Sashe 3
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ba kowa ke samu ba domin idon wanda ya fi kowa daraja ne a cikin masu daraja mafi kusancin Allah, to ama nakin nan ya girma da yawa ga wani shegen dogon hanci uwa zanen cartoon!" Du cikin yannayin jin haushi ne ta fadi magangannun nan ga y'ar cikinta , wanda na so gannin mutuwar jiki da bacin rai a bayane a fuskar yarinyar, sai dai ga mamakina hankali kwonce ta ce" Abincina ne ban samu ba, gashi bani da cenji komai a jikina ki dan zuba min madara da garin cen na sha na kwaso yinwa yau mafarkin dogari na yi a aji." Hannunta ta saka ta talabe habarta cike da mamakin yar tata, kafin ta girgiza kai ta ce" To a kan me zan baki garina bayan kin san ina ajiye da shi ne dan shegen koma bayan tayan ubanki na sai an gama raba abinci su dawo su cinye nasu kuma su cinye na mutane, ke dai bara in lalubo maki hamsin a cikin kudin da kika banin nan, ni an kwana biyuma baki bani komai ba Allah dai ya sa ba daina kula saurayin naki mai bamu kika yi ba dan haukan da ake kadawa cewar kina fama da shi?" Wannan maganar ma sam bata wani d'ad'ata da kasa ba, saima kallonta da ta yi na maganarta ta karshe da ta sanyayar mata da gabai ta ce" Yanzun kema kallon mahaukaciyar kike min kennan oan maganar dogari? Ku dukanku zan baku mamaki ne a kan maganar dogari, sai na kawo dogari har gidan nan ya aureni mun koma kusa da sarki sai na ga mai k'yamata dan Allah." Tana gama fad'a ta juya zata fita ta kuma juyowa tace "Kuma ma rik'e garinki, kuma shima mai banin zan kore shi yau tunda dai kema baki yarda cewar ni ba mahaukaciya bace ba, kuma kin ga insha Allahu karatun matuk'iyar jirgi sai na cinma burina koma menene ni da Allah na dogara." Tana gama fad'a ta kuma juyawa ta yi tafiarta ranta a b'ace, hakan ya saka uwar rakata da kallo kafin ta yi hamma da mik'a tana girgiza kai tana d'an shafa dokin wuyanta da take ji ya d'an rik'e mata a bayane tace "In ba hauka ba ina kalar fatarki ina zama ko kalar shiga jirgi ne bale zama matuk'iyarsa? Kaf a afrikama mace nawa ce take tuka jirgi? Bayan wannan ko a karuwan jirgin nan ai babu bak'ak'e bale a d'auke ki , kawai b'ata lokaci nasarun da suka bud'a wannan makaranta sune yan iska, ke dai kawai ki auri masu zuwar maki, suma na tabbata wannan k'irar taki ce ba wani abin ba, bari dai na mik'e na d'an watsa ko na jini garas." ___________________ Tana shiga d'akin da yake mallakinta bayan ta bud'e da ky d'inta ta jefar da jakar makarantarta kafin ta cire hijab dinta ta k'arasa bakin katifarta ta zauna tana kallon waje d'aya. Abinda take tunawa irin kayan da aka ce lalle lalle shi za suna sakawa gabanan dan fara d'aukan darasi na wa'inda suke da ra'ayin aiki irin nata, ita fa babar damuwarta shin oga dogari zai yarda ta yi aikin jirgi? A duniya burinta biyu ne auren dogari ne na farko sai ko kasancewa matuk'iyar jirgi, wannan buri ya shiga ranta ne daga ranar da ta ga farar banasariar dake matuk'iyar jirgi, daga ranar ta gama yankewa kanta hukuncin a duniya bata da wani aiki sama da shi, aman fa idan dogari ya yarda. Kuma d'aga kanta ta yi tana duba 'yar k'aramar agogon d'akinta, yunwa take ji sosai fa, irin sosai d'in nan, gashi ba abinci Dolema ta yi zance yau idan tana son kwana lafia ba tare da ana yak'i irin na sambisa a cikin tumbinta ba.