← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 114

Sashe 113

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 7 *ALHAMDULILAH, ALHAMDULILAH, ALHAMDULILAH, ALHAMDULILAH, ALHAMDULILAH* A washe garima wunnin gyara akaiwa Muneerath, a wannan rana kuma mahaifiyarta da kanwarta na gefenta, haka kuma aminiyarta Amina da ta dawo daga bautar kasar da ta tafi ta samu labari ta zo kuma an bata damar shiga, hakan ya sa anai mata gyara bakinta ya ki ya rufu da ita da aminiyarta da kuma Saudat Murmushi Amina ta yi tana girgiza kai ta ce" Tabas idan ka ji maraya rago, haka kuma lamari na ubangiji babu yadda baya kasancewa, idan Allah ya tsaya maka zaka hadu da alkhairin rayuwar da baka taba tunanin cewar kai din jan zaka samu kanka a ciki ba" Muneerath dake zaune cikin rufa ta bargo mai nauyin gaske anai mata hayaki marar yawa yana ratsata ta lumshe idannuwanta ta yi murmushi ta ce" Allah , shi ke gyara tuwon makaho, nakan yi tunanin ko barci nake na ringa mafarki irin wanda na saba?, Sai dai sensation din dake fito da kanta a zahiri kan sakani karra buda idannuwana, Amina HANJA ne mijina....kuma baya minti biyar idan muna tare bai ce min yana so na ba, na rasa ni me zan ce masa ya faranta masa, Allah ya wanke sarkin dogari ya bani" Amina ta yi yar dariya tana kallon Saudat dake murmushin hirar tasu ta ce" Babu irin abinda ba'a cewa a kanta a kan dogari da son zama HOSTESS, ni kaina mun sha yin baran baran a hanyar makaranta idan ta tsayar da tafiyarmu ta dauko magangannun nan, sai na ga ta yaya? Ta ina?, Muna aji muna daukan darasi ta ce zata je gida kanta na ciwo, daga nan ban kuma ganninta ba, Oga ya ce wai ya samu waya wai ko za'a dauketa aikin masu raba abinci a cikin jirgi ko me?, Tun ina sa ran ta bilo har na zubawa sarautar Allah ido, har na yi tafia harkar bautar kasana a shekarata ta biyu, kin ga MUNEERATH ta cinma burinta a saukake" " Ke ba a saukake ba kam, da adu'a ba dare ba rana, da naci, da kafiya, Amina na ga abubuwa ciki harda gani ga zaki.......kin san Hanja kiwon zaki yake yi, a ranar na fara dane jikin namiji da kaina " ta fada tana kauda kai Amina ta girgiza kanta ta kalli saudat ta ce" Halin na nan " Saudat ta ce" Ba zai kau ba kam har abada" Dariya sukai su dukansu A tare suka wuni, sai wajen yama aka ce ga Oga ya zo tafia da mama Ai kam ta sha mamaki a lokacin da ta fita ta ga wani dan uban shada da Oga ya sha da wani gilas baki da hula harda agogo Ido ta zuba masa da mamaki ta ce" Oga a ina ka samu kudaden nan na shiga uku" Oga ta ce" To Allah ja da ranki hala ji kike na sadakin naki ne nake kashewa? To bari ki ji kyautar uwa da ta uba da aka bamu sai mu siye kaf anguwar nan da ita, bale kin ga mijinki da yake cen waje yana hawaye wai ko mamansa ta farka har sun yi vido cull ko me na ji sunna fada, ya tashi ya mike ya zaro takarda ya bani fara, kur'ani juwa da ta dibeni na kusa summa na zata ya karki ne, sai da aka duba min aka ce ai ba wannan bane, kudade ne ya zuba wai na godiyar na bashi y'a, walahi Yar oga sai gani ina so su barni na kai gwuiwoyina kasa na yo godiya sunna rikeni sunna hannani, kai na ci kuka na sha hawaye kamar ba gobe" Muneerath ta girgiza kanta kawai , inda mamanta ta karra jadada mata abubuwan da ta fada mata a ciki na dangin su nasiha da kula da miji da sauransu, ita kuma ta ringa gyada kanta tana murmushi ta raka su baban filin wajen tanai masu byby abinta kan cewar ai ko gobe ta so ganninsu zata dawo ita da Hostesss ce kulun sunna cikin tafia Ita dai Amina bata ce mata komai ba, hakama Saudat, suka koma ciki har lokacin da Hanja ya dawo ba a yadda akai zai dawo ba Da farin ciki mai tsanani yake fada mata cewar Mah , Mah ce ta farka, Mah har sun yi vidio calll, Mah ta rikice da farin cikin jin ya aureta, haka kuma ya amshi sarauta, gaba daya ya nemi rikice mata da son rukunkumeta a gaban au Saudat salon a yi gaba da ita a ce itama ta fara raba hali ta dauki halayan da ba nata ba watau Inda suma suke kakawar da kai domin su dai a kasarsu ba'a sakin jiki a yi haka a gaban wani koda kuwa matarka ce Gannin ya kasa samun kanta ya dauketa cidak ya yi ciki da ita, a guje suka fito sunna zarro ido kafin su bushe da daria Saudat na fadin" Kalarta irinta Allah ya bata abinta " Amina ta yi murmushi tana girgiza kai ta ce" Tabas Allah na aiki da zuciyar bawa, Allah ya basu zaman lafia ya sa su kasance har a gidan aljanna cikin dankon soyaya da kula da junna" Dukan wani masoyi ya kasance a cikin yan rakiya, Rungumarsu take tana fada masu cewar zata dawo a gobema idan tafia ta kama su, shi dai yana biye da ita sai ya yi murmushi a ransa yana ayana' haka fa ' A cikin yar taf iyar da suka yi, wada a cikin jirgin da a tunaninta iya su ne sai masu masu hidima , aka kara shirya shi kafin ya bude wata akwati da kansa ya sake ciro wata alkyaba mai ruwan zeba mai kyalkyali sasauka ya rufa mata a kan shigarta ta duguwar rigar lesh mai ruwan duhu da dan haske hasken fari kadan a jiki Fuskarta ya karra kurewa da kallo yana jin ko a yanzu yana iya maimaita abinda ya yi jiya da dare da ita Kanshin da take fitarwa na saka masa nutsuwa hakama kalar nutsatsiyar kwaliyar da akiwa fuskarta na saka masa jin nishadi idan yana kallonta Daurin dan kwalinta ya karra shafawa yana ji a ransa sun masa adalci , sai dai baban burinsa ya saka kafarsa a gidansu ne, zai ce da Mah dan Allah ta saka matarsa a irin suturar da take sakawa, shi kam yana ga wannan shiga ta Mah dinsa itace shigar da ta fi dacewa ga kowace mace, rufe suturar jikinta zai sama masa nutsuwa A hankali ya mana mata kiss a goshinta sannan ya dan lankwashe hannunsa kusa da cikinsa ya sanyo nata a ciki ya juya ya fara tafia da ita a hankali Gaba daya idannuwanta ta wara, hakama dukan wani tunaninta ya nemi iyakancewa a lokacin da ta ga duban al'uma a laye a tsare, haka kuma manya manyan dakarun sojoji da bindigunsu wasun shigarsuma ba'a gannin fuskarsu sai iya lebensu da idannuwansu sun zagaye ko'ina sun rufe ko'ina A hankali ta karra matse masa waje ta dan dago dan kallonsa Sai dai yannayin fuskarsa sai da ya saka gabanta faduwa Girma, daraja, ni'ima, duka ta ganni a fuskar mutumen dake dawainiya da yi mata hira ba dare ba rana, mutumen da ya bita har anguwar su oga ya bayana mata sirrin zuciyarsa, gaba daya sai ya so rikide mata ya cenza mata har ya kai daidai wani waje da zasu hau ita bata sani ba har sai da ya dan sasauta rikon da ya mata ya taimaka mata ta ankara cewar wani wajen ne zasu hau Ajiyar zuciya ta sauke ta hau suka karasa gaban amsa kuwar da aka tanadar da wani farin teburi dan dogo da tissu a ajiye da dan abin goge hannun nan A gefensa ya yi mata waje, a nan ta sauke dubanta a kan mutanen dake gabansu wa'inda suke tsaitsaye kowa cikin kyakyawar shiga irin tasu, watau mazan da suit, matayen kuwa daga mai dan bingilin sket, sai mai dan wando da riga dai da sauransu , haka kuma du sun saka huluna yawanci da dan flower a jiki mai kyau ba kalar na zuwa sutura ba Namijin dake tsaye da takardar da akai masa rubutu ne ya mike ya gabatar da barka da zuwa wa sarki da kuma sarauniyar kasarsu, tare da nuna tarin Flowers din barka da zuwa da aka ajiye masu da kara yi masa barka na daurin aurensa, da sheda masa cewar sun tanadar masa biki na musaman idan ya huta tare da iyalinsa Sannan ya bada damar a haudo surprise dinsu Ai kam wannan surprisd din da aka tanadar masu baki daya ba komai bane sai Mah da PAH ke turata a saman kujerar tura mararsa lafia, domin ba wai garas ne ta mike kai tsaye ba, sai dai tafoar ce bata iya yi da kanta sai a hankali Farin ciki, murna duka sun bayana a saman fuskokinsu, a hankali ya duka a gabam kujerar ya kama hannayenta a sanyaye ya ce" Mamanah" Mah ta hade daria da kuka tana shafa gefen fuskarsa sanann ta riko hannun Muneerath ta hade da nasa ta ce" Jarumina, albarkana " Su dukansu murmushi suka yi suka rungumeta, itama tana dan taping din bayansu sannan ya furta" Kin ga ya tirsasani ko?" Pah ya yi yar dariya yana karra kallon mutanen dake gefe da gefe Mah ta ce" Ya min adalci , ya cikan burina " Sai da suka gama farin cikinsu sanann ya samu kansa da maida kansa da kansa ya fuskanci al'umar dake sauraron bayanansa Dan murmushi ya yi ya karra duban wajen su Muneerath ya kafeta da ido kafin ya dan girgiza kansa a sanyaye ya ce" Tabas na ji tsoro mai karfin gaske a yan kwanakin nan da suka wuce da barazanar rasa mata biyu da suka fi soyuwa a zuciyata da duniyata ta tunkaro ni, sai dai gashi yau sunna gabana tare da ni sunna kuma saurarata, Ban san ko na cencenci zama sarkin kasata ba?, Domin ba dan ka zama prince ne zai zamana dole kai ya dace ka mulki kasarka, sai dai abinda ma koya a yan kwanakin nan sune sannin darajar lokaci, anfani da shi, mutunta dan adam, kare hakinsa, yabawa kokarinsa, talafa
Chapter 113 · 0% Book details