Sashe 44
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 3 Maganin warin hamata a saukake shine lemun tsami, ka yanka shi gida biyu ka gurza a hamatarka kafin ka shiga wanka, kana shiga ka wanke kamar yadda ka sana wanka shine maganin warin hamata da dukan wani lungu idan kana so, sannan bashi da wani aibu, kuma ba dole kulun sai ka yi ba yana iya yi maka kwana hudu bai dawo maka da bugawar hamata ba domin wani sa'in da turaran da komai aman idan aka sha rana akan hadu da bugawar hamata har kai da kanka ka ringa jin sai a hankali jikin naka, to ba wuni a rana ba ko a ina ka wuni idan ka yi haka ba zaka yi warin hamata ba komai zufar da zaka yi Bale mu mata, mu sani turarukan nan na hamata akoy masu mugun karfin da suke balo ciwon nono boyaye, na gani da idona matar da daga fesa turaran fesawa na hamata hamatar ta dan kaikaita mata sai zuwa nono daga nan kafin dare nono ya sundume nata ashe tana da kansar nono bata bayana ba, wannan turaran ya bayanar da ita da karfin gaske, danma hannu da shuni aka fita da wuri karshe dai sai cire shi aka yi .....wannan ciwo ne kuma haka Allah ya kadaro mata ....aman akoy musababi, turare a hamata bashi da kyau bale irin na kantin nan na fesawa...........mu bincika dan tabarwa.....na gode Sun dauki lokaci a hanya kafin suke karasawa wajen aikin Kasancewar waje ne da hanyar ma'aikatan wajen daban da ta passinger sai bata gane ta kofar da suka shiga ba, abinda dai a yau ta samu kanta da yi shine admirern abinda idannuwanta ke ganni domin a yau tar take gannin wannan duniya tasu da idon basira, a yau da hankalinta yake jikinta ya kasance wannan doguwar tafia da suka yi sam bata kula ba dan idannuwanta na nuna mata duba irin na mamaki Yan karafunnan dake bakin hanya idan suka karaso sai direban ya rage gudun motarsa sosai sai karfen ya yi kasa kafin su bi su wuce, haka idan suka tunkaro wajen duwatsu masu tsini summa sai su kauce kafin su wuce kafin su fara isowa wajen camerar da du idan sun tsaya sai ya zuge gilas din gefen da take camerar ta dauketa da kyau kafin ta nuna wata blue din wuta sannan suke sammun shigewa idan ta nuna ja kuwa baka isa ka taka gaba ko kace zaka yi baya ba domin idan bayan ka ce zaka yi da gudu wadinnan abubuwan da ka wuce ba zasu kau a hanyarka ba dan daga cen za'a hanna hakan kafin sojoji su tarboka da bindigunsu .....wannan abubuwan na cikin tsare tsaren bada kariya wa ma'aikatan wannan ma'aikata wanda ba wai dan kawai muneerath na sanye da suturar Hostess dinsu bane ya saka suka samu shigewa ba, no dan akoy hotonta da computer ke ajiye da shi sannan sunna da sannin cewa yau zata fara aikinta A haka har suka karasa wawakekiyar rumfar ajiye motocin da ta ga motoci sun fi a kirga a kimtse wula wula da su hakan ya sakata karra yin sharan da baki tana kallo har sai da ta ji an bude mata bangaren fitowarta kafin ta daga kai ta kalli sojan da ya bude mata yana jira ta fito daga motar Irin shigarsa take karewa kallo tun daga irin hular dake kansa da kuma farar wukar dake hannunsa wace ta tabata ita ce makamin dake tare da shi kadai , shigar kakin jikin sojojin oalas din ba iri daya bane da na sojan cikin gari, hakama hulunnansu ba iri daya bane sannan su ba kowane ne ke rike da bindiga ba, wa'inda ke rike da bindigogi iya wa'inda ke yawa da Hanja da ko da Sarki ne, suma gugunsu da yawansu bamgarensu daban , salarrynsu daban domin ko formation din da ake basu ba iri daya bane da wadinnan Dan murmushi ta yi a lokacin da ta ga wani dan hancinsa zuwait da shi a bayane ta ce" Allah daya gari bamban, su kiwa ga irin nasu dogarin " Shi dai a yadda ya kame mata bai ajiye ba sai da ta fito kafin ya rufe ya kuma shiga bin bayanta tamkar jela fuskar nan tasa a hade kirin da ita Da mamaki ta ja tana kallonsa kafin ta ce" Kaini zaka yi wajen? Ka ga kuwa ban san inda zan bi ba" Da yannayinsa na bata girma ya ce" eh aikina shine na nuna maki hanya sannan na baki kariya a du inda zaki je " Ido ta ruko tana kallonsa a zuciyarta tana maimaita kalmar kariya? Gannin ya nufi wata kofa ya dana wasu butom kofar ta bude ya saka ta biyo bayansa ta shiga kafin shima ya shigo da sauri ta dora hannunta ta rike dan karfen ailbar dake jiki dan ra kula irin na Palas ne mai yin sama ko kasa da bawa ya tsilira shi a yan sekwani, kai ita dai tana gannin garajen dan adam yanzun idan ya makale da kai kuma yaya zaka yi? Shikenan ka mace ko akoy yadda ake yi? Sanyin kamshi da ya buso ta da haske ne ya sakata tsayar da tunaninta a lokacin da suka bayana a cen sama wajen baban filin taron ma'aikatan A hankali ta sako kafarta waje tana kiftawa tana kallon yadda mutane ke kai kawo, gaba daya wajen sai ya so sakata juyawar kai domin waje ne mai girman gaske ga kuma mutane maza da mata sanye da suturu yawancinsu sanye ne da irin suturar dake jikinta ko kuwa dan bingilalen sket ko dogon wando irin dai kayan sweet na maza aman kowace ka kala kayanta kamar sabo dal domin ba alamu na yamutsa ko na dati a jiki bata dai san kuma bangaren wari ba, sai dayan abin takaicin ita dai bata ga daya mai kai a rufe ba, gaba dayansu kawunnansu a bude suke haka kuma irin yadda suturun suka matse su kamar da sun yi wani wawan motsi zai yage Mazan kuwa sanye suke da nasu kalas costume din watau swt baki dayansu ba mai jalabiya ko mai riga da wando na dinkin yadi ko shada, bambancin suturarsu daga color ne sai ko tsada aman baki dayansu sun sha karanpasan swtt dinsu gasu farare har idannuwanta sunna neman mata ciwo kafin take hango yan tsirakun kalarta a cikinsu, haka kuma yannayin mazan su sai ya fara sakata a tunanin to ko dai baki daya mazan su kyankyasar inji ne? Dirka dirka da su malan sai dai a yannayin baban jikin akoy mai kyau akoy kuma wanda zaka ga kawai ya yi wani sandandam, wani kuwa da katon tumbi irin an ci an tada kai a kasar nasaruma Sai da ta gama kauyancinta ta kula ba wanda ya damu da ita kafin ta juyo ta kale shi yana tsaye ita dai yake jira ya ce" An ce na kai ki asibitinsu sai an gama maki binciken lafiyarki sannan ku tashi kunna da tafia nan da awa uku da minti goma sha bakwai" Ajiyar zuciya ta sauke ta bi bayansa suka nufi cen ciki Sun dan yi tafia kafin su karaso wajen, daga sama an rubuta sunnan dake nuni da wajen likitoci ne da inglish , nan ya ja ya tsaya ya yi mata nuni da tana iya shiga Sai da ra waiga kafin ta yi adu'a ta saka kanta Dan ja ta yi ta tsaya tana karanta waje waje dake rubuce har ta kawo kan wajen dake bayanin nan ake gannin hostess hakan ya sa ta yi murmushi ta karasa ta dan kwankwasa ta tsaya har aka bata damar shiga bayan an dauki lokaci sannan ta dafa abin ta bude ta shiga a hankali Sama sama muryarsa ce ke bada dadadan amo cikin yannayi na yana yin fada fada , bayansa ne ya ba kofar hakan ya saka ya miko hannunsa ba tare da ya juyo ba ya ce" John bani " Tsuru ta yiwa hannun nasa da kuma idannuwan da suka sauka a saman kanta na tsararun yan matan dake laye au biyar , sai uwa uba SIR da ta gani yana tsaye cen gefe shima cikin yannayin nan nasa da yakan yi masu a Nijer idan yana cikin aiki Zuciyarta ne ke dukan tara tara , tarin tsoro ya darsun mata a kasan zuciyarta na abinda ka je ya zo duda ba fuskarsa ta gani ba aman ba zata manta yannayin gashin kansa da irin tsarin kirarsa ba A hankali ta lumshe idannuwanta nan da nan ta kamo abinda ta tabata ba dai mutun ba sai dai idan Allahn ne ya kadaro mata samun matsala d a wani a nan ta shiga yi shine adu'ar neman tsari ga dukan abinda zai iya cuta mata Da karfi ya juyo dan jin shiru bayan ya mikowa John hannu kan ya bashi takardar da ya saka shi daukowa dan yana so ne a masa bincike na kirki a kan su domin tafiar da aka yo da jirgin ghana an tafi da biyu a yannayi na maye, hakan ya sa ransa baci yau tunda ya shigo yake balbale au da masifa wadincen din ya kore su ya saka kuma an kaisu centre dan a yi traitment dinsu, hakan ya sa ya shigo yau komai a gabansa za'a yi bayan wannan aiki da ake masu mai yawa ne ga takale takale sai a hankali dai A kan fuskarta da ta bayanar da yannayi na tsoro ya sauke fuskarsa Da sauri ya cire da dubansa sakamakon bugawar da tasa zuciyar ta yi , sai dai cirewar ko second biyu bai bari ya yi ba ya maida saman kan fuskarta Maganar da yake yi ne take kai kawo a makogwaronsa , lokaci daya ya ji hankalinsa na neman tashi dan ba komai ya saka a ransa ya buga masa da zuciya dan ya kalli fuskar wannan rusheshiyar ba sai dan tana muguwa lale lale tana tare da wata mugunta ne, hakan ya sa ya maido dubansa cikin nata tar kafin ya ya iya jimke hannunsa da yake wuwurgawa yana fadan ya lumshe idannuwansa ya bude ya sauke a kan John da ya shigo dalilin gannin kofar bata rufe da