← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 114

Sashe 36

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
2
Ba edditing fa
Sosai yakara kausasa fuskarsa kafin ya ce" ba zata zo inda kuke ba, ba wata bakuwar fuskar da zan kawo gidan nan kun ji na fada maku gaba dayanku"
Tsuru ta masa da ido tana kallonsa har ya gama saukowa daga saman bed din fuskarsa a hade din nan ya nufi bayi ita kuma ta raka shi da kallo kafin ta cire dubanta ta mike ta nufi wajen suturarsa tana dan cije lebenta na kasa a ranta tana fadin 'ba dai naci kake so na maka ba? Zan maka shi har sai ka ji kamar zaka saka kuka domin yarinyar nan ni shaida ce bata da kowa a nan, sannan irin damuwar da na gani karara a kwonce a fuskarta sai na maye mata da farin ciki a kansa'
Kaya ta ciro masa bakaken swttt da abubuwan hadinsa harta da agogo sai da ta ciro ta ajiye kafin ta tafi falonsa ta zauna ta gyara zamanta sosai tana jiransa da karamar waya a hannunta ta kirayi yarinyarta da take wajenta ta shaida mata abubuwan da take so sannan ta dora zaman
Ta dauki a kadan awa guda har bayan kanta ya fara sara mata kamar yadda ya saba yi mata sukan nan tana zamanta sai ya soketa ta dafe kadan ta lumshe idannuwanta tana tofa adu'a ya fito daga dakinsa
A hankali ya karasa ya duka gabanta yana kallon fuskarta kafin ya saka hannunsa ya shafa gefen fuskar tata a hankali ya ce" Me yake damun Mah? "
Mah ta sauke ajiyar zuciya ta cire hannunta tana kallonsa ta dan girgiza kanta a sanyaye ta ce" ka dauko min ita, ina so ta zo kusa da ni please"
Kansa ya kawar ya kama hannayenta ya juyo yana facing dinta a hankali kamar baya son magana ya ce" Duniya ta rikice, mugayen mutane sun cikata da muguntarsu a cikin zukatansu, ku....kune duniyata, kune farin cikina, sai yaushe zaku gane cewa bana tunanin idan har zan iya aikatuwa idan bakwa gefena? U see da hannuna zan shaketa sai ta daina motsi koda musu ta yi da ke bale ta ilata min ke, Mah koda tokarta ce sai na kona na kuma konawa na kuma konawa, na shiketa na busarta na kuma jiketa na zuba a kwata!, Ba zan iya kwatanta maki tsorona da dukan halitar da zata rabeki bayana da abuina, kin ga ko wannan da kike riko mai kallon tsiyar nan ba wani yarda na yi da ita ba!"
Murmushi ta yi cike da kaunarsa a kasan zuciyarta inda fuskarta ta bayanar da shaukin kauna irin na uwa tana tuna yarintarsa da irin yadda ko bata da lafia yake adu'ar Allah ya sauke mata ya dora masa,watau wata irin shakuwa ce ta ban mamaki a tare da su, ko mamansa da tana raye da iyakar shakuwar nan kennan
A hankali ta shafa itama wajen sajensa a sanyaye ta ce" Burina ka zama mai tausayi, ka zama mai taimaki, ban ki ba duniya yanzun ta zama abin tsoro sosai, aman kuma a cikinta akoy na kirki cike fall, hakama akoy innocent cike da ita, Son akoy marayun da suke da iyaye, akoy bayin Allahn da suke manyan mutane ne a boye abinda ya hanna su bayana just dan taimako ne na manyan da suke sama da su, Son ka faranta min dan Allah"
Idannuwansa ya lumshe yana kallonta a hankali ya kawo hannayenta wajen bakinsa ya lumshe idannuwansa ya manna mata kiss a bayan hannayenta sannan ya dago da dan tsugunnin da ya yi a gabanta ya mana mata wani kis din a saman goshinta a hankali ya ce" I love u "
A bayane ita kuwa ta dafe saman gashin kansa ta shiga kwararo masa adu'o'in tsari kafin ta karashe da furta masa kalmar Allah ya yi masa albarka sannan ta mike ya riko hannunta sunna tafe a hankali har suka fito waje kafin ya yi gaba tana daga masa hannu ya je wajen motar da aka bude masa ya shiga sauranma du auka shishige da gudu suka tada suka kama hanyar tafe tafen da zai yi ciki harda zuwa ya ga Zakanyarsa.
Da dan sauri ta koma bangaren mijinta, tana zuwa ta zauna kusa da shi tana murmushi ta ce" Idan ya zo da ita Khalb sai ka soya min kwon nan yau"
Murmushi ya yi mata yana daga kafadarsa yana yatsine baki na maganin da ta matsa masa ya sha wanda a saudiya aka yi ta saukar alkur'ani aka hada da wasu ganyayaki nasu wai ya ringa sha in sha Allah sai dai idan ciwonsa ba na warkewa bane, idan dai na warkewa ne zai warke ne cikin sauki a lokacin da shi kansa bai tsamata ba, watau sun nuna masa cewar ayar Allah ita ce magani, babuaganin da ya kaita karfi hakan ya sa yake sha aman ba wai dan ya saka a ransa wai zai warke ba, wani warkewa kuma? Ai warkewa mai gaba daya na tunkaro shi a kowani second wanda ya tabata yana yinta an kare, haka kulun ta dafa masa su percil, su sasake sasakenta ita dai mijinta kar ya barta, sai da ya yatsina fuskarsa kafin ya ce" Wanene zai daukota? Kin manta irin tsanarsa da mutun bako? Bama zai daukota ba"
Kanta ta dora a gefen kafadarsa jikinta a sanyaye ta ce" ni kuwa da sai na masa kuka, kuma na je na daukota da kaina"
Murmushi ya kuma yi yana girgiza kansa a hankali ya ce" Noor, ba zaki zubar da kwalarki na ko na wasa ne idan dai ina raye "
Shiru ta masa dan bata so a yi nisa da maganar idan yana rayen nan domin ba abinda ya gagareshi yanzun ya zurmiyar da ita a kogin tunanin rayuwa babu shi
..................................................
Idan aka ce nutsuwa, ana nufin nutsuwa,barci ne take na nutsuwa, cikin nutsuwa, bayan tarin gajiyar da ta kwasa na yau
Tabas kasashen waje sun yi nisa irin nisan nan da hankali ba zai dauka ba sai idan ido ne ya gani
Na sha gani a cikin familly Kardashian da cikin emission kala daban daban na irin yadda mutun ke sawaya lokaci daya watau a cikin sati daya idan aka fara bashi kulawar idan ka ganshi zai zama bako a wajenka har sai ka kuma tambayar kanka da kokowa da tunaninka kafin ka tirsasawa zuciyarka yarda cewa shine ba
Girman jikinka na iya ragewa ya koma sakwaikwai , tumbi na iya shafewa ya komai luwaiwai ba tare da ya bar tarin fata ba ko nankarwa irin na mai jiki idan ya rame ba domin akoy mayuka da kuma sport din da zai ja maka fatarka sosai ta janyu ta yi kyau sosai
Shi ba shirurgi ba, ba kuma tsafi ba, reality ne wanda sai ka bi tashohinsu zaka ringa gani ko idan ka je inda suke zaka karda du girman jikinka yana iya raguwa ya daidaita ya yi kyau, haka kuma du tumbinka yana iya shafewa ya dauki kala, komai girman duwawunka idan baka so akoy irin aport din da zaka yi su ragu da irin kalar cimar da za'a doraka a kai ......watau zaka cenza iya cenzawa sai dai halayenka su shaida ko wanene kai domin hausawa na cewa idan ka rabu da mutun tambaya idan ya yi arziki aman halaya na nan...........
Shi ne ya faru da rayuwar MUNEERATH a tsayin sati uku, wanda ta amshi wani irin kulawa tun daga yannayin jikinta da sam ta ki a rage mata duwawunta ta nuna a kan me a barta da halitar da Allah ya mata, sai dai tumbin nan nata gaba dayansa ya lafe ya shafe ya tafi duniyar da takan kamuwa da mamaki ta ringa shafarsa tana juyawa dan son gannin ina ya je ya lafe, domin ko ta ci baya nuna kansa ya rigaya ya amshi gyara mai yiwuwa shi da ya tasa sai ko yaro ya shiga,
Fatar jikinta kuwa ta hadiyi na hadiya ta shafa na shafawa, bakin nan nata ya zama baki na mararin farar fata ko wacece, bakin nan ya zama baki mai birge kowa, fatarta ta yi wani irin laushi na mamaki domin tun AC na sakata mura har ya yi hakuri ya ba kansa lafia ya zubawa sarautar Allah ido dan kuwa duda kasancewar garin garine mai sanyi shi yasa ba ko'ina suke da AC ba yawancin guraren sunna dauke ne d chauffage, aman haka Take kwonciyarta a cikin sanyin nan ko ta yi kai kawonta a cikinsa ba tare da tana makuarkyatar sanyi ba, har wani sa'in takan tambayi kanta to yaya aka yi take jin tsoron sanyi a da a yanzu kuma bata tsoro?
Gashin kanta ya gama bayanar da bakinsa da ts
ayinsa da laushinsa, ita kanta a yanzun takan saki murmushi tana hangota a Niger idan aka mayar da ita gata ga Oga ga mamansu ga yan gidansu uwa uba idan ta zagaya ta tabata a yanzu dogari sai ya yi kuka kafin ta yarda da maganarsu ita da shi! (Ciwo na dogari yana nan dan har yau har gobe tana kan bakanta)
Ga sir a gefe guda ya zamto mata aboki, aminin shawara a ganninta, inda shi kuwa ya zuba mata ido yana son a hankali ya cire mata maganar wani wai dogari , domin ya kwatanta mata cewar wannan mafarki ne, inda ta shaida masa ko kasancewarta A wanann waje a matsayin hostess mafarkinta ne ya tabata, ta tabata wata rana zata ganta gata ga dogari a matsayin mata da miji..............watau dai su din zasu taka matsayi na yan uwan sarki, wanna. Daraja tana so ta zamo gaske dan ta san sarki ko dansa sun fi karfin yar oga..........sunna zantawa da shi ne ta yanar gizo gizo domin har yanzu yana nan a hannun HANJA bai sake shi ba
A zabure ta farka daga barcin da take a lokacin da karaurawar da ake tashinta a barci ta dauki kuka kirrrrrrrrr
A firgice cike da mamaki ta kai dubanta kan agogon dakin dan gannin hala har lokacin tafia gudun yama ne ya yi bata tashi na bayan ta kasance mai tashi a kan lokaci?
Maganar dake shiga kunnenta ya sakata yin kasakai tana sauraro kafin ta sauko lalausan kafafuwanta ta zura cikin takalmin dake kusa da bed dinta ta saka hannunta tana kunce hular kanta sannan ta cire dan Siririn ribom dinta ta yamutsa gashin kanta a sanyaye ta ce" Prince kuma sir? Kin fa ganni fa cikin lokacin barcina ne fa ko so kike muna girki ina barci kuma ki ce laifina ne?"
Murmushi ta yi daga zaunen da take tana kallon yadfa take turo baki ta ce" Yan mata, ki rufa mana asiri ki tashi ki je ki kimtsa kamki cikin minti goma ki fito domin nan d aminti talatin zai karaso, ki kula idan har wani abu ya kauce ni da kaina yana iya korata a nan, ko so kike a kore ni?"
Kanta ta dago ta kai wajen camerar ta dan tsura ido kafin ta mike ta ja tawul ta nufi bayin
Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta bi bayanta da kallo ta dan dafe gaban goshinta ta kali ta kusa da ita da ta ce" Banan tashin hankalina irin abinda zai faru a kan maganar girkinta da kuma kiyawa da ta yi a taba mata hips dinta, ki duba ki ga a da bai fito sosai ba domin a da tana da tumbi, a yanzu kuwa da tumbin ya shafe kina gannin yadda gaba daya ya gama bayana, bombom dinta ba zai boyu ba koda wandon jine ta saka , ina tsoron sanadiyar wadinnan matsalolin biyu yau ya wanke mu tas"
Mai bima babar tasu ce ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Madame, me yasa wai kika ki taba mata duwawun nan nata kika biye mata aka bar mata su a haka bayan ga yadda suke da girma da fadi?"
Dan murmushi ta yi ta ce" nan fa burinku ku samu duwawu koda rabin rabin nata ne, duda na san ba maganar ra'ayi bane aman wannan wajen fa waje ne da kowa da yadda yake son gannin nasa sai idan bai samu ba"
Dan murmushi ta yi ta ce" ita bama wannan ne damuwarta ba, baki ga abinda ta ce ba, cewa ta yi kar izgilin ya yi yawa a bara mata halitarta haka ita kamta sun dameta aman bata so a rage su dan kamar za'a yi izgili da yawa wai"
Mikewa madame jocyline din ta yi tana harhada takardu da sauri sauri ta ce" Wani lokacin haka musulmai suke, idan zasu yi abu sai ki ji sunna cewa kar su sabawa Allahn su, ban san me hakan yake nufi ba, aman ita da ta hanna a taba mata bayanta ya hauta sosai, wannan bayan nata du nimiji mai lafia zai motsa idan ya kalla , dan dai shi sir din ne ya zama ba wannan ne a gabansa ba, ni dai fatana kar a kore ni yau, mu tafi maza maza mu gama shirya dakin tuhumar, ban san me ta aikata da za'a tuhumeta ba"
11/14/21, 12:48 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
Chapter 36 · 0% Book details