai ya garzaya ya nufi gidan sarkin duda ya san abu ne mai wahala a barshi ya shiga
Sai dai tun daga nesa ya ringa fara harda da magana
r gannin irin taron al'umar da suka cike wajen , domin Sarki kamar jira yake ya yi gangami na mamaki, ya tara al'uma ta mamaki, ya cika wajen da abin mamaki inda aka baza tsaro aka shiga yanke yanke kamar cen dama an shiryawa wannan daurin aure, jama'a kuwa suka ce gasunnan ta ko'ina ba ji ba gani inda cen ciki kuma Sarki ya gama yiwa HANJA bayanin komai a nutse wanda abin ya nemi buga zuciyarsa dan a ba zata ya zo masa
Du irin kuncin da zuciyarsa ke ciki da ihun da Muneerath ta masa cewar zuwa ya yi ya kasheta? Zuwa ya yi ya yi wasa da zuciyarta? Me ta masa? Me ta tsare masa? Zuwa ya yi ya wulakantata dan ya ga ita ba kowa bace? Zuwa ya yi itama ya ga karshen tata rayuwar shine ya bilo mata da maganar soyaya? Ya daina taba ta, ya taimaketa ya daina kallonta, bata tunanin zata iya yarda cewar wai shi HANJA dan wane jikan wane zai diro kasarta da yake kyankyami, da ita kanta da yake yiwa kallon mahaukaciya ya ce wai yana sonta, du yan matan nan na kasarsu? Du yan matan nan na duniya? Babu inda zai saka kafa ya nemi mace a hanna masa , shine zai so har Oga?, Shin bai san Iman na sonsa bane? Dalilin son da fake masa ta tsaneta kamar ta kasheta har take fada mata yana taraya da wasu mata? Yanzu shi da baya jin tsoron Allah yake so su jona da ita ko me? Dan Allah ya rufa mata asiri ya barta ta iya da rayuwarta , kar ya hargitsa mata tunani, walahi ya fi karfinta..........
Sosai magangannunta suka rikita shi, har ya ji mamakin wai shi HANJA iman ke so? Lalle ya wulakanta kansa har ta kai yadda Iman ke tunanin ta kai macen da zai iya raba lokacinsa da ita? Lalle zina zubar da mutunci ce, yanzu yarinyar da yake yiwa kallon kanwa dan ta san ya kasance mai raba abin cikin wandonsa har ta kwadaitawa ranta? Shi ya tabata yarinyar nan karyata ne zai yi biyu ya zubawa tgr ta cinye kashin dake tare da fatarta sakamakon fadawa Muneerath sirinsa da ta yi kai tsaye
Ko daukotan nan da ya yi da farko wutsil wutsil ta fara kan ya sauke , da ya rungumeta kam a kunnenta ya rada mata cewa idan bata nutsu ba yana iya ladaftar da ita walahi
Shine fa ta yi luf a kirjinsa dan tana tsoron ya kuma furta mata kalmar so ya kara summar da ita, ita kam ta shiga uku ta lalace ta ga rayuwa gannin idannuwanta
Matsanancin farin ciki, da matsananciyar damuwa ne suka dirar masa harma ya kasa daukan tufafin da aka gabatar masa da rawani da sarkin sawanin da zai nada masa duda irin zumudin da yake kan ta ganshi da rawani yaya zasu kwashe? Tsoron rashin amsarta wa soyayarsa ya saka shi a gaba ainun harma ya fi damuwa da hakan fiye da komai
Shi dai ya san daurin auren nan daga Allah ne, damuwarsa yaya zai iya da rigimarta ne? Aman idan ya tuna ana daura aure ta zama tashi fa, shikenan bashi da wata damuwa ta kar a kwace masa ita, sai ya samu kwarin gwuiwa, a haka har Pah ya samu karasowa tare da dakarunsa shima inda duniya ta dauka ana ta neman hanyar da za'a yi magana da su abin ya gagara domin ba halin daga waya
Irin gaisuwar da suka saba suka yi da junna, a hankali Pah ya dan bubuga bayansa ya furta" Wani irin farin ciki kake ciki?"
Iskar bakinsa ya furzar ya furta" Da na fada mata ina sonta summa ta yi"..
Ido Pah ya zarro yana kallonsa , sai kuma ya yi dan murmushi a nutse ya ce" A haka za'a daura aurenka da shigar da ka zo da ita?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Baka fahimta bane? Inaga fa bata so na"
Pah ya yi dan murmushi ya ce" To sai ka koya mata sonka, ka san dai ba zan taso na baro matata kwonce na zo dan halartar wannan daurin auren ba kuma na koma ba'a daura ba dan kawai yarona ya kasa tankwasa zuciyar matarsa?, Fushi take da kai dan kana kula wasu matan , tuni a nan kana da maki mai girman gaske, kaine zaka tankwasata ta gane cewar sai da kai fa zata kai labari..........."
Kwarin gwuiwa ne ya same shi da nutsuwar zuciya, hakan ya sa ya sauke ajiyar zuciya ya bi bayan mahaifinsa yana karra wayar kansa da al'adun namu kasar, watau kasata mai albarka
Gari da yar ciki ce farare kal, basu sha wani muhun aiki ba so simple sai dai mai tsari
Bayan ya saka an gyara masa hannayen aka zo aka nada masa nadin Rawanin da aka bata lokaci ana yi har sai da ya gama gajiya da tsayar da kai waje daya inda Pah ke gefensa cike da kauna da shauki hakama mutanen da suke da damar hakan sunna gefensu, Attahir na daukan vidion dukan abinda ke faruwa har aka gama sannan ya mike tsaye
Sarki ne da kansa ya fara furta" MASHA ALLAH, ALLAH YA JA DA RAN SARKI HANJA MUHAMAD, ALLAH YA TAIMAKI SARKI YA KARE"
ai kam du suka shiga maimaitawa hakan ya saka Pah kuma sakin wani murmushin cike da shauki ya bada damar a karaso da akwatin dake hannaun baban mai bada tsaro wa Palas ya duka har kasa ya bude ya dago abin sama
Da ido HANJA ke kallon Pah, yana son nuna masa kar ya masa haka
Pah ya tsare shi da idannuwansa shima a nutse sannan a sanyaye ya ce" Da bakinka ka furta cewar zaka hau kujerarka idan na tashi sauka ko?"
HANJA ya rintse idannuwansa yana jin wani irin yam yam yam tun daga tsinin kafarsa har zuwa kansa, a hankali ya furta" Ya Allah ", a kasan zuciyarsa kuwa ta cika da fargabar wannan ranar harma ya fara tunanin ko dai ranar karshensa yake ganni haka da aka hado masa dukan fargabarsa a lokaci daya?
Pah ya karra fuskantarsa a sanyaye ya ce" Ka bani amsa "
HANJA ya kalli camerar da aka bude wace ya tabata a yanzu kowani lungu da sako na kasarsa ana haska su ne, kuma tabas ko a dokar daji yana da damar amsar sarautar nan, domin ba siyasa bace bale ace sai an yi zabe, kuma ba yau ba yan kasarsa ke korafin ya hau kan kujera ya ja kasarsu , shine ya tirje kan gaskiya sarauta ba tasa bace, shi ya fi son rayuwa irin ta inci, ya fita lokacin da ya ga dama, ya dawo lokacin da ya ga dama, ya yi barci awannin da ya ga dama ya kwonta da macen da ya ga dama
Sai gashi lokaci daya komai na son tsaya masa?
Jikin sarki har rawa yake na wannan baban al'amari dake faruwa a masarautarsa a baban dakin taronsa
Ai kam masarautarsa ta kuma kafa tarihi an nada sarkin ingila a cikinta, sannan za'a daura auren sarkin a cikinta? Kai abin alfahari ne
"HANJA, ka san talakawanka na kallonka, kuma sunna jira su ga shin zaka jagorance su ko zaka ki jagorantarsu? Ka sani idan baka hau ba dole zan maida sarauta hannun Johnny domin na ajiye sarautar kasata a yau, dan na kai gajiya, shekaruna sun ja zan rungumi matata ne mu huta"
Idannuwansa da suka yi mugun ja ya sauke a kan fuskar PAH,
Ya maida sarauta hannun mutanen da suke da burin korar musulunci a kasar?, Ya maida sarautar hannun mutanen da basu tanadar mata kyakyawan abu ba? Baban budget din Johny shine fara gina gidan giyar da du wanda baya saka albashinsa ciki zai fuskanci mumunan hukunci a gidan horon masarautar, eh lalle ya yarda Pah ya gaji ta yadda gajiyar ta kai shi a yanzu baya tunanin sakamakon dake iya haifar masa
Idannuwansa ya lumshe a kasan zuciyarsa ya furta" TAWAKALTU ALLALAH"
YAna gama fada ya kai gwuiwoyinsa kasa sannan ya dukar da kansa
Kabara aka kwasa, musulmai kennan, inda masu kiran abinsu na coci suma suka fada da dukan karfinsu, wa'inda basu da adini kuwa suka gyada kai cike da ihun murnar ya amsa
PAH hawaye na fito masa ya dauki kourone din ta zinari ya dora saman kan Hanja bayan ya yi masa adu'a sannan ya kama hannayensa ya mikar da shi tsaye ya kuma amshi sandar zinarin da aka miko mai kauri daidai misali da kan Zaki jikinta mai kyan gaske sai walwali take kamar ta dauki ido ya kamo hannunsa na dama ya saka masa kafin ya nemi zubewa a gabansa dan hakan kowa zai yi a gabansa
Da wani irin hanzari Hanja ya tare shi yana jimke hannayensa a kausashe ya furta" Kar ka kafa wani laifin Abui"
Pah ya saki murmushi ga kuma hawaye a fuskarsa shabe shabe ya juya yana fadin" Allah ya ja da kwanakin sarkin kasata"
Wata irin busa aka saki tare da doka wata uwar ganga da suka zo da ita ta karfe wace ta bada wani kuka mai karfin gaske dukan wanda yake dan kasarsu ya gane me hakan yake nufi tun dag gida africa gar zuwa kasarsu kowa da yake haifafen kasar ya san me hakan yake nufi dan haka dy suka zubar da gwuiwarsu daya kasa dayar kuwa a tankwashe kusan a tatare sunna masu sada kawunnansu da maimaita abinda Pah ya fada
Hanja dake kallon live din da ake haskowa na kasarsa ya samu kansa da lumshe idannuwansa lokaci daya yana jin dukan lamura na sarauta na hawa kansa na ratsa jinnin jikinsa da bargonsa harma shi HANJA iza ta sarauta ta shige shi lokaci daya furucin bakinsa suka yi masa nauyi a nutse ya iya daga hannunsa na hagu kawai ya yi nuni da sunna iya tashi , wanda hakan ya tabatar masu ya amsa ya kuma hau
Ai kam daga nan shagali ya kaure a kasashe
Da yawan sarakuna suka fara aniyar zuwa kasata dan taya murna sannan su halarci daurin auren HANJA MUHAMAD tare da gannin wannan amarya mai kashin arzikin da ta janyowa kasartama arziki ba gidansu kadai ba
11/14/21, 12:54 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
Chapter 105 · 0% Book details