← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 114

Sashe 63

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 4 Hannun nata ya warta a lokacin da ta afka a duniyar tunani ba tare da ta ankara ba ya damka ya kuma mikar da ita Ido ta kwalalo domin da dayan hannunsa ya saka a wajen kugunta ya karra mikar da ita sosai ya matso da ita dan daf da shi kafin kansa a gefe ya shiga tafia da ita da dan hanzarin da ya saka ta saka katabus sai tafiar da yake yi kawai da ita har ya fice a cafetariar baki daya kafin ya bude motar da ya zo da ita ya turata ya zagaya da dan sauri ya bude ya shiga ya tayar ya harba kan titi Idannuwanta a waje suke, gana daya numfashinta sama yake yana kasa da wani irin sauri tana wuki wuki sannan ta kasa zama waje daya sai ta yi kamar zata kama ta bude sai kuma ta ji hannayen nata sun kwashi wani irin bari tamkar ba zasu iya dannawa su bude mata ba Haka tana ji tana ganni ana watsa masu hotunna Sir na tsate yana binta da kallo hakama Kawarta Hanja ya ja motar nan ya yi gaba fa ita Wani masaukin ya nufa da ita, wanda yana tsayawa ya bude motar stil bai tsaya ya yi jiran ta fito ba ya kuma damko hannunta ya nufi ciki da ita Wajen dauke yake da dan fili daya kwal zagaye da gilas da alamu shine zagayen gidan wanda baya hanna a ga mutun dan yana ciki haka kuma wajen kamar shi kadai ne kwalin kwal a ajiye Ciki ya nufa da ita ya saka hannunsa ya danna cod din wajen kafin ta tura ya bude ya shige da dan sauri da hannunta wanda take ji zuwa yanzu tana ga ta karye nema Da dan karfi ya hankadota da hannun nata da ya riko, hakan ya da ta yi gaba tagal tagal ta je ta kifu a kan kujerar dake falon kafin ta dago a firgice tana kallon irin hararan da yake binta da shi Makwar ta hadiye yawun wahala tana jin kamar zata hira ta gudu dan tsoro ne fal a kasan zuciyarta na yannayin wannan mutun Kai kawo Hanja yake da wayar a hannunsa android yana ta tunanin yadda zai yi da ita A hargitse ya juyo kanta a lokacin ne kuma kira da message kala daban daban ke shigoea wayarsa Kiran ya fara dagawa domin na lauyan gidansu ne Shiru kawai ya yi yana sauraron abinda lauyan ke fadi cewar ya ga hotonsa yanzu yanzu an dora da wata wai matarsa ko budurwarsa duniya na son karin bayani, shi da baya yarda a dora hotonsa irin haka da mata menene kuma ya hada shi da aikata hakakodai budurwar tasa ce da gaske? Hannunsa ya daga ya kai wajen goshinsa ya dafe cike da takaici ya ce" AA " Lauyan nasa ya ce" Ok ina zuwa bara na dakilar da yade yaden sannan na ba yan jarida amsa, domin sunna ta tambaya ne dama kana fita waje ne ka yi yawo da mace a sake baka yi a kasarka? " Kit Hanja ya fara kashewa da sauri ya shiga yanar gizo dan tabatarwa kansa Hotunna kaloli ne aka yayada a wannan dan mintunnan har ya zaga ya kai wajen manyansa A hotunnan wa'inda suka fi bashi haushi sai wa'inda aka nuno karara ya riko kugunta da kuma dayan hannunta kam sannan ya janyota jikinsa sosai kafin ya fara tafia da ita Tabas du wanda bai san ba wani abu tsakaninsa da wannan yarinyar ba dile zai ce wata dinsa ce Da takaici ya ajiye hoton a gabanta ya zauna ya rafka tagumi yana kallon yadda take binsa da kallo a zaune dangalgal kafafuwanta a hade waje daya gaba daya jikinta na bari bari tana kallonsa a mugun tsorace, gashin kanta a fili dan dan kwalin ya zame, zufa ta jika gaban goshinta hakan ya sa gashin nata ya liliku a gaban ganta , sai idannuwanta dake yawo a fuskarsa da dakin , wannan kwayar idon ta kara girma tana ta yawo a jikinsa Hannayensa biyu ya rafka tagumin da su a lokacin da shi kansa bai san tagumin ya yi ba yana binta da kallon haushi da tunanin yaya zai yi da ita Ransa bace, sai dai muryarsa da sanyi ya ce"me ya kawo ki rayuwata? Wani ya aiko ki ne ki hada min ciwon kai?" Muneerath ta yi gagawar girgiza kanta tana kallonsa ta hade hannayenta ta ce" Walahi ka ji na rantse maka ni ba wanda ya turo ni, ka manta kaine da kanka ka dauko ni a garinmu?" Hanja sai kawai yake bin yannayin da take maganar da kallo Lebensa na kasa ya cije da tarin haushi ya ce" Dubi haukan da ake dorawa wai ni Hanja wai ke budurwata ce ko matata? Sai nake ji kamar na yankaki na birne a wajen nan na huta" Jikin Muneerath ne ya kuma daukan bari da sauri ta dauki wayar tana dubawa kafin ta ahiga girgiza kai ta kuma hade hannayenta ta ce" Kayya, kayya, aman wanda ya yi wannan munafuki ne kuma ba zan yafe masa ba koda kabarinsa zai kama da wuta balbal, dan Allah kai ai ka san ba wannan tsakanina da kai, maganama ni da bana maka tun ranar da ka shakeni ina zaman zamana? Ka min rai kar ka kasheni Oga bai ganni ba, ka yafe min wannan gangancin da aka ce wai ni din nan budurwarka, ka ga fa da saurayina walahi nima ba zan taba yarda da wannan maganar ba wa'indama suka dora basu da hankali ne, aman dan Allah kar ka yi maganar kasheni a kasar nan ka maida ni kasarmu na tarda iyayena na rayu da su, ko yau na bar aikin Hostess na ci riba domin zan fada cewar aikin nan na taba dandanawa " Tana magana ne tana dan kusanto shi da daga yan yatsotsinta masu dauke da faratuna farare tas ba digon abinda yan matan kasarsu ke sakawa farce musulman da kafuran, hakama hannun nata baya dauke da dogayen faratuna, sanann sai ta hade hannayen nata ta kuma rungume a kirjinta Fuskarta da furucinta gaba daya sai suke masa nuni da yarinyar is innocent, tamkar yarinyar da bata san komai ba Idasa zama ya yi a saman cafet din wanda shi da kansa bai san ya yi hakan ba A sanyayen da bai sanuryarsa har ta kai haka sanyi ba ya ce" Kin tabata idan nace zan maida ke kasarki daga nan zaki yarda? Na saka ki a wani jirgi ya kaiki?" Muneerath ta koma dan nesa da shi ta zauna tana ta ahiyar zuciya a hankali ta gyada kanta kuma tana kallonsa ta ce" Wanda zai tashi idan ya taka biredi ai ya rage, bale har ya samu hawa bene? Walahi ko a yanxu aikina ya tsaya alhmd zan koma na cewa mamanmu mafarkina ya tabata, na samu biyan bukatana, zan cewa kishiyar mamanmu nice na taka kasashe hudu na duniya ina aikin da ya zamo burina, sannan zan nunawa oga da ya ce ya san ni ba mahaukaciya bace kuma yana tunanin idan na yi kokari ina iya zama wani abu a yayansa cewar lale na je na taka jirgi kuma na yi aiki, ka ga sai na dauko takarduna na ci gaba da karatuna a university" Lebenta da take hadawa tana dan warewa idan tana maganar yake kallo , sannan yana dora kowani furucinta a kan ma'auni yana aunawa A hankali ya cire dubansa a kanta cike da mamakin kansa So yake ya hanna kansa ci gaba da yi mata magana dan yana so karfi da yaji ya karyata cewa yana jin dadin yin hira da ita a wannan lokacin harma yana son sannin dukan amsoshin tambayoyinsa dan a ganninsa a kan meye zai ci gaba da magana da parfait inknow haka ba gaira babu dalili, sannan yarinyar da a tunaninsa du dunia babu wanda ya raina shi irinta, yanzu haka ya tabata dan ta ga daga ita sai shi ne yana iya karya mata wuya har take mada magana, da ace a kusa da Mah ne da bai san yaya zasu kwashe ba A hankaki ya juyo ya ga kamar zata dauke shi da ido, duba ne na tana son karantar a wace suke ciki, zai mata ilan ne ko zai sasauta mata A hankali ya cire dubansa yana fadin" Ki daina tsareni da ido " Da sauri ta cire idannuwanta a kansa, a kasan zuciyar Muneerath adu'a take tun karfinta kan Allah ubangiji ya rufa mata asiri ya rabata lafia da mutumen nan, ita dai ta san bata taka masa ba, bata karya masa ba, aman ya tsaneta kamar wace ta masa wani mugun abu, A hankali ta kara juyowa zata kuma kallonsa ta ga ita yake kallo hakan ya sa gabanta ya fadi ta juyar da kanta Walahi ba zata taba mantawa da wata bugawa da yayarta ta mata wani lokaci da aljannunta suka tashi, watau tsayuwa ta yi sunna fada sai ta ga ta kureta da kallo ashe ashe abu na kusa tana kyarara ihu sai ta warci Muneerath din ta doka da kas....kafin dai ta ankara ta gudu ta kara balata, wannan shi ya sa a yanzu ta ji gabanta na dukan dari dari Idannuwansa sun yi ja kamar ba nasa ba, hakan na mata nuni da abin na kusa Inahu sulaimana wa inahu bismilahi rahamanin rahim, Allahu la'ila ha ilahu, alhayul kyayum....... "haka mamanki ke cewa baki da hankaki dan kina son zama Hostess?".......maganar da ya ji yana fada kennan, wanda itama ya sakata daina adu'ar da take a kasan zuciyarta da sauri tana kallonsa Kanta ta sada lokaci daya tana tunano iyayenta A hankali ta dago tana murmushi ta dan matso kusa da shi sannan ta juya tana kallon inda yake kallo a hankali ta ce" Ko kaine sai kace bani da hankali, ka ga ni ban iya girki ba, ban iya ruwa ba a lokacin, ban iya komai ba fa....bani da hanyar shiga makarantar nan dan kudin da ake biya Oga ba zai biya min ba, a haka kuma nake ikirarin ni Hostess ce" HANJA ya juyo gaba dayansa wannan karron yana kallonta, a
Chapter 63 · 0% Book details