Sashe 25
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 1 Da sauri ta saka slifas dinta ta yi waje , da sauri sauri take tafia tana dube dube, sai dai bata ga kowa ba sannan bata jin maganar kowa Turus ta yi gannin wani gabjejen soja a gabanta , cikin daure fuska ya ce da ita ta biyo bayansa Sai da ta yi dan jim kafin ta bi bayan nasa cikin sanda dan tana tafe ne tana tunanin idan fa ya juyo ya jibga mata dukan mutuwa? To ita bata ga alamun daria ko fara'a a tare da shi ba ko dai wani ya zage shi? Sai da suka yi tafia mai nisa kafin su bayana a wajen da take hangen alamun ruwan sweeming pool Sai a lokacin ta fara jiyo magana kasa kasa ba sama sama ba, sannan ta fara hango ikon Allahn Gaba dayanta ta idasa bayana a wajen a lokacin da suke tsaitsaye Zuwanta ya zamanto suma sun juyi sunna kallonta cike da mamakin wacece wannan kuma? Gaba daya ta sare, gaba daya ta ringa jin wani abu makamancin sagewar gwuiwa da tsoro kasancewarta a gaban yan matan nan, yan matan tamkar wa'inda ke rayuwa a kasar kankara, mulmulmul fatocinsu suke kuma ba bak'ar fata a cikinsu dan ko mai duhunsu banasaria ce a kusa da tata fatar, irin shekin kuma da suke zai nuna maka koda a nan din ana basu gyara cen dama y'ayan hutu ne A hankali ta kai hannayenta wajen kirjinta ta rungume tana kifta ido tana kallonsu Atu ce ta yatsina fuska kasa kasa ta ce" Wannan fa mai sanye da irin kayanmu? " Kafada Humaira ta guada itama ta kuma juyowa tana karra kallon Muneerah Muneerath kuma kallon suturun jikinsu take, su dukansu sun saka kayan shiga ruwa ne irin yadda ake gwadowa a tv bakaken fatar ko nasaru na sanye da su, watau dai pant da bra, kowace tamkar cikinta zai hade da bayanta , kowace gashin kanta a fili da mai gashin da mai kurkur din kan ya sha gyara sai kyali yake yana karrawa Kasancewar basu sanma da ita a gidan ba, dan ko ranar da ta diro an mayar da su dakunnansu ne an rurufe su an basu damar yin kalo ko au shiga internet su yi dube dubensu ba'a fada masu dalili ba, su dai an gwada masu cod Red an zanna masu kurtun ba zasu fito ba, hakan ya sa a yanzun da suka ganta sai suka ga kamar daga sama dai? A sanninsu an rufe dauka ai Matsowa ta yi ko a yanzun dai sket din ne tsagage in ji Muneerath ta tsaya tana fuskantarta ta ce" Ki gabatar da kanki! " Muneerah ta hadiyi wani yawu mai nauyi a makogwaronta a sanyaye ta ce" ASALAMU ALAIKUM " su dukansu , baki daya taronsu ta kasa samun wace zata amsata, saima kallon kallo da suka shiga yi sannan su sauke dubayansu a kan AMEERAH wace take uwar gidansu Gabanta ne ke faduwa da tsoron yannayinsu dan bata saba mu'amala da abokai ko yan makaranta da irin shiga haka ba, sannan ta gama yanke humuncin ba musulmai bane baki dayansu duba da salama ta masu ba wace ta iya amsata saima wani kallo da ta kasa gane na mamakin gannin bak'ar fata ne suke ko na kaskanci? Murmushi Ameerah ke yi a kasan zuciyarta tana ayanna 'zaki fita ne da kafafunki, dan ko su basu ga irin fatarsu ba, in ba wulakanci irin na PPM (Shugaban kare yancin mutane) ba meye na wani dorawa da dafawa sir a dauke ki rana tsaka ko iliminki bamu tantance ba sai wani tuwon takashi dake rinjayarki ta yaya zaki iya kula da manyan mutane na jirgi? Wani kampani nema yana kallon yan matan nan namu sala sala zai dauke ki? Tun daga yanzu zan shaka maki azaba ta hanyar saka ki a cikin ruwan nan ke kadai!' "Amen wa alaiki salam" wata siriryar murya ta amsata tana tahowa daga gefe , ita dinma sanye take da pant din da bras din sai dai ita ta saka wani dan kwali ta daura a kugunta ba daga ita sai pant din bane, duda wajen daga su sai su aman ita din tana daure da shi ne Haka kawai Muneerath ta ji sanyi harda sauke yar ajiyar zuciya tana kallonta, ita dinma ita take kallo kafin itama ta kai dubanta wajen Ameerah su dukansu sunna jiran karrin bayani Ameerah ta gyara tsayuwarta ta gabatar masu da ita a matsayin daya wace zata kasance a cikinsu ta amshi horo tare da su, sannan sunnanta Muneerah ta yi rashin lafia ne ya sa bata zo a kan lokaci ba Da tsaftatacen faransanci ta masu bayanin , ba turanci ko daya a ciki hakan ya sa kowace ta gane bayaninta, da yawansu nan suka juya suka shiga harkarsu, su dai basu mata oyoyo ba, kuma basu nuna alamun ta gaje masu waje ba dan kuwa suma zuwa suka yi kuma ko dari aka karro basu da yancin hannawa Wasun kuwa kawai kallonta suke yannayinta bai masu kama da yar gayu ba, kwata kwata irin shirin nata bai dauke su ba duda suturar dai iri daya ce aman sakatama iyawa ne, ga kuma dauri da ta daure ta matse kai Hannun da yar budurwar nan ta miko mata tana murmushi ta ce" I'm Saudat Muhammad frm Arlit , nc to meet u Muneerath " Muneerath ta lumshe idannuwanta kafin ta saki sansanyan murmushi a hankali ta bata hannun itama muryarta cen ciki ta budi baki zata yi magana Ameerah ta ce" Gaishe gaishen ya isa hakanan, oya ki zo ki shiga na ga yadda kika iya ruwa kafin mu je bangaren girki " Sai da gabanta ya yanke ya fadi da ta ji maganar girki, aman kuma sai bata nuna komai ba, jikinta a mace ta kalli irin shigarsu cike da tunanin wai a haka zata shigan ne itama ko yaya? Bata dai tambaya ba sai ji da ta yi kafafuwanta na neman makata da kasa domin gaba dayansu dakatawa suka yi da abinda suke yi sunna kallonta, ciki kuwa harda wa'inda suke kai kawo da wani zungureren takalma a kafafuwansu sunna wani irin laudi sannan su dauki tafiyar gagawa duka da takalmin da ta yi imanin idan ta cira kafarta a samansa sai ta karya kugu kafin cinya a gangaro gwabri da tafin kafa, kai harta da wanda ke cikin ruwan sai ta kama karfe kawai ta hau hawa har na uku ta fito sosai itama tana kallonta Yawu ta hadiya, rana jin kamar ta je ta kama hannayenta ta ce da ita'ki rufan asiri mana na shiga daga ni sai ke?' Sai dai ta kula wannan mata ba mai rufa mata asiri bace Kasa kasa saudat ta ce" ko baki iya ruwa ba?" Juyowa Muneerath ta yi da sauri tana kallonta ta kasa magana A hankali Saudat ta ce" Kar ki ji tsoron kowa a nan, yadda kika zo haka kowace ta zo, idan kina baya baya ko kina boye iyawarki rainaki zasu yi, idan kuwa HOTTESTE suka ga damarki kin bani, dan zaki zamo tamkar yarinhar aikinsu, ki daga kafarki ki shiga ruwan nan idan har kin iya iyo, duda basa daukan wanda bashi da takardar shedar ya yi cour na natation ba, aman duda haka ki nuna masu in ba haka ba harta a wajen Ameerah zaki sha wahala" Shin ta yaya zata iya sakin jikinta da su, gaba daya jinta take bare a cikinsu tamkar ba halitu irinta ba haka take ganninsu, sun cika mata ido sannan du jinsu take tamkar ba yarenta ba A hankali ta nufi ruwan da kayan dake jikinta, wanda hakan ya kuma saka Ameerah sakin murmushi a boye dan ta tabata in dai ta iya ruwa ba zata shige shi a haka ba domin babu picsine din da aka basu damar koya ruwa da sutura haka a jikin mutun Sai da ta lumshe ido ta yi adu'a a kasan zuciyarta kafin ta cire slifas dinta tana kallon ruwan yadda yake kyali harma ana iya hango kasansa dan duka duka 3 mtr ne tsayinsa bayan ita ta koyi ruwa ne a wajen da bawa ba zai fadi zurfin ruwan ba sai wanda ya tara shi a wajen watau Allah Kai ita gaba dayama sai take tsoron kar a je idan ta shiga ta ji ta buga kai da kasan nan dan kuwa a kusa kusa yake gashi irin shigar da suka koya mata ba ta a taka matatakalar a shiga cikin nutsuwa bane, na a shiga da karfi ne ta yadda za'a dira harta da ruwan sai ya yi karra ba wai kai ba Kuma kallonsu ta yi ta ga kowace na kallonta da yannayi na son gannin me zata yi, a hankali ta juya wajen AMEERAH da ta tsareta da ido itama tana kallonta bata ce da ita komai ba Tana kallon Ameerar, ya kasance ruwan na bayanta, ta dago hannunta na hagu a hankali ta kai wajen hancinta a bayane cen kasan makoshinta ta furta" Tawakaltu AllaLah.... " Basu kawo haka a rayukansu ba, du jira suke ta dawo da sauri ta ce ba zata iya ba tsoro take ya mata zurfi , du jira suke ta fashe da kuka ta ce a taimaka mata kamar yadda da yawa suka yi sai a hankali suka iya shiga ruwan nan dan ya masu zurfi su ba da irinsa suka koyi ruwa ba a 2 mtr ko a 1,5 suka koya sai gashi a lokacin da su duka suke mata kallon bagidajiyar nan a ina zata ga ruwan da zata iya shiga har ta koya , ai iya ruwa a abin wasa bane ta fada cikin makeken ruwan nan ta baya baya bayan ta dan cira kafafunta ta tafi gaba dayanta wanda hakan da ta yi ruwa ya bada wani sauti Bacal.......mai karfin sauraro kafin wajen ya yi shiru domin a lokacin da ta fada ta nutse kasansa dan gannin yaya zurfinsa yake me da me ya dauka a kasansa, shin kamar ruwan tekun da suke shiga ne da kawayenta , shin akoy kifaye da halitu kala daban daban da cikin ruwa a nan ma? Shin ruwan na shiga ido ya hadasa kaikayin ido