Sashe 31
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 2 Tana zuwa bata yi wata wata ba ta falawa fuskar Muneerath mari wace sai a lokacin ta dawo cikin hayacinta gaa dayanta ta kurawa kowa ido A yanzun ta gama yada cewa tata ta sameta, idanma suka koreta ta komawa oga mutun cikakiya ai sun masu mutunci A hankali ta lumsheidannuwanta daga jin yadda juwa ke neman dimata da kasata sauke dubanta a kan Ameerah tana dane kanta da daukan hannunta ta kwada mata marin idan ya so a yi wace za yi dan kuwa darajar kanta ta sani ba zara kyale yar iskar nan ba "Ya salam, me yake faruwa harda mari? Yaya haka da saurin mari a fuska waje mai daraja, Son me yasa ta mareta?" Aleesa ta fadda da muryata a sanyaye aman kuma kalamanta na nuni a hankalinta a tashe yake Da sauri sir ya hade hannayensa biyu shima da yaren turancin ya ce" dan Allah ku yi hakuri sir, yarinya ce bata san abinda ake ciki ba aman zan mata fada sosai ita da kanta tana baka hakuri " Ameerahma ta dawo da sauri tana hade hannayenta tace" wani hakuri zata bada? Sir yarinyar nan bata da kunya, sam bata san girman manya ba, tunda muke bata formation ta kasa koda dafa tea mai kyau ne, bata iya tafia da dogon takalmi ba, bata iya kwaliya ba, ko kitso bata so a mata sai shirme da raina mutane bayan ko sisi bata biya a nan!" Sai da ta gama fada kafin kuma ta tuna cewa idan ruwa ne ta balo ta balo harda ita a ciki, domin kuwa vote aka yi da tawun bakinta Muneerath ke gidan, bandama wannan ba zata taba son wani abu ya samu aikin Sir ba, dan ita kanta tana zaune ne da taimakonsa domin kuwa da farko gaba suka sakota sosai Da ido yake bin kowa, irin yadda dakin taron ya rikice kowa ka kalla sai zarro ido yake sannan du sunna nunata irin ta dai daukowa kanta ruwan dafa kanta Bakinsa ya tabe ya kama hannun mamansa dake ta kokarin ta karasa wajen Muneerath yana karra yatsina fuskarsa a sanyaye ya ce " ina zaki je Mah? " Mamansa ta ce" kuka fa take kana gani ta mareta kan me? Dan ta yi daria? Dama haka aikinku yake da tsauri?" A hankali ya dawo da ita kusa da shi kafin ya juya da ita ya kaita wajen kujerar da aka janyo masa dan ya zauna ya janyota da kyau ya zanar da ita yana kallonta a ransa yana ayanna ta yaya zaka iya aiwatar da aikinka idan Mah na nan, ba zata taba bari ba A hankali yace" zauna bara na je na ji a kan me ta mareta " Kanta ta gyada tana kallonsa ya sauko daga wajen ya nufo inda suke Da hannunsa yamasu nuni kan su karra matsawa kusa da yan matan A lokacin da suke matsowa Muneerath sai a lokacin ta ji kafafuwanta sunna neman tona mata asiri ta hanyar yi mata tawaye, domin sau uku tana gwada daga kafarta dan ta arta a guje aman sai ta ji an riketa a wajen mugun rikon da ta kasa tsawatarwa kafafun nata har suka cin mata A dake sannan kasa da muryarsa sosai ya ce" du wata dake min kuka ta hadiye haukanta a wajen nan kar ta tadawa mamana hankali, sannan kowace ta matso sosai ku saurare ni!" Kasancewar da ainahin inglish ya yi maganar kwararen inglish tatace a cikinsu idan ka cire sir da Ameerah sai Muneerath sai ko Saudat da ta tsinci dan abinda ba rasa ba Yana hankalce da su da sauri Ameerah ta tatabo su da hannayenta ta daidaita su, sai dai Saudat da Muneerath da kansu suka matso din suka bada hankulansu A dakensa ya ce" ina son a bani bayani dala dala na abinda yake faruwa a gidan nan! Wani irin abu ne kuke kwabawa? Wace irin tarbiya ce kuke bawa dalibanku? Meye maganar ba sisi da kuma maganar komai baa iya ba? Ina so maganarku ta kasance kasa kasa ta yadda ba zai kai kunnan mahaifiyata ba! A dake ne ya yi magangannun nan, sannan a cicire ne ya yi su, haka kuma tsayuwarsa ya yi wace zata kare Aleesa da gannin komai, haka kuma yana yin maganar ne yana karra dunkule hannunsa dake nuni da da ace babu wani shigen dake hanna masa rawar gaban hantsi da koda bai iya ashar ba da an ji duka irin mai gigita bawan nan Sir ne ya dauki magana da sauri sauri da inda inda kafin ya karasheta yana mai sadda kansa cike da firgicin ranar da nan da Muneerath ta aikata aikin nan, zai iya cewa a yau ya yi nadamar kafafiyar zuciyarsa da ta nace kan sai an dauketa, shi din da kansa ya san ya gama yawo A kausashe ya ce" wani irin banzan zance ne kake fada min haka? Baka ga takardunta na shaidar ta yi karatun girki ba, baka ga na shaidar ta iya ruwa ba, a kasashenku da ake kawo maku hare hare, idan har da gasken turota aka yi ta ilata ku? A sanyaye ta budi bakinta ba tare da ta jira an bata damar magana ba, ita fa hasalima gani ta yi normal magana ce ake yi da kowa ta yadda kowa ke fahimta kuma tana iya karre kanta daga kokarin da ake a hadata da yar ta da ta fara magana da tsadadan turancinta wanda bata yi wasa wajen iya shi ba ta ce" walahil azim ni ba yar ta da bace, ban san menene kalmar nan ba, ban rayu da wannan a zuciyata ba, alfarmar Allah nake ci, ni ba yar kowa bace dan ko iyayena basu waiwayeni a nan ba, abinda na sani na rayu da burin zama HOTTESTE shi yasa na dage ma yi karatu da dukan karfina da nutsuwata, ban zo nan da na lalata komai ba sai dan na ga yaya gidan yake na fada a tarihin rahuwaa cewar na yi yaki da son zama hotteste na kuma fadawa Allah kan ya datar da ni na zama mafarkina ne bai cika ba ba laifina bane, ban kasance mai zubar da burina da sauki ba shi yasa kulun nake tare hanya dan na kalli dogari, ni ba mahauk..,,,,,,,,,," Da dan daga murya Ameerah dake jin kamar ta rike makogwaron Muneerath dan haushi ta ce" zaki mana shiru a man uban wa ya baki damar yin magana ko dan baki da tabiya?" Wani mugun kallo da ya watsawa ameerah sakamakon daga muryar da ta yi na uku kennan tun da ya zo wajen nan har tana neman hadasa masa ciwon kai ya sakata yin shiru tana rage muryarta sosai ta ce" ka yi hakuri sir, wannan yarinyar sam bata da yannayi da tarbiyar hottes, caractere dinta ba na irin aikinmu bane, wannan tana iya zubawa pasinger tea mai zafi a jikinsa ko ta tsoratar da shi " Muneerath kam yanzun ta shaka , ranta bace sannan kasa kasa sosai ta ce" akoy marar tarbiya irinki ? Shin kin tsane ni ne domin na kasance mai taka dokokin Allah ko kin tsane ni ne dan bakya son kalar fatata? Ke wai Allahn da ya yiki ya maki albishir din a haka zaki gama da duniya ko tunaninki ke zaki zauna a wajen nan har duniya ta nade? Kafin ki zo wata ke wajen haka kuma zaki bar wajen du nacinki wata ta hau dan babu abinda ke zama dindindin a duniya ita dukanta karya ce! Kuma idan takamarki ke wata ce ni nan zan auri dogari kwana kusa zan zama yar uwa sarki kwana kusa zaki dawo talakata zan zo nan na hanna ki wulakanta mutane! Ku rike Hotteste dinku haka Allah yahukunta min ba wani ba! Takai dubanta kan ameerah da gaba daya ta gama tsurewa da kuma yarda cewar muneerah fa mahaukaciya ce ta ce" ke kuwa da kika mareni Allah in dai tsautsayi ya hadani da ke a waje sai na nanaga keyarki a kasa, idan ba haka ba kuwa na barki da Allah wuta balbal! Wato Allah na yin bayin Allahn da sam basa tsoron budar bakinsu su fadin abinda ke cikin zuciyarsu ko a gaban waye, bale rayuwar Muneerath ta yita ne cikin ihu a makwontai, watau tana magana ne tun tana tsoron fadi har ya zamana fadi take tun karfinta kuma s take dole a saurareta Walahi bai taba gannin fitinaniya, fitsarariya, tsayayiyar yarinya irin wannan ba, a yau da ace Mah bata dakin taron nan da sai ya tsiyayewa yarinyar nan kaf man dake kanta! A yanayinsa na nutsuwa koda ransa a bace , sannan muryarsa cen kasa kasa dan kar ya masu ihun da gaba daya za shiga uku ga mamansa ya zaunar da ita a cen bayansa a tunaninsa bai san ta taso tuni tana bayansa tana saurare da kuma bin kowa da kallo ba a hankali yana kallonta yadda ta tsafe abinta ita ta san korarta za yi kennan ko wace wace ya ce"Hey" Ga mamakin kowa na wajen nan juyoea ta yi ta ce" tsaya in gama sai ka kore nin kai kuma!" Ta dora da fadin" Saudat ba abinda ta yi, kuma ita ta iya girki, ta iya ruwa, ta iya tafia saman dogon takalmi na tabata ko dan kar ranmahaifinta ya bace zata jure wulakancinku na adadin kwanakin da kuke son tafka mata, ku rufa asiri dan soyayarku da fiyayan halita kar hukuncina ya shafeta! A kore ni ni ita a barta ta yi abinta, ga dukkan alamu aikin Hottest din nan karuwanci ne dan gashi dan ban iya tafia da dogon takalmi ina karairaya ba za kore ni!" Baiwar iya yarensu da Allah ya bata ne ya sakata zagewa ta fadi komai da turanci kafin ta juya da niyar tafiarta tunda ta gama fada zuciyarta cike da tunanin me zai kaita gida? Abu daya dai da ta sani shine a yau idan ta je gida yayan gidan oga sai ta fasa kan kowani shege, dan ta tabata sai sun mata dariar da suka saba Muryarta kasa kasa ta ce" Kar ka barta ta tafi Da sauri ya juyo jin muryar mamansa gaf da