← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 114

Sashe 32

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

su, idannuwansa ya zarro ya kuma damkar hannunta zai maida ita wajen zaman ta tirje tana kallonsa ta cenza harshenta zuwa larabci ta shiga magana a sanyaye tana watsa hannayenta ta ce" Allah fa ta ce ya tsaya mata, cewa fa ta yi Allah take fadawa ya cika mata burinta, haka fa ta ce bata wasa da buri akan karatunta, zuwa fa ta yi dan ta ga makarantar ta tsinci kanta a ciki, shin wannan bai zama babar hujar da ta isa a rike dan a kamawa yarinyar nan ta kai ga cinma burinta na son kasancewa Hotteste ko kana cikin manyan da suke da damar talafawa talakawa aman kuma suke take su sunna karra murje su dan basa son su ga sun ci gaba? A hankali ya kamo hannunta dan so yake ya zaunar da ita ko zai gabatar da aikinsa sai dai ta ki basi dama, a hankali ta fara yar gargadar murya irin hawaye fa zata masa a nan gashi yarinyar nan mahaukaciya sai ihun a bude mata ta fita take masu a sanyaye ta ce" kai ne fa uban talakawa, sarki mai taisayin talaka ne koda ba a kasarsa ba, kai ne fa Allah zai tambaya yaya ka tafiar da naka ikon? Kaine fa ya dace ka talafawa du wani wanda ya kasa ," A sanyaye ya ce" Mah, kar ki yi kuka mana a kan wannan, kin ga aikinmu yana da tsaurin gaske, sun taka doka ta hanyar daukan yarinyar nan bayan bata da cikakun takardun da aka saka dokar sai da su, ni ba dan tana daukan horo kyauta ba, ko daya, sai dan bata bi tahanyar da ya dace ace tana nan ba, mama bata yi makarantar hoton girki ba, bata yi ta horon ruwa ba, bata yi ta horon tafia ba, ta ina zan iya kyale haka?" Aleesa ta da n fara daga muryarta dan ita fa so take tun yanzu ta fara tankwasa shi ta faa ganewa idannuwanta ya yi act irin na saraki a kasar da ba tasa ba dan haka ta dage kai da fata ta ce" kai zaka tsaya mata, kai zaka cike mata takarduntata hanyar sakata ta koyi girkin a makarantar daya dace" Gashin kansa ya dan yamutsa yana dan dama bai fito da su ba ya ce" Mah ta yaya? A yanzu idan na saka kaina a wannan rigimar ina cikin matsala nima dan kuwa cewa zasu yi na take dokar da na dora, Mah ki fahimta zan bata makudan kudaden da zara tafi ta yi abinda take so da su, aman idan kika ce a yi haka ban san ta ina zan fara ba" Mah ta juya tana kallon Muneerath da ta juyo ta nufi wajen su Ameerah da sukai tsuru tsuru ita da sir Murmushi ta yi ta ce" Bana tunanin idan kudinka zai saka ta ajiye burin aikin nan, aman me zai hanna mu yi wani abu? Ban ki ka katanta mata maganar kudin ba, idan har ta zabi ka bata kudin a kan aikin nan bani da ja, bt idan har ta zabi aikin a kan kudin zaka yi du yadda zaka yi dan ka kama mata, ciki kuwa koda a nan ba zai yiwu ba mu tafi da ita" Fuskarta ya kurawa ido, a duniya wannan mata tana da karfin iko da shi, tana dora abinda take so koda baya so kuma ya ji ya gani dan kuwa babarsa ce yana son abinsa baya tunanin akoy abinda zai sa ya mata rashin biyaya, Matsawa ya yi kusa da ita sosai ya rage tsayinsa a hankali yakai lebensa kan goshinta ya mana mata kiss kafin ya ciro fari kal din papier a hankali ya shiga goge mata yan kananun hawayenta da ta fitar da rigima kafin ya jimke hannunta ya maida dubansa kansu sunna faatawa dayaren hausa shi kuwa baya jin yarensu abinda dai ya fahimta sojojin dake tsare da kofar take nunawa tana magana tana hade hannayenta Lebensa na kasa ya cije cike da tsaa yadda zasu kwashe da su baki dayansu, dan kuwa shi ya tabata ko a kasarsa kasar arziki da wuya ya nunawa yarinya irin kudin nan ta wani zabi wai aiki bale a nan!, abinda dai zai so shine kafin ya salameta da kudinta sai ya koya mata hankali! Uwa uba masu gidan nata da suka dauketa a kan tsarin da ba shi ba, su da kansu a yau zai mayar da su terrain! Zasu koma bakin aikin cikin jirgi daga Ameerahn har sir din, dama shi mai kula da tafiar da aiyukan Hottest ne a cikin tafiar jirgi ci gaba ne ya samu aka bashi wajen nan na horo, ita kuwa Ameerah tsohuwar hoteesss ce da tayi yawon kampaninika daga karshe itama ta samu mukamin nan ta sauko kasa, horon da zai masu a yau shine ya mayar da su saman su koma su kara daukan lesson kafin su sauko su ba wasu lesson din A hankali yake nufarsu Aleesa na biye da shi itama a hankalin , a kasan zuciyarta kuwa adu take yi kan Allah ya sa kar yarinyar nan ta bata kunya, ita so take ta ga yaronta na taimako, so take yaronta ya kasance daya daga cikin manyan mutanenmu masu talafawa yaa sunna taimaka masu wajen gannin sun tashi suma sun zama wasu gobe, ya kasance mai tausayin talaka mai talafawa matasa masu zuciyar yi Yana karasowa du suka yi cirko cirko sunna kallonsa, sai a yanzu muneerath ta bi hannunsa daa dake dunkule da kallo Allah bata shirya ba ta hadiyi wani dunkulalan yawu kafin a hankali ta labe a bayan sir dan kuwa wani tunani ya zo mata yanzun idan ya kima mata hannun nan nasa ai ya kasheta ya kare, gwara ta labe a bayan freind duda ta ga sai fada yake mata kan kar ta kuma yin magana idan wannan na waje wai shima mai gidansa ne, in ba sir ba ai shi yake mai gidansa ita ai bata sanshi ba dan haka ba mai gidanta bane sir shine mai gidanta, baban bakin cikinta ta fita ta ga babu dogarai, kai yau da sai ta tada hankalin kowa a wajen nan walahi! A dake ya budi bakinsa bayan ya ba kansa hakuri da lalashin zuciyarsa sannan ya jure irin magangannun da yake ta yi a yau a yanzun nan ya ce" 11/14/21, 12:47 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*
Chapter 32 · 0% Book details