← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 114

Sashe 9

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mayafi tamkar matacin koko da ta yane kan nata da ita, sai jakar tata ta gado ta zuwa makaranta wace bata rabo da ita koda yaushe tana bayanta A sanyaye take tafiarta a yauma domin bata da kuzari ko daya baki daya tunanin yarda zata fitowa matsalarta ta gama cike mata kwakwaluwarta, Sam bata ji tsayuwar motarsa a gefenta ba sai kalmar Dogari da ta sakata juyowa tana kallonsa a sanyaye Sani dake tsaye jikin motarsa, matashin saurayi mai jinni a jika mai nema da karfinsa dan kasuwa ne ginane sannan dan bayan layin su Muneerath ne, kuma a da kawance suke na kud da kud da junnansu aman daga bakin lokacin da ya nuna shin zata iya aurensa? Ta nuna masa aa, ita kawancensu shine ya sa take kula shi ai ya san wa take so dan Allah kar ya kawo mata wannan maganar, shi kuwa Sani a duniyarsa yana son macen da bata bleating, irin rayuwar da Muneerath ke fuskanta a gidansu bai dame shi ba, ai lowani gida da nasu irin kwamacalar, gwara su ba a munafurce suke rayuwar ba, a bayane take ita cema bata son a yi maganar gidansu shima kuma ba dan tana karyata rayuwarsu ba, Muneerath ta masa gaba da baya da zata lamunce masa da ya je gidansu ya yi birgimar ko a aura masa ita ko ya fasa fita kasuwa, kasancewar shine ci da shan gidan baya tunanin zasu yi saken ya ajiye nema ah tam Dan murmushi ta sakar masa a hankali ta karasa inda yake tsaye ta ce" Lah, Sanini ban ganka ba, daga ina haka? Ina yini ya kasuwa " Murmushin ya mata shima yana fadin" Alh Muneerana, daga kasuwa nake zan koma gida nake kiran Munee, munee shiru sai da na ce ta Dogari, hop kina lafia yaya dogari?" Dan sakai ta yi da bakinta kafin ta watsa hannunta a sanyaye ta ce" Nima ban san yaya yake ba " Sani ya dan zarro ido ya ce" Ba dai har yanzu baku hade ba?" Kanta ta dan sada cike da jin ciwo a zuciyarta , sai kuma ta watsar tana zagayawa gefen daya ta bude motar ta shige gaba tana fadin" Oya direban Munee karasani gida mana " Daria ya yi cike da jin dadin da alamu zata dawo masa irin na da yarda suke zumuncinsu ba wani kwane kwane ya shiga motar yana fadin" Daga nan har wucin gari zan kai Muneerar dogari" A lokacin da ta shiga gidansu dai yannayi ne irin na kulun, da alamu kuma tsohon gidan na nan dan kuwa yawancin zaman nan da suke na yama kowa a wajensa yana tsula mai gyara shi idan uban gidan na falon ne, ba wai dan su bashi waje ya huta ba fa suke haka, no iyayen kowane ke koro shi waje da dan cin hanci dan ya samu zama kusa sa ogan gidan ba dan tana ranar girkinsa ba, aa , dan kawai a samu na fafatawa a tashi a yi ta masifa har makota na samun jifan marfin kwano Bata yiwa kowa magana ba, duda wasu cikin yayunta yan matan sunna kugin kiranta da *Ta Dogari* da sigar neman fada dan ta biye masu a yi masifa, aman sai ta share kowa abinta ta yi shigewarta ciki dan a yau so take su zanta da shi mai gidan, tana son su dan tatauna ko yayane Da salamarta ta shiga a bakinta, sai dai abin haushin daga matan har mijin ido suka dago suka zuba mata an rasa mai amsa mata salamar da ta nemar masu amincin Allah ya tabata a gare su cikake Bakinta ta dan yatsina tana kallonsu kafin ta karasa kanta tsaye ta shiga ta zauna a gabansu baki dayansu hakan ya sa suka yiwa junnansu kallon kallo ciki kuwa har abokan zaman majaifiyarta suka kamu da jin dadin ga ta inda zasu jata fada ya fado masu a banza Ido hudu suka kuma yi da mahaifinta kafin ya dan yi murmushi yana kada kansa ya ce" Ruky, duba ki gane min kyankyasata, in ba dan ni kaina ina tsoron kwakwaluwar muneerath ba ai da na ce na samu jari, kin san fa akoy mazan da dan sakarci su kawai bak'sr mace ta masu a rayuwa, wai har fadi suke su idan suka samu bak'a a wannan zamanin da bata shafe shafe ko nawa zasu batar dan ita basu da bakin cikin hakan, kuma fa manyan masu kudi fa, sai na yi mamaki sosai har na ringa tunanin su kuwa ko magaya ne basu da shi?" Ya karashe yana dauko wayarsa lokacin da matarsa Ta budi bakinta irin da yannayin kisar nan ta ce" Shine ai boss abin ke damuna, ka ga yarinyar nan mace har mace, eh lale bakinta ya yi yawa sosai aman duba ka ga kafma a cikin yaren wa ya yi fitowar gashinta da kirarta?, aman ka ga a banza tunda ba zamu anfana da shi ba, y'a kamar wace aka zara a cikin taran?, duba ka ga tana tafe tana mafarkin dogari...." ta karashe tana kilkilewa da daria Dayarma ta ce" Ni du ba wannan ba, du kyan bakin mutun ai ba abin yabawa bane da zaka yaba kyanta, kuma tun kyanta ai a banza tunda a bayane take Muneerath mahaukaciya ce" Mahaifiyarta dake zaune cikin shiga ta atampa an mata wani shegen dinkin da ko y'ar a yanzu da wahala ta saka irin rigar nan haka ta fita da ita tana dan gyara farcenta tana kallon kowa tana girgiza kafarta daya dake saman dayar tana kallonsu bata ce kun ci kanku ba, domin ita a yau ta yi niyar sai ta caji oga ba zata kula ko wani shege ba Zamanta ta gyara a sanyaye ta ce" Baba, dan Allah wajenka na zo ina son ganawa da kai" Wayar da yake dannawa ya dakatar yana kallonta , sai kuma ya ce" Ba dai a kan maganar Dogari da kuma son zama Hottest bane? " Sai da ta hadiyi yawu marar dadi da jin ciwon irin yadda suka dauketa kafin ta lumshe idannuwanta a hankali ta gyada kanta a lokacin da ta samu wata idea ta gyara zamanta ta ce" Ba su bane, ina so ne ka bani kudi ko yayane na nema na karra na je na shiga clob din da ake koya ruwa, ina son na iya ruwa" Wannan karron mamanta ce ta ce "TO FAH" tana kallonta Lishiyar mamanta ta fashe da daria tana fadin" Yau mun yi abin kanmu mun karra kankaro wulakanci mun samu buri na uku, sai yar Oga naki salon daban ne" Muneerath da ta tsare shi da ido ba irin adu'ar da bata janyowa tana kallonsa tana tofe shi a kasan zuciyarta, ita bata iya karya ba da ta yi masa dan ya bata yan cenji, yana basu kudi fa ba baya basu ba matsalarsa ba zai yi asarar kudin makaranta ba a cewarsa dan ya tabata ba karatun zasu yi ba wai basu da takaici Da daidaya ya ringa bin matan da kallo kafin ya ce" Ni ina mamakin matan gidan nan, yanzu da kuka tsatsaremu da y'ata ta kawo magana mai mahinmanci na farko a rayuwarta so kuke na zageta ko me? Kai ban taba gannin yan bakin ciki irinku ba, ai ni abin alfaharina ne a ce daya cikinsu ta iya ruwa, baki ga wani abokinmu da dansa ya iya ruwa ba yadda motsi kadan zai ce wane ya ciyo gasar kaza a gari kaza dan tsabar kwarewa, dama haushinsa nake ji idan yana irin maganar nan, aman yanzun nima zan faso zai ga rashin mutunci, Ke yar oga nawa ne kudin?" Ba Muneerath ba harta mahaifiyarta sai da ta zarro ido bale kishiyoyinta Da sauri ta sanar masa kudin na tsayin wata biyu har jikinta rawa yake lokaci daya mahaifiyarta ta ce" Aa oga gaskiya ba haka za'a yi ba, to ni nawa bukatar fa, na fada maka ina son kudi wayata ta fara samun matsala tun ranar nan ka ce na bari ranar aikina na faranta maka ka bani kuma yau ne ranar zaka wani bata kudi?" Da sauri kishiyarta ta cafa da fadin" Ke bama wannan ba, a kan me zai bata kudin koyon wani ruwa na kaniya? Ai muma nakuda muka yi muka haifa sai ka zana na kowa ka bada dan ba wanda ta fi a gidan nan Walahi ko a yi tashin hankali!" Murmushi ya yi ya mike ya soka wayarsa a aljihunsa ya kalli Muneerath ya ce" Sai ki san irin zaman da zaki yi da kowani shege a gidan nan, kina dai gani irin bakin cikin da suke maki, idan kika kware kika zama hamshakiya kika kula su inaga a nan zan tsine maki kowama ya huta!, bari in je in biya da kaina ki shirya gobe ki fara abinki yar oga!" Yana gama fada ya yi waje, nan da suka juyo gaba dayansu kanta, ba wanda baya fadin abinda ya zo masa bakinsa cike da bakin ciki da jin haushinta tamkar zasu cinyeta danya Ita kuwa gaba daya sai abin ya kara sace mata gwuiwa, mahaifinta ne wannan, ta zo masa da maganar da mai yiwuwa namiji ne zai koya matan, sannan ta yiwuwu su ki yarda da cewa zata yi da wando mai dan tsayi dan kare mutuncin kanta, aman bai wani dan tsaya dan binciken komai ba ya kada kai ya tafi, ga kuma mahaifiyarta na mata fada a kan dan me ta kawo bukatar kudi a lokacin da ita ta so kawo tata? To ta nemo mata cikon kudin wayarta ko ta ga iskanci .................idannuwanta ta lumshe a lokacin da ta rufe dakinta ta fada saman gadonta a sanyaye ta furta "YA ALLAH" 11/14/21, 12:43 PM - Allah Akbar: *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*
Chapter 9 · 0% Book details