Sashe 56
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
wanka daure da towel a kugunta gaban madubi taje dan daukar mataji ta taje kanta da ta wanke tare da abun busar da kai dagowa iman tayi dan jin mutsin muneerath din ta zubawa faffada kugunta ido ko keftawa batayi cewa take chab din gaskiya dole ma inyi wani abu akan yarinyar nan tun bata tafi da abinda na dade ina muradi a rayuwata ba oh ji yarinyar karama da kira kamar ita tayi kanta cab da sake wllh tasowa tayi ta matso kusa da muneerath din da take ta kokarin shafawa kanta data gama busarwa mai Da nata salon son kusanta kanta da Muneerath din ta ce" dan kawo na taya ki mana?" Muneerath ta dan kaleta a ranta tana ayana 'su yan gidan nan mamaki suke bani, sai su ringa shiga harkar mutun da sanyin rai bayan mu a namu gidan eh yane ne, kana kallon wanima zai dura maka ashar ya ce kallon fa? Ni du sai na ga wani salon munafirci ne sun kama yaro sun dura masa vitamine ya zama gabjeje yana yawo da yar riga a cikin mutane yana langwui......' dan murmushi ta yi tana girgiza kanta tuno tambayar da ta yiwa sir cewar wai dan Allah shi zai tuka mu? Sir ya mutu da mamakin jin dalilin tambayar nata dan cewa ta yi ita walahi du kallon wani dan baba da rai take masa, a anguwarsu kuwa idan aka matsawa mutun da sunnan dan baba da rai irin yayan nan ne da ake sangartawa basu iya komai ba sai sangarta da fada da shirme, Kumewa kawai ya yi a ransa yana ayana lalle duniya mai ba dan adam dama, lamarin rayuwar Munnerath na saka shi kallon duniya a yar mitsitsiya mai cike da abin al'ajab ......watau mai dauke da al'uma masu abin mamaki, A hankali Ta ringa taimaka mata tana dan janta da hira haka kadan kadan tana nuna mata yadda zata yi kwalliya da sauransu dake iman din yar gaye ce kwararriya ce kuma wajen iya kwalliya tuni muneerath taji dadin yadda iman din ta koya mata simple mak up wanda ya yu mata kyau ko ya zauna das a kyayyawar fuskarta Komawa bakin gado sukayi iman ta dago kanta ta kalli muneerath tace" niko in tambaye ki man ?" Muneerath ta dubeta tace "inajinki" iman tace" daman gami da dogarinki ne ni ban taba jinki kuna waya dashi ba ko irin ya kawo miki visit dinnan a bazatan nan duba da irin yadda na sha ji kina maganar dogari" Muneerath ta dago ta kalli iman irin a rikice dinnan ta turo dan bakinta tace" to ai ni dogarin ma bamu taba haduwa dashi ba sau daya ne ma wataran nazo wucewa ta kofar fadar garinmu na hange giftawar shi sa ilin da zai shige cikin fada, sai kuma a hanya idan zai wuce , sai kuma ranar da zaku sato ni, sai na nan na wasan karam da kuke cewa dogari, yo Allahna tuba dogari fa dan uwan sarki ne, shima fa rawani yake sakawa, kafar sarki kafarsa, Mamanmu ta ce idan na samu dogari na caba, jira dai nake na koma gida idan ba dogari bana tunanin zan iya aure ni kam" Da mamakin hirarta iman ke kallonta, abin mamaki, idan ta kula yainyar nan batama fara soyaya dogarin nan ba?, Da sauri ta mike ta dauko computer Muneerath din wace bata anfani da shi sam dan ita batama san aikinsa ba gaskiya, ta zauna ta shiga opperath a nutse ta hada connxion bayan ta saka cod din masarautar sannan ta kuma hada layinta ta hau google A nutse ta dora harafin sunnan Dogari tare da danawa kan africa ta shiga kallo A hankali take kallon hotonsu da irin shigarsu da matsayinsu a fadar sarki Da mamaki ra juyo tana kallon muneerath da yanxun yar riga ce a jikinta daidai gwuiwarta kanta a hade waje guda , dan mak up din da ta yi mata ya fitar da tsarin kyanta, yarinyar ta bada kala irin ta manyan hannu ce aman ta mace a son irin wannan? Sai ta samu kanta da bushewa da dariya tace "yanzu daman muneerath baki taba haduwa da dogarin ki ba, aman kike maganar mijinki dogari meye meye ki ishemu da zancen dogari ? Ta karashe tana wata dariyar ............. muneerath ko ta cika fam sabida dariyar da iman din ke mata A hankali Muneerath ta cire kanta, seriusly itama abin na damunta, a hankali ta juyo gannin Iman ta dawo gefenta tana kallonta Iman ta dafa hannunta ta ce" Ina iya taimaka maki har ki samu soyayar dogari mai kyau mai tsari wa ke kadai" Muneerath ta ji zuciyarta na dan bugawa tana kallon iman ta ce" Allah zaki min haka?, Aman ta yaya ke zaki iya min haka ke da kike nan?" Iman ta yi murmushi ta janyo computer ta ajiye ta cire wayarta kirar iphone ta gyara zamanta ta shiga Facebook tana kallonta ta ce" Baki san yanzun duniya ta yi ci gaba na mamaki ba?, Daga nan da kike zaune kina iya malakar zuciyar dogari harma ya haukace sai ke ba? Kin ga ta facebook yanzu har aure yake haduwa a kuwa sha shagalin biki a tare, kin ga abu mafi sauki kennan a yau yau ki fara hira da dogari, a hankali ki tura masa hotunnanki ki mike a haka ki karkato bombom din nan naki na maii hotuna masu masifar kyau ki karkato mamanki ki rike su ki bankaro su sosai ki yi yannayi na yarinya mai fuzga wace zata tada sha'awar namiji daga ya kaleta irin haka...." Iman ta mike ta rike mamanta ta wani gantsare ta turo lebunnanta ta cije daya ta wara kafafuwanta takashe ido daya inda Munnerath gaba daya baki da hanci bude tamkar sabon kamui take kallon iman har ta gama ta zauna ta dora da fadin" mu dora shi saman dp dinki na facebook mu ringa matsa masa har ya amshi invitation dinki daga nan mu ringa masa hira kala kala idan yana son sannin wacece ke mu fada masa ki fada masa irin son da kike masa, na tabatar maki cewa nan da yan kwanaki zai haukace maki sai kin ga dogari a kasar nan koda a kafa ne" Gaba daya Muneerath sai ta ji kanta na sara mata, wani irin takaicin iman ne ta ji na shiga zuciyarta, muryarta a shake ta ce" Ki ce karuwanci zaki koya min?" Iman ta tsaya da maganarta tana kallonta da mamakin jin furucinta domin ita dai a nan bata ga meye ya kawo kalmar nan ba Muneerath ta girgiza kanta gwuiwarta a sage ta ce" Yaushe mata suka yi arha har haka? Yaushe muka yi zubewa har haka? Yaushe musulunci ya zama abin wasa har haka? Yaushe rashin sannin ciwon kai ya cika matan duniya har haka? Anya kuwa maganar ta al'adu ne ba iskanci bane duba da koyarwar litafin daya ne?? Anya kuwa mace na anfani da karancin shekaru irin nata kuwa? Dole a ambaci mazinaciya kafin a ambaci mazinaci domin du iskancin namiji malamarmu ta pc ta ce da mu ba zai kai hannunsa kan mace ba sai ya kula cewar itama lalataciyar ce! Yanzu iman ni da ke Mah ta ce da mu ko tabamu namiji ya yi zamu dauki ciki, a nan ta ce da mu koda kowa na yawo kansa bude mu mu kasance masu lulubewa domin suturar mace mutuncinta.... aman shine kike irin wannan abin? Anya ba tambayar mah zan yi ba kuwa ke ba yar iska bace?" Iman showwwwwwwwwwwwwwwwwww 11/14/21, 12:51 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*