Sashe 74
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 4 Sai da suka gama, suka gaji dan radin kansu sannan sukai mata salama bayan ta kara tunatar da su cewar idan sun shiga su tabatar bayan yin wanka sun daura alwallah, sannan kar hira ta shagaltar da su har su cika dare dan kar su kasa tashi sallar asuba a kan kari, sannan kar su manta da adu'a kafin su yi barci Har sun kama hanyar tafia Mah ta bukaci kan Muneerath ta bata wayarta zata yi wani abin da ita Ai kuwa da murnarta ta bata suka yi tafiyarsu ba tare da tunanin komai ba A wannan daren bayan Mah ta gama kula da mijinta wanda tafiyar gagawa ta taso masa du yadda ya so ya kaucewa tafiyar hakan bai yiwu ba aman sai ya nemi alfarma a wajen matarsa kan ta boyewa Hanja domin ya tabata idan ya sani zai fito kai tsaye ya hanna ne, Ita din da kanta ta samu kanta da yarje masa ba fan komai ba sai dan tana matukar jin dadin irin yadda yake dan haba haba da jikinsa da lokacinsa bayan a da ya zubar da komai maganar fatar bakinsa daya biyu zancen mutuwarsa ne, duda ta san haka din abu ne mai kyau dukan musulmi ya kasance ya rayu da sannin yana iya mika ran aro a kowani lokaci, a kowani lokaci sai dai kuma mugun zurfafa tunanin mutuwar na iya hadasa cuta, hakan kuma na iya kasancewa cutarwa ga bawa domin da ace hakan ba komai bane da Allah bai boyewa bawa ranar mutuwarsa ba sannan da bai saka hijabi a tsakanin mala'ikan mutuwa da dan halita ba Dan haka ta bashi dukan kulawa ta yi masa rakiya har wajen motar da zai bi boyayiyar hanya ba tare da media ta san da fitarsa ba sukai kyakyawar salama ta dawo cikin dakinta Kai kawo ta ringa yi a baban falonta da byro a hannunta tana dan wasa da shi ta hanyar juya shi a hannunta A hankali ta kai zaune saman bed ta mika hannu ta dauko wayarta cikin nutsuwa tare da ta Muneerath wace ta amsa Number ta dauka ta kwafa a wayarta ta danna kira tana mai kai dubanta wahen agogo wace ta nuna mata karfe kusan biyu ne na dare, sai dai ta tabata wanda ta kirayan zata same shi koda a karfe nawa ne, kuma bata tunanin zata iya rintsa idannuwanta idan har bata daidaita wannan abin ba Ba ita ta kwonta ba har sai da ta gama komai kafin ta dauro alwallah ta taho saman bed dinta tana mai adu'aa dukan motsinta ta haye saman gadon A hankali ta rintse idannuwanta sakamakon murdawar da cikinta ya fara yi mata Sannu a hankali ta ringa adu'a a irin tsugunin da ta yi a saman gadon tana rike da hannunta tana beman sauki a wajen ubangijinta wanda ta tabata shi kadai ke kawo mata agaji a irin wannan ciwo nata Ciwon ciki ne da take yi , wanda yake taso mata wani sa'in sai ta kusa shekara biyu bata yi shi ba Wani irin ciwon ciki ne dake gagabowa tun daga mararta ya yi sama gaba daya ya rikitata ya yi ta juya mata ciki tana birgima du hakurinta da girmanta kuwa, da jyar yake sakar mata amai kafin ta samu zuwa bayi ta zubar da datin dake taruwa wanda yake bata tsoro a dukan lokacin da ta samu yinsa domin shi ba gudawa bane sam, hasalima tauri ne da shi kuma ba tare ba, haka dai take fitar da shi mai mugun warin dake juya mata kai "Hasbunnalahu wani'imal wakim" shine abinda take maimaitawa tana kallon agogo gannin har hudu ce ta gota ta tabata a yanzu Son baya kusa ita kuwa du abinda zara tsinci kanta a yanzu ba zata iya kiran mijinta da ya fita dan hidimar kasarsa ta dawo da shi ba, haka kuma ba zata kirayi Iman kururuwar iblis ta tara mata jama'a ba Hakan ya sa a hankali ta ringa murkususunta tana ambatar sunnan Allah tana karra gyara daurin dan kwalin da ta dora a saman doguwar rigar barcinta fara mai dogayen hannu mai laushi domin sam bata wani lafe mata a jiki ba Wankin hula ne ya nemi kaita safe, tun Mah na gane yaren ciwonta har ta dawo ta fita a hayacinta, har lokacin salar asuba ya shige bata san inda kanta yake ba bayan ita din mace ce mai bi kofar du wani yaronta da ya kwana ya wuni a gidan ta tashe shi sallar asuba , dan kuwa ko anfani da waya bata yi ta fi gane ta je da kafafuwanta ............................................... Jiki mai rike abin sabo ya maimaita shi da karfin gwuiwa, sabawa da ta yi da tashin asubar ne ya sakata tashi a kan lokaci harma ta tashi Saudat suka daura alwallah suka gabatar da sallah bayan sun yi wanka domin tsaftar nan ta Muneerath ita kadai ce abinda bata taba barinta, tsafta akoyta ta jikanta da kuma mugalinta, du inda zata zauna koda na minute daya ne sai ta yarda da tsaftarsa Bayan sun gama sallar suka gaishe da junna Shiru Muneerath ta yi tana duban agogo kafin ta kalli Saudat dakr Hamma ta ce" To yanzun ai ya dace mu bashi amsa ko?" Saudat ta katse hammarta tana dan zarro ido kafin ta yi yar dariya tana talabe kumatunta ta ce" Anya kuwa sir mai sanyin haki zai iya da rigimarki?, Kin san menene idan har bai zama kazar kazar ba ina tsoron ki mayar da shi solofiyon namiji" . Muneerath ta yi yar dariyar itama tana cire hijab dinta a hankali ta shiga dan motsa wuyanta kafin ta kwonta ta ta shiga dan motsa kafafuwanta tana jim na sasafe da take dan yi dan ci gaban rike lafafen ciki kamar yadda aka koya mata ta yi murmushi a karro na biyu ta ce" kin san menene?, Attahir na nunin shima wani zaki ne, harma ya ce zai iya saka rigar dogari dan na so shi...................wannan wasan da ya buga ya saka ni a tunaninsa........................aman;;;;;;;;;;;;;;' ta dan yi shiru tana kikifta ido alamun wani tunani ne ya shigo kwakwaluwarta hakan ya sa saudat tabo hannunta tana fadin" Aman me?" Muneerath ta yi murmushi ta juyo tana kallonta ta ce" Ni fa bana tunanin idan har namiji laso laso zai iya rayuwa da ni lafia, kin ga meye anfanin namiji idan zai maka magana sai ya sanyayar da murya? Ni fa gani nake to wane ka bara min kennan? Kin ga aka ce mace ita ce yar kwalisa, yar sanyin murya, yar lalashi, yar yar yar yar..........., Ki duba ki ga Attahir idan zai yi magana fa fari yake, na taba tambayarsa ko ciwon idannuwa yake ko kuma haka aka haife shi ne? Sa ce min ya yi aa wai akoy abinda ke saka shi cikin shauki irin haka, shi kuma haka Allah ya halice shi bawan Allah" Wata irin daria ce ta kubcewa Saudat har tana rike ciki a saman salayar tana kwonciya, ya subahannalah wai shin wace iri ce Muneerath ? Yanzun yana mata irin kashe idon nan dan ya saka ta afka a soyayarsa wai ta masa tambayar ciwon ido yake? Bata karasa wannan ba Muneerath ta girgiza kai tana zama ta mayar da gwuiwar hannayenta baya ta gyara kwinciyarta ta daga kafafuwanta kadan ta tsayar da su tana ta sauke ajiyar zuciyar wahaka dan wannan yana bata wahala duba da mazaunan nata idan ta yi haka wani bajewa suke abinsu ta yi murmushi ta ce" Allah ya daina baki daria wannan abin, to sai na ga ni me namijin ya bara min dan Allah?, Haba ai ya dace nakiji kawai ya kasance mai kaza kaza,mai balaki da tashin hankali, dan rikici na mamaki, wanda idan na masa zai daga ni sama ya nunawa shirwa ni ya nana da kasa............a haka zan fi jin tsoronsa, ke ogama cewa ya yi wai akoy kura wai kawai in ya kula ni din wannan an so a yi tabi tabi sai dai aka gyara min aka zari hamsin a dari, wai a haka zai barni ko dan idan ya min aure ya ci daria, dan ya san wai ko a yadda idan namiji ya ce irin wai ina da ko manyan kaya ko me? Nake fada masa in ce masa ya daina dinka min manyan kaya, ke ni dai da abin ya ishe ni sai na koma siyan gwonjo da kudina na kari, yo shi kamar wada ya tsane ni a cikin y'ayansa kulun kulun sai ya sa a min baban dinki, mai dinkin nema munafuki sauran ai dinkin motsa da karfi ka yage yake masu sai ni yake yiwa buhu dan kawai an tsane ni" "Innalilahi" shine abinda Saudat ta fada tana karra wara dubanta a kan Muneerath, walahi ita bata taba gannin mutun mai faranci irin Muneerath ba, yanzun babanta take cewa an ce tana da manyan kaya? Haba haba dole ya ce an zari hamsin, kuma tsakaninta da Allah ne take maganarta , Sai kuma tausayin Muneerath din ya tsargun mata a zuciyarta, shin menene musababin wannan hali da take ciki? Munnerath bata taba zama ta bude mata sirrin cikin gidansu ba, idan ta kamata wani sa'in tana hawaye ko ta zurma a tunani idan ta tambayeta ba'asi tun tana ce mata ba komai har wani lokacin ta fashe da kuka ta dora kanta gefen kafadarta tana fadin Saudat, kin ga fa iyaye ne da ni, da ransu da lafiyarsu, idan na ga asabar ko lahadi ta gabato na ga iyayenku na kawo maku ziyara, wa'inda suke nesa da kasa sai na ji zuciyata ta tsinke, shin wai anya baki daya y'ayan gidanmu su suka haife mu?, Sam basu damu da mu ba, mahaifiyata na raye ina nan bata neme ni ba, shin me yasa ba shakuwa ba soyaya sai kiyaya nake karanta a tare da su?, Idan kina so ki ga ana sonki a gidanmu tabo fada a waje yanzu zasu ringa yiwa kansu kirarin su an gwada masu rashin mutunci? To wannan fa an tabo waje watau zasu nuna maka su din sun iya masifa mai sunna masifa wace bata da hadi, abin bakin cikin ba dan