← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 114

Sashe 104

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

idan ya samu kansa a gaban sarki, sai ya samu kansa da tunanin to yaya kuma tarbiyar yarinyar? A nutse ya budi bakinsa , a gadarance da izar sarauta ya furta" Ko itace ta tafi aikin Hostess tare da Gimbiya KHADIJA?" Ba wani irin a sada kan nan Oga ya saki murmushi yana kada kai ya ce" Ita da kanta, ai yarinyar tunda ta dauko kalar fatana na san ba karamar mutun bace" Salihu ya yi saurin mintsininsa yana hararansa kasa kasa tare da tunanin Anya Oga ba zai saka su samu ladan bulala maimakun karin girma ba kuwa? Waye ya ce masa ana amsawa kai tsaye ba tare da an baka damar amsawar ba? Kai sarki ya cire daga dubansa ya maida kan wayarsa da ta dauki ringin Gannin kira ne daga masarautar ya saka shi yi masu alamun kan kowa ya yi shiru baya son hayaniya komai kankantarta A nutse ya daga kiran ya gabatar da kansa sannan ya yi masu confirmen eh shine ya nemi da a hada shi da sarki kan maganar da ta shafi HANJA Kamar da minti biyar wayar dakin Pah na ringin kafin ya daga a nutse ya yi salama yana rufe al'kur'anin da yake karantawa Gaisawa suka yi sosai a mutunce kafin sarki ya ce" Dangane da ziyarar da Mai Girma Hanja ya kawo ne " Sai kuma ya yi shiru yana tunanin me zai dora a kai Pah a tausashe ya ce" Akoy wata damuwa ne ko yarinyar ta ki ta aminta da soyayarsa ne?" Da mamaki Sarki ya ce" Dama ba soyayar suke yi ba?, Eh toh damuwar ba wata mai girma bace gaskiya sai dai ta fuskar da za'a fuskanceta ne, mahaifin yarinyar ne ya zo da maganar cewa yana bukatar a daura auren nan kawai ya juya da matarsa domin shi baya son ......baya son wasu dabi'u na rashin kunya a idannuwansa da suke nunawa su yaren a gabansa" Da mamaki PAH ya ce" A daura aure kuma?, Wani irin aure ne haka kai tsaye ba shiri ba komai?, To ita yarinyar ta yarda tana sonsa ne zata iya rayuwa da shi ne? Dan a maganata da shi dai yana min korafin a kan me na hada tafiyar da mutanen da take so da kuma saurayinta, bayan na yi haka ne dan na kara isar masa da wani sakon cewa idan ya yi sake , saken zai gani, aman menene abin rashin kunyar da suka yin ne?" Sai da Sarki ya dan yi gyaran murya kafin ya furta" Ya ce an rungumeta a cen cikin asibiti, sannan yanzun da kanta yarinyar ta fada kirjinsa ta rungume shi a gaban mutanen anguwa, ka san mu a nan bama haka Allah ya ja da kwana" Murmushi ne ya subucewa Pah, ya ce" Dama sai da na fada masa naku al'adun sun bambanci namu, ya kiyaye, sai dai maganar ta fada jikinsa ta rungume shi shin da gaske ne?" Sarki ya kallo wajen Oga ya ga shi kawai yake kallo yana murmushi da alama shima ya iya turancin ya ce" Eh haka kam ya fada, kuma haka abokinsa ya fada, yama ce tunda ta zo bata sha ko ruwa ba tana kukan ko yana kula wasu matan? Inaga soyaya suke yi ko nace ta yarda da soyayar tasa ne" Wani murmushin Pah ya yi sannan ya dan yi shiru yana ta analysng din situation din A nutse ya ce" Auren my PRINCE na so ace kaf kasashen duniya babu wanda bai halarta ba, na so a daura auren my hero a kasar saudiya, na so ace aurensa yana gefena mun saka fararan jalabiya mun dora hirami mu yo sujadah ana daurawa na bashi kujerarsa na sauka na rungume yar matata mu ci gaba da istgfari da neman gamawa da duniya lafia, Allah ya kara maka lafia Na so ace NANA KHADIJA na gefena ranar daurin auren yaronta dan na ga irin murmushin da zata yi idan ta ji yaronta ya zama mijin wata, watau shima mai gidan wata, zai bata farin cikinta da take ta mararin budar ido ta gani shine jika daga tsatson yaronta....." Shiru ya yi yana lumshe idannuwansa yana adiye damuwarsa hakan ya sa Sarki muryarsa a sanyaye ya ce" Allah ya karawa Gimbiya lafia, ya sa zakar jiki ne" Pah kasa kasa ya amsa adu'ar kafin ya ja numfashi ya ce" kana gannin idan aka daura auren nan haka kai tsaye ba tare da an mata gayar da ta dace da komai ba an yiwa yarinyar adalci kuwa? Ka san fa mata yadda suke shirya aurensu da komai da komai" Sarki cike da yarda da maganar da zai fada , dan shima fa gaskiya yana so a yi auren nan, taf a kasarsa Hanja ya fitar da mace? Ai abin murna ne dan haka ya ce" Ka san mu a nan iyaye na iya yankewa y'ayansu hukunci kai tsaye kuma su yi biyaya (uhum anya kuwa sarki ya san su waye Ogas familly?), Idan ya yanke aka yi ba zata taba tada kai ta nuna dan mi ba, gashi ya ce baya so a yi a kofar gidansa dan kar yan anguwa su ringa zaginta cewa yawon banza ta je abokin yin ya biyota ya aureta, ya fi so ya koma masu da maganar ai mijinta ta runguma , ka san lamarin wajen namu kennan, sannan a ganina kaima a yanzun ba zaka so a yi wani hayaniyar da duniya zata dauka duba da mamansa a asibiti, bama zaka samu nutsuwar yin hakan ba, shi din kansa ba zai samu ba" Pah ya gyada kansa yana fahimtar maganar sarki domin shi yana cakuduwa da sarakan kasashe daban daban yana fahimta cewar kowace kasa da irin nasu al'adun, hakan ya sa sam bai ji wani abu dangane da lamarin da Oga ya gabatar ba, sannan adini bai hanna ba bale ace adini ya hanna a daura aure dan ba'a shirya bidi'a ba, dan haka ya ce" a fara shirin dukan abinda ya dace, a yi jiran saukar jirgin karfe biyar in sha Allah, za'a daura" Daga haka suka yi salama Pah ya yi shiru ya shiga tunanin wa ya dace ya tura wakiltar daurin auren gudan jinninsa? Waye ya dace ya tura? Kanninsa kuma dan uwansa daya ya rage masa shi kuma ya bayana kansa a matsayin wanda yake adawa da au baki daya saboda kujerar sarautar, idan har ya tura shi lalle ya tura Hanja a bakin kura da kansa kennan? Mikewa ya yi gannin lokaci na dan tafia dan ya lalubo ya ga wa ya dace ya tura kiran asibiti ya same shi da gagawa 11/14/21, 12:54 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*
Chapter 104 · 0% Book details