Sashe 80
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ta cire dubanta a cikin nasa ta sada kanta tana shafa gefen wuyanta a hankali ta ce" Sir zan tabo ka idan an jima zan yiwa Mah maganar zuwanka abinda tace sai na fada maka" A hankali ta kashe kiran ta ki kallon wajensa, gaba daya ji take bata iya kallonsa bata san me yake ji a tsatsare mutun da ido ba A hankali ta ce" HANJA, yaushe zaka mayar da ni gida? " HANJA da gaba daya ya ji abincin ya tsaye masa a kirjinsa ya cinkushe masa, gaba daya ya ji zaman wajen ya fara isarsa maganarta sai ta diro masa a wani baibai Me take nufi da yaushe zai maida ita Niger?, Me take nufi da shi?, Shi wai sa'anta ne ko meye? Mai kula da Tgr dake tsaye yana jira shima a kadan ya yi minti arba'in a tsayen ya kai dubansa kansa, yana shirin masa nuni da ya tafi da shi su Mah suka sauko Turus Mah ta yi gannin a yan taron harda su Tgr ga kuma y'ayanta da alamu an tsatsare su ne , sai itama ta ki idasawa har sai da ta ga an ja Tgr an tafi da ita kafin ta karaso tana murmushi Jikinta ya yi sauki sosai, saman kujera ta zauna tana zama ta dan daga murya ta ce" Abinci ake ci ne? Wanda ya gama ya zo na ganshi, Son harda kai a cin abincin?" Muneerath yanzun ta samu kanta, an tafi da Tgr haka kuma ga Mah a gefe dan haka sai ta dauko dan mayafinta ta kade abinta ta yafa sannan ta mike tsaye da kyau tana gyara rigarta ta kalli Saudat, yar daria ta yi da yannayin na Saudat ta ce" Sai ki taso mu karasa cen yau mun tsira Allah dai ya sa mu rabu da kasar nan lafia, taso kin ji" Tana fada tana kamo hannun Saudat ta mikar da ita hankali kwonce ta jata suka yi wajen Mah Wata shakar ya yi, harma ya ki ya motsa daga yannayin da yake Daga inda yake yana ji dan rashin kunya yarinyar nan na fadawa Mah zata kawo kato gidansu, ta karashe da tambayar Mah yaushe za'a maida ita Niger? Tana missing din iyayenta fiye da tunanin dan adam, sai ya ji kawai shi take nema da fitina dan haka ya mike tsam tare da daukan tissu ko ruwa bai tsaya ya sha ba ya juyo ya sauko da sauri sauri ya karaso Yana tsayawa su Pah na shigowa da baban Minister da matarsa da y'arsu yar kwalisa sai rangaji take abinta Bai tsaya da niyarsa ba yana zuwa rai bace ya ce" Ke!, An ki ba'a mayar da ke Niger din!, Kuma dakike maganar zaki gayato wani sakaran saurayinki marar aikin yi sai ki gayato shin mu gani tunda ke bakya jin magana sai neman rainawa mutane wayo da batawa mutane rai da kika fi kwarewa a ciki, ba zaki je din ba kuma ba zai zo nan ba!" Ikon Allah ne kawai gaba daya al'umar dake wajen suka tsaya kallo, ciki kuwa harda Iman da yar gidan Minister wada tunda take bata taba sannin yana doguwar magana haka ba, itama sai kai dubanta kan wace yake yiwa ihun, Iman kuwa da gaba daya kwanakin take dan fuskantar ya cika zakewa a lamarin Muneerath jin ba zai maida ita ba ba kuma zara gayato saurayinta ba sai ta yi mutuwar tsaye tana dane kukan dake son fasowa ya fito daga bakinta Kallon kallo suke kafin Munnerath tsam ta mike ta koma datan gefen Mah ta shirya tsaf koda ta kwana ta ce" To kuma ni yanzun dan Allah me na maka, kai kawai ka tsane ni?, To a kan me zaka ce ba zai zo ba bayan saurayina ne kuma Mah ta san da zamansa?, Bayan wannan Niger din nan fa ba anguwa ba nake nufi sunnan garinmu ne garin iyayrna inda ka dauko ni, ko zan iya sannin a kan me ba za'a maida ni ba? Ni wollah Mah kin gani haka fa ya hayo cem wajen da zakinsa ya hanna mana cin abinci karshe harda hawaye kawata take na ta gama sarewa cewar mun mutumun lalace, kuma dai ai ni na daina yi masa rashin kunya shine zai ce yanzuma ba zan je Niger ba?, To ni dai sai na je ko a tayar jirgi ne koa kafa!" Hargowa da rigimar da ta shiryawa din ne kam ya gama hadawa kala kala, fitina tashin hankali fada shine abinda iyayensa suka gama karanta a tatare da shi wanda yake kiris ya fashe da su Lokaci daya ya daga kafarsa zai zagaya ta dayan Bangaren, hakan ya sa Saudat ta duke jikina bari cike da tsoron yannayinsa ta rufe ido ta dora hannu a kai tana dana sannin zuwanta gidan ta gama sannin cewa tasu ta kare hakama sun gama rasa aikinsu kennan ko wa ya tsaya masu,sam bata san Muneerath rikakiyar mahaukaciya bace sai yanzun da ta baiwa sir Hanja amsa a haka, in ba kasada irin tata ba idan yace ba zata je ba ta yi hakuri a lalaba shi mana sai ya mayar da ita a hankali idan ya yi niya duda bata san dalilinsa na cewar ba zata koma garin iyayenta ba, haka kuma ita da kanta ta ga gangancinta na cewa zata gayato sir Attahir gidan nan , ita a tunaninta yadda ya zamo waje mai saukin shiga a wajenta hakama kowa ? Gaba daya ta tsorata da jan da fuskarsa ta yi shi yasa ta duke dan ta san har ita yau sai ta dauki duka! Da gudu Muneerath kuwa ta dafe rigarta ta juya wajen matakalar benen ta fara haurawa da dan ihun neman ceto tana kiran sunnan Mah da Pah Gogon kuwa ko idannuwansa basa gane masa da bakin fuska a wajen, ko lamarinsa ya yi daukakan da baya iya hakuro har su tafi?, Ya aniya bin bayan nata da nasa kalar salon bi da gudun dan so yake ya damketa ya yi mata shakar mutuwa sai ta fara bambance raini tsakaninsa da banza Attahir din da duk a cikin abin ya fi bashi haushi ba tare da ya san dalili ba Pah dake yar daria ne ya yi maganar da ta saka jinnin kowa kusan hawa a wajen nan, kama daga iyayen budurwarsa masu neman iri, da shi gogan dake neman kasara yar mutane, da kuma Iman mai fama da nata miki cikin shiru, da Saudat da bata san abinda ake ciki ba, da Mah wace ke kokarin taro shi kar ya aikata haka dan bata san a yaya zasu kare ba ta tabata ba iya tsere masa zata yi ba duda ta fala a guje abinta a lokacin da ya ce" Ts 's my dghter in low " Shi dai turancin nan ba yarena bane, idan ban yi daidai ba ku daidaita 11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*