Sashe 35
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
yar kasarsu? A mutunce duba da wanda ya damkata a hannunsun mai kasar ne ya kuma jadada kan ta kasance kwarariya a aikinta dole zasu kula su yi taka tsantsan ta yadda zai kasa ganeta koma me dinsa ce a tausashe sannan a mutunce cikin yaren turanci , irin kwararan nan da sai da ta dage ta saurara da kyau kafin ta gane me take fadi ta ce" ki taso mu tafi cen school din" Sai da ta kikifta ido kafin ta karra gyara zamanta tana kallonta ta ki yi mata magana sannan ta ki tashi Karasa shigowa ta yi ta zauna kusa da ita ta karra tausasa kalamanta sosai ta ce" ki yi hakuri zai dawo da wuri, sun tafi saudiya ne da mahaifinsa da mamansa, ya ce mu kula da ke sosai a makarantar ta yadda zaki goge ki iya komai na aikin hostess kin fahimta?" A hankali ta gyada kanta duda bata san wa ake baa hakurin a kansa ba, abinda dai ta sani shine kawai zata bi su, ta je ta koyan, tana kwarewa a maida ita kasar iyayenta dan ba zata zauna a garin nan ba , ta ina zata iya rayuwa da arnawa Da dan sosinta take biye da ita da sauri dan gaba dayanta a tsorace take balema da ta fito waje ta ga garin ya ganta Wata galeliyar mota ce wani soja ya bude suka shiga kafin a ja su a yi gana da su A yanzun kam makarantar da aka zo da ita sai ya zamana tsoron fitar da kafarta waje ya kamata dan tana tsoron ta taka ta saka masu dati Wasu mata ne a tsaye su uku kowace cikin shigar dogon wando da riga da dogon takalmin hils sunna jiran fitowarsu Da mamaki suke kallon Muneerath tun daga sama har kasa kafin su ringa kallon junnansu Babarsu ce da kusan idannuwanta kadai ke nuni da ta dauki shekaru sosai sai ko wuyanta da ya dan nuna shima da turancinta ta ce" ina yarinyar ne?" Wace ta kawota ne ta nuna mata Muneerath dake tsaye ta hade hannayenta a jikinta tana ta waige waige cike da tarin kauyanci da tsoro kafin ta maido dubanta kansu taga suma dukansu ita suke kallo sai du ta tsargu ta tsinci kanta da hade kafafuwanta waje daya kamar mai jin fitsari Kai babar ta dan juyar kafin ta nuna da hannayenta ta ce" Me da me yake bukata gyara a tare da ita?" Wata kyakyawar budurwa ce da cikinta tamkar zai hade da bayanta itama da kula ta ce" da farko dai fatarta, tana da kalar fata mai kyau sai dai hankalin fatar ba a kwonce ba, ba santsi ba alamun laushi, sai fuskarta tana bukatar gyaran da zai cire mata wannan fari farin abin na hancinta da wajen idannuwanta, tana da lebe masu kyau sai dai basu da laushi, gashin dake kwonce a kusan kunnayenta sun nunna yana da kyau gyara ne yake so, tana dauke da manyan bombom dan suke da bukatar kara rike kansu, sai matsalar tumbinta da dole a yi aiki kansa, sai mu dawo kan gwuiwar hannayenta da tafin hannayenta da faratunnanta sai wajen farin idannuwanta da yake da duhun haske yana da bukatar ya samu gyara, ni dai iya abinda na gani kennan" Dubanta ta maida kan dayar itama ta matso sosai kusa da Muneerath da ta saki baki da hanci tana kallonsu da mamakin wai du ita ce ake zancenta ko wa? Ai kam zata masu barin mahaukaciya a wajen nan idan suka nuna ita din kazama ce, yo kaf gidansuma waye yake wanka biyu in ba ita ba? Dayar ta ce" tana da matsalar tafia da dogon takalmi idan kun kula kafafuwanta sunna da matsala" Daga su har Muneerath din sai suka kai dubansu kan kafafuwan nata, da sauri ta dago gannin matar ta amshi waya tana maganar ttana son gannin docter kafin ta kale su ta ce" Gimbiya Aleesa ce ta ce ta zama perfect......dan haka zata zama perfect " Tana gama fada ta yi gab Daga wannan lokacin Muneerath ta shigo sabuwar rayuwa, Watau tana gannin rayuwa mai sunna rayuwa Airfa kala daban daban ta yau da kulun , ga wankan da ake darza mata ita kanta ta san da ace faa na kodewa dan wanka da tata ta gama kodewa , Hakowaranta kansu sai da aka sake koya mata yadda zata wanke su Abinda ya fi bata takaici irin yadda ake koya mata magana, yo in ba iskanci ba yaya ake so ta zama ne wai? Duwawunta kuwa haka za daura masu wani abu kamar igiya a tsayar da ita a kunna ya ringa rawa a jikinta Baban bakin cikinta cin abinta lokaci gare shi, kuma zaba mata ake, sanan bashi da yawa, tana gama ci ake bata wani hadin su lemun tsami ta sha ba dan dadi ba sai dan wahala Cikin nan nata da take alfahari da shi ne yake lumkewa yana shigewa sanann ana shafa mata abun nankarwa dan kar aje mai fitar da nankarwa ce fatarta ta fitar ta lalata mata fata duda bakin fatarta ba mai gagawar nuna nankarwa bane Yan guli guli din mamanta ne ta ga sunna dan girma duda ba cencen ba aman ta kula kumbura suke ga rigunnan mama kala daban daban a laye da pant dinsu wai du nata ne Abinda ta kasa ganewa shine a haka har yanzun bata dawo yadda babar take so ba dan da sasafe auke fita gudu tare tana karra koya mata karuwancin da ta rasa na uban menene wai du a aikin ne ko meye? A ranar da ta shiga ruwa da su kuwa su kansu sun sarawa iya ruwanta kuma sun shaida koda bata iya komai ba ta iya ruwa Sannu a hankali ta fara shiga kicin Yannayinta ya fara dauka, fatarta ta dauki gyara ta dawo wata irin bakar fata mai masifar kyau din man da maza ke hari, cikinta ya lafe sosai sai duwawunta suka kara budewa suka baje sosai abinsu gwannin kyau da su idan ta tsaya a tsaye daga sama kirarta kamar ta rihana zuwa duwawunta kuwa ta kusan kamo niki minaj sai dai basu yi girman na niki minaj din ba, kalar fatar tata kuwa kamar ta rihana din dan kuwa ta amshi guara ta kuma saje da sanyi ta yi minas da ita Tashin hankalinta bai wuce ko girkin nasarun ta kasa iyawa ba Yi ake a nutse, a rrubuce ake bata, a bayane ake bayana mata aman cikin ikon Allah ko wainar kwai da ta gwada soyawa ita kadai sai da ta kone kurmus tana shawarar ta soyu bata soyu ba! A haka take tare da mutanen nan da suke darajata ko dan wanda ya bada ita, sai kuma uwa uba su din sunna daraja kowa din ne Kusan watanta daya kennan tare da su bata ga kowa nata da ya kawota wajen ba, a yanzu ta fara damuwa da son gannin Sir dan ta tabata shi din zai kaita inda ya daukota ................................................ Gaskiya ne, masu abu da abinsu, A wannan kwanaki HANJA da iyayensa sunn zaga kasashe masu yawan gaske, sun yiwa saudiya shiga biyu kafin su fara shirye shiryen dawowa kasarsu A yau bayan ya dawo daga masalaci ya zame a falon da iyayensa ke zaune ya nemi waje ya zauna cike da gajiya yana kallon mahaifinsa da ya ga ya kura masa ido yana kallonsa Abansa ya yi takwaf takwaf da fuskarsa a sanyaye ya ce" 11/14/21, 12:47 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*