← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 114

Sashe 55

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 3 Wani irin luuuuuuuu ya yi da idannuwansa a tsayen da yake da sauri ya kara dora dubansa a kanta Kan iyayensa ya juyo da fuskarsa domin zuwa lokacin ya kula da sun sauko Irin yadda fuskarsa ta fara zama ja ransa ya nuna bacin rai karara kafin ya juya da waji irin sauri ya fice a falon ya saka mahaifinsa kallon Mah Murmushi ta sakar masa a sanyaye ta ce" Mu je mu dawo" Sai a sannan Muneerath ta ankara da su Ajiye nata plat din ta yi itama ta nufo su tana dan murmushi a nutse ta ce" Pah barka da warhaka, Mah kun sauko ne?" Mah dake kallonta tana sauraron Pah na amsa mata lokaci daya wani tunani ya ringa darsun mata a zuciyarta Murmushi ta yi a hankali ta shafi gefen fuskar Muneerath ta ce" Muna dawowa ku shiga kicin ku yi girki " Tana gama fada ta bi bayan Pah da yayi gaba tuni Tafia ce suka yi tamkar kurame, tafia ce ta sirri domin mota hudu kawai ta masu rakiya sai tasu ta tsakiya ta biyar Gari bai san da fitowarsu ba,hanyar kasa aka tsare su kadai suka bi har suka sada kansu da makeken asibitin inda likitan ya tarbe su ya gama aune aunensa Kwarai shima ya yi mamakin fitowar gashin, ya saka shi a injin yin scan ya gama daukan komai zai samu manyan likitoci a yau su duba result din a tare dan gannin me ya faru me yake shirin faruwa da shi Ya tabatar masu cewa bai taba gannin cas din da aka kai wannan matakin gashi ya fito ba,sannan bai taba gannin wanda ya kai wannan matsayin ya samu lafia ba, dan haka yana tsaka tsaki amsar da zai basu ma kan takardun dake hannunsa zai dawo da kansa da dare A haka suka fito a cikinsu Mah ce kawai bata wani karaya ba da maganar bayahuden, abinda ta sakama ranta harma take kara rikewa da karfinta shine Allah ya yi magana, sai da ya saukar da maganin cuta ko wata iri ce, ta tabata idan zai tashi zai tashi, kuma wannan alamu da suka gani ta tabata ba na banza bane dan haka baa cinkushe zuciyarta ba Mahaifin Hanja kuwa tarin tausayinta,da na yaronsa, da na al'umar kasarsa ke cinkushe a kasan zuciyarsa A lokacin da suka fito da ido yake bin du wa'inda aka tsare yana kallo , yakan nema masu sauki har kasan zuciyarsa kafin su shige su kamo hanya Hanja kam kansa a jikin madubi ya lumshe rinanun idannuwansa Gaba daya wani lokacin sai ya ji zuciyarsa banda kunna babu abinda take yi Kamar irin wannan lokacin na yanzu, ya rasa a wani mataki zai ajiye halin da yake ciki da tunaninsa da zuciyarsa baki daya, hakan sai ya hadasa masa tashin hankali mai tsananin gaske Idan ya kalli mahaifinsa sai ya ji dama yana iya gannin ciwon nan?, Idan ya kalli fuskar mamansa sai ya ji shi din ba kowa bane ba kuma komai bane tunda har gashi a tsaye a gabansu sunna cikin hali na rashinu walwalar zuciya aman ya kasa kawo masu mafita sai dai ya kale su Abinda ya fi sakawa a ransa shine zai ci gaba da kamanta faranta masu har karshen numfashin shi yana mai musu addu ar dawwama cikin farin ciki tare da kwanciyar hankali mai daurewa har suka iso gida hanja bai sani ba tsabar ya tafi duniyar tunani sai jiyayi mah na taba shi firgigit ya dago tare da fita a cikin motar ya shiga bin bayan su mah da tuni sun isa cikin kayataccen parlon su ciki ya shiga kamar marar laka a jikinsa ya samu daya daga cikin kujerun dake zagaye da parlon zaunawa yayi batare da ya ce musu komai ba Mah ce ta taso daga inda take ta iso gareshi da sauri ta zauna kusa dashi Dafa kafadun shi tayi cike da damauwar yannayinsa tace" son lafia kake kuwa gaba daya yau bana ganin ka daidai daga zuwan mu hospital har zuwa dawowar mu , shin mai yake faruwa dakai ne son pls tell me " ta karashe tana shafa gefen wuyansa Daidai lokacin aka gama gabatar masu da drinks dan su sha dan huce kishirwar hanya zabura yayi kamar wanda aka tsikara ya mike tsaye magana yake cikin fada yana cewa " Mah ba zai yuwu ba wllh, wannan yarinyar terrorist ce ni nasan kashemin ku take son yi !" Da sauri ya dora hannunsa a gefen kirjin shi da ya mishi mugun nauyi yace" Washhhhhhhhhhhhhhhhh" dadai lokacin da ya hada ido da muneerath suna karasuwa ita da iman dan yiwa su mah barka da dawowa basu lura da yanayin da hanja ke ciki ba sannu da dawowa sukawa su mah suka shige abinsu karasawa yayi gaban pah ya hade hannayen shi duka biyu yana rokon pah akan su masa rai su ni san tata da shi wllh shi bai taba ganin fitsararriyar dake kallon sa ido cikin ido tai masa fitsara irin yarinyar nan ba, Muryarsa a raunane ya ci gaba da fadin" pah baku ba har dani yarinyar nan take son halakawa sabida jiki na yana bani a duk lokacin da muka hada ido da ita inba terrorist bace ba zan ringa jiin hakan ba pah tabbasa akwai wata kulleliya da take shiryawa akanmu dan ra tsaka ta kona mu!" Ya kuma kallon Mah da ta tsare shi da ido tana karantasa cike da mamakin yannayinsa a hankali ya ce" Pah idan ka hada ido da ita baka ji gabanka ya fadi?" A sanyaye pah ya girgiza kansa shima cike da mamaki n wai me yarinyar ta tsare masa har haka? Hanja da ba abinda ya dame shi da lamarin wani shine du ya fitini kansa a kan yarinyar da bata tsare shi da komai ba? Idonsa cikin idon Pah ya ce" Ko daya baka jin haushinta a ranka?" Pah ya rike hannunsa yana kallonsa ya ce" Son me yake damunka ne? Me ta yi maka ne? Idan wani abin ne yake faruwa ka gabatar min da shi sai na nisantata da kai da mu baki daya, aman idan baka da huja ka barmu mu idasa ladanmu mana" Kalon mahaifinnasa yake a kasan zuciyarsa yana tunanin wace huja suke so da ta fi wada yake fada madu a yanzu? Wace suke so ne? tashi yayi cikin fushi ya bar parlon tamkar zai tashi sama inda Mah ta raka shi da kallo tana murmushi tana girgiza kai a hankali, Pah kuwa ya raka shi da kallon tashin hankalin yannayinsa mah ce ta karaso kusa da pah hannun shi ta kama ta zauna a kusa da shi sosai a hankali tana shafa gefen fuskarsa tace " mai ka fahimta gami da son ?" tagumi pah ya rafka yace" nikam da za abarni sai ince na fahimci wani abu" da sauri tace "kamar me?" Pah ya dan watsa hannayensa ya ce" Ba zan ce ga takamaimai ba, ban san me ta tsare masa ba, ba itace mutun ta farko da muka dauka ba, ba itace kalar bak'ar fata ta farko da muka dauka a cikin duniya ba, sai dai ita kadai ce ta africa, sannan kwarai haka ne ita kadai ce mai kallonsa cikin ido harma ta juya kai tsaye ta ci gaba da magana bayan yana wajen a tsaye tamkar kowani mutun ba abinda ya dameta, tabas itace ta farkon da na ga ta aikata haka ya yi diri diri ya wuce bai dora hukunci a kanta kai tsaye ba, na yi mamakin da yake nan shawarar barinta zai yi ko korata zai yi.....hakan sai ya sakani tunanin a cikin rudani yake cikin biyu watau barinta ko koratan, kin ga ya dora mata sunna wai terorist......ko wa ta tada a gabansa?, Kin ga Prince yana fada akan mace? Sai na ji ina son zama na ringa kallonsu, sai na ji ina so mu yi cij abinci a tatare da su a table daya a lokaci daya ina kallon su, sai na ji haka kawai ina son na zauna a daidai lokacin da zasu yi fada.....haka kawai nake jin koma meye na yarinyar nan alkhairi ce ga rayuwar son, tabbas na gano tanada matukar tasiri a cikin rayuwar sa ta halin fada ko jituwa......" murmushi mah tayi tace" isha Allahu lokaci zai nuna mana Allah yasa hasashen dana ke ya tabbata akan son da muneerath" fuskanta ya shafa ya kashe mata ido daya ya ce" ameen ya Allah kalb" Sunkuyar da kanta tayi tanajin kunyar pah saboda abubuwan yanzu da yake mata na soyayya tunda shekaran jiya zuwa yau kuma ba wasa yanzu ita har mamaki take yadda jarumtar shi ta dawo kamar ba shi ba, ba zara taba manta yau din nan ba, bata tunanin zata kuma samun ranar sai gashi ta sameta ido bude, ita kam me zata ce da wanda ya haliceta bayan ta kara ninka ibadunta? .....a kasan zuciyarta ta furta'Alhamdulilah' kama hannun shi tayi tace" muje kayi wanka ka huta lokacin shan maganin ka ma yayi" a tare suka mike pah yana dan bata rai sabida takura shi da take na shan maganin nan .............................. ....... Su muneerath kuwa suna komawa daki ita da iman wace ta biyota dakinta , haka kawai tunanin yadda aka yi ya bata wayarsa take hakan ya sa ta mugun sake da ita dan so take ta fada mata wai ta yaya hakan ta faru? toilet ta fada dan yin wanka saboda wainar kwan nan da ta soya wai ita a ganninta tayi wani babban aiki ne Iman ko guri ta samu a bakin gado ta zauna tunani ta fara na yadda zata bulluwa muneerath tabbas jikin ta zata shiga sabida a dan zamansu ta gane muneerath din ba wani wayo ne da ita ba sabida haka ta samu makamar da zata na cusa mata kiyayyar ko wane irin namiji kawai ta tsaya ga dogarin ta ya fi mata domin itafa ta hasasu kamar ta fara samun matsayi a gurin hanja so ya kamata tayi wani abu akai duda bata tunanin wai Hanja zai iya kula wannan yarinyar,aman fadan sun nan ya tsaye mata a rai Muneerath ce ta fito daga
Chapter 55 · 0% Book details