Sashe 20
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ya ce" Oga wannan fa ina ga shirya abinsu suka yi, ka barni na shiga na jigata su ta yadda zasu yi bayani da kansu!" Ogan nasu ya dan daga masa hannu yana kallon itin yadda suke maganar , a hankali ya kai dubansa wajen shugaban makarantar da ya tsura masu ido su dukansu ya ce" A jikinsu babu mai dauke da wani micro komai kankantarsa a kowani irin lungu ko sako na jikinsa dan mun duba, sannan ga takardun bayannan ko su su waye nan yanzun aka miko daga dakin bincike na computer bango, inaga da gaske ba turo su aka yi ba dan cutar da kowanmu, dan karrin bayani kuma muna iya zuwa cen gidan iyayen nasu su duka biyu, idan kuwa kun yarda da maganata ban ga wani abu mai duhu ba kawai a sake su " Malamin Psychologist ne ya juyo da byro a hannunsa yana dan cicijewa ya ce" Ban karanci wani yannayi na munafurci a kallonsu ba, ga yadda computerna ta nuna min aman zan so na shiga koda na second goma ne na gansu gani ga su dan karrin yarda, aman koda ban shigan ba na yarda da irin abin nan da nake gani na computerna dan ban taba aiki da ita na ga ba haka ba, ana iya korarsu su tafiarsu" Shugaban mai kare hakkin mata ce ta dauki magana tana fadin" Na tausaya mata, aman dan Allah ku bani jakarta ina son gannin meye a ciki ?" Sai a lokacin suka dauko jakar suka budeta, baki daya abubuwan dake ciki suka zazago saman table din Su dukansu ido suka zubawa kayan kafin su dauke takardun su raraba wa junnansu suka shiga karantawa dan gannin ko na meye? , takardunta ne kama tun daga na Entrer en 6eme, na Brevet dinta da na Bac dinta wanda yake hade da yar takardar dake nuna ko wace ita a bac dinma, takardunta na jarabawarta kaf sunna ciki, sai wani turare na fesawa sai litafi na rubutu kamar kwaya uku da byro kalar ja da blue, sai dala ashirin Junnansu suke kallo gaba dayansu kafin ta kara gyara tsayuwarta ta tausasa muryarta ta ce" A wannan zamanin da wahala ka ga budurwa irin wannan ba ja gira ko jan baki da madubi harda su pant a cikin jakarta ba, tabas ni na yarda da kalaman yarinyar nan, ina kuma rokon oganmu da ya duba wannan lamari ya taimaketa ya saka hannu ya kai maganar ga gwamnatinmu mai adalci a zuba mata ta samu horo ta fito a cikakiyar ma'aikaciyar Hotteste " Daya daga cikin sojojin ne ya dauki magana da dan zafi zafi ko kuwa dan muryarsa ce mai gautsi ko meye oho ya ce" Eh ban ki ba, kuma tana iya zama haka idan aka tsara ta zamo hakan, abinda nake nufi a nan shine ba zamu saki mu yi gangancin da zamu dauki wada zata cutar da y'ayan mutane ba, ku fa tuna irin yanda duniya ta rikice, lale yarinyar nan tana iya zama innocent mai tafe da buri na son zama hottest kamar yadda kuma take iya zama makashiyar dake da burin kashe mutane da kanta" Mai kula da yannayin yan matan wajen, watau mai tsaban tsarin halita, tsarin fata, tsarin yannayin jiki da irin gogewar mutun ta sha sket dinta damame fuskarta dauke da farin gilas na gayu ta sha madaidaicin jan bakinta ta ce" Bama wannan ba, in ba shirme irin nata ba a Niger kasa mai dauke da buzaye, filani, kyawawan hausawa , kyawawan yan mata na kabilu daban daban ne zata saka irin wannan ra'ayi a ranta? Ta kuwa san menene girman kalar da ake so a hotteste? , Bakinta ya min yawa sannan bani da tabacin idan kaf jikinta ne haka, hausarta wata gatse gatse ban ji ko kadan ta sako turanci tsaftatace ba, eh lalle takardarta ta nuna tana da ilimi aman ai ba shi zai tabatar min ba sai idan na gani a aikace, duwawunta sun yi girma da yawa mu da bama daukan masu katuna katunan duwawu?, idannuwanta sun wani lumseh sosai ta haka zata ringa yiwa pasinga magana? So kuke a fara samun matsala ne da zaki ce a duba lamarinta ? Bayan an rufe dauka kuma yanzun ita aka dauketa yaya zamu yi da iyayen yaren manyanmu da suka kawo muka kiya?" Da sauri mai kare hakkin yara ya dauki magana ya ce" ina da magana, ni kuwa mai zai hanna a duba irin yadda take da motivation? Ku juya ku gani har yanzu kuka take tana kuma jadada masa , idan har ta samu aiki irinsu ne masu aiki da zuciya daya, ya dace a ringa duba yayan talakawa, da yaran da suke da burin aman ana dane masu dan son zuciyar iyayensu" Dukan wannan tataunawa sa suke shugaban makarantar matashin datijo dan ba zai fi shekara arba'in ba mahaukacin iliminsa ne ya kawo shi matsayin da yake kai yanzu yana tsaye ne yana bin kowa da kallo sannan yana marantar dukan abinda suke fada, a wannan makaranta a nan dukan wani shugaban kare kare da rikice rikice yake , hakan ya sa basa daukan decision kai tsaye sai a jima ana rigima a kan abu Sai da wajen ya nemi rikicewa kafin ya yi gyaran murya da takardun da aka yi bayanin ita din wacece da makarantar da ta yi ya ce" Takardunta sun nuna shaidar ita din yar kasa ce, haifafiyar kasa kuma girman kasa, da farko dai dukan bayanan takarda ba su kadai ke gamsar da ni ba, dole zan baza yara kasa a min bincike a kanta, idan ta fita ina take zuwa? Me take yi? Da su wa take? A bincikar min malamanta na makaranta, a duba min gidansu yar ciki ce ko sunnan tana haifafiyar gidan ce? Ina nufin barci ke kawota ita din ko kuwa sai ta yi kwanaki bata ciki?, koda ta kama sakin nata ta koma gidansu ne sai mun yi hakan" Dan jim ya yi ya kuma kallonsu baki dayansu ya tsaida dubansa a kan mai zaben yannayi da sauransu ya ce" Da ace abubuwan da kika zana za'a bi kafin a dauki mutun da wannan wajen bai dace da ke ba domin kina kan dogon takalmima tsayinki bai fi 1m 60 ba" Ya maida kan wanda ke maganar a koreta ya ce" Da taka ce zaka fadi haka? Ko ka san naka da suka fito a yanzun me suke aikatawa a cikin gari?" Sai kuma ya ja gabansu gaba dayansu ya ce" Muna haihuwarsu ne mu zubar, idan na ce mu zubar ina nufin ba mu ke binsu waje dan gannin me suke aikatawa ba, su din sunna tashi da burikansu, da yawansu sukan dauki hanyar lalacewa dan neman samun cikar burinsu, shin idan muka dubi lamarin daya cikin dubu muka tsamo muka talafa matsala ne? Maganar nan zata iya mutuwa a tsakaninmu na sai ta hau sama ba domin mu ke basu horo mu ke kaisu kampani ya zaba, idan har ita din ta cencenci zama hotteste abin a talafa mata ne ta zama ba mu koreta ba!" Ya dora da fadin" Ku kun san menene aikinmu, shin wannan ta iya ruwa? Idan bata iya ba ba mu zamu koya mata ba!, shin ta iya Inglish kamar ruwa? Idan a takardarta satar amsa ta samu ta rubuta ta cuci kanta dan koda mun zauna a nutse mun baiwa kanmu amsar riketa mu talafeta dan talafawa yara su zamo wani abu ya kasance bata iya ba dole zamu saki hannun junna, Aikin Hotteste ba aikin direban mota bane ko kwondastan mota ba, sai ka zauna a table ka kuma kawo sakamakon jarabawa koda zaka samu ci!" Karra dubansu ya yi da kyau ya ce" Ba zamu koreta ba, ba kuma zamu riketa ba" Shugaban mai bada tsaron da kwarai ya ji dadin hakan a ransa a bayane ya ce" Yaya zamu yi da ita kennan sir?: ........sorry yan uwa 11/14/21, 12:44 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*