← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 114

Sashe 67

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

take kara wara dubanta a kansa yana zaune yana opprat din laptop a saman kujerar da bata san a ina ya daukota ba Kayan dake jikinsa a yau farare ne kar kar masu shegen kyau irin na Pilot Sun karra haska fatarsa sun masa wani irin kyan da ya birgeta har ta samu kanta da sakin murmushi tana kallonsa tare da dafe kuncinta a bayane ta ce" Kai kamar mutanen da ake nunowa a TV wollah, kai kam ka ringa shan maganin baki kar a cinyeka" Sai kuma ta kai dubanta da sauri wajen kofar da sauri ta zabura ta mike tsaye tare da nufar bayi da dan gudu gudu ta shige ta rufe bayin Hakan ya saka shi bin bayanta da kallo kafin ya dan girgiza kai Yana ta aikin nan ta fito ta dauki kayanta dake cikin jakarta dan tana farkawa ta fara gannin jakar ta kuma komawa da wayarta tana karanta cewar nan da minti talatin zasu tashi ta kuma duba lokaci ta ga har tara ta wuce da sauri sauri ta saka suturarta sannan ta ciro hijab dinta na sallah ta tayar da sallar bayan ta gama gungunnin yana kallonta ana kiran sallah bai tasheta ba Sai da ta gama sallar sannan ta kuma daukan wayarta, nan ta ringa gannin message din Mah tana ta afkin tambayoyin nata kafin ta fada mata yau Birthday dinsa ne sun shirya masa dan karya karya surprise kar ta sanar masa Dan bakinta ta tabe a kasan zuciyarta tana ayana'Ku yi shagalinku kudi ke maku kaikayi' Tana nan zaune ya mike yana rufe Laptop din ya dauke shi a hannunsa dama ba jona shi ya yi ba ya dan kaleta ya sakar mata harara gannin kale kalenta take hankali kwonce ko yar gaisuwar nan bata yi masa ba ya cira kansa ya shiga tafia Da sauri ta mike gannin a shirye yake, sannan ta ga an saka lokacin tafiyarsu tana biye da shi tana hararar keyarsa idan ta daga kanta a ranta tana ayana' Bakin hali ba zaka min magana ba bayan ba gaba ba muke, sai me karma ka min wollah nima ai ba yi makan zan ba malan mu dai je garin namu a maida ni kasata ya isa hakanan a zamana da kai ba abinda baka nuna min ba, bindiga ce, shaka ce, hankada ce, ka kunto min zaki, ka ajiye min zaki duka kaf dan ka halakani Allah ne ya tsaya min kuma na san zai kare ni' Sun yi tafia cikin nutsuwa da kwonciyar hankali kamar yadda suka zo Pilot din su biyu ne , dayanma fararan kaya ne jikinsa , kuma bakin fata ne mai fara'a, yana tafe ne da nufin ya karra gogewa a harkar tafia, sai kawayenta da Sir wanda tuna suka dawo ido kawai yake binta da shi, yana jiran su kadaice ya isar mata da sakon zuciyarsa, shi kam wannan lamari na bashi tsoro da ba dan ya ga abinda aka rubuta a shafin masarautar cewa ba matarsa bace ba budurwarsa bace bama kawarsa bace yarinya ce da mamansa ta dauko Hostess ce bayan wannan ba komai a tsakaninsu ya dan samu nutsuwa ba da shima gaba daya hankakinsa ya tashi da lamarin A baban dakin da suke haduwa ya yi maganarsa ta karshe kan kowa ya rike wayarsa a hannunsa suka shiga gaba dayansu inda Muneerath ta kebe baki ta dan karkace gannin da duhu a dakin duda basu saba gannin haka ba ta hade fuska tana rike da hannun Saudat ta ce" Bara ki ga yadda zai yi daga ya shigo" Ta dan yi gaba ta dawo ta ce" fuska kamar kunnun safe zai kalle mu ya ce" Kun dawo daga aiki,aiki kuka rafi yi, kun yi kun sauka hakan baya nufin ba zaku samu kira a kowani lokaci ba, idan kira ya same ku ku amsa ko ku samu takardar kora". Ta karashe tana kebe bakinta ta ce" kamar wani aikin shiga aljannah" Saudat dake daria kasa kasa zata yi magana tare da mamakin duhun wajen ta yi gagawar ja ta tsaya gannin gaba daya wajen ya dauki wani irin haske da walwali yana walwalwalwalwal Da sauri suka karta wara dubansu sunna kallon lokacin da HANJA ya shigo tare da wasu ma'aikatan gidan lokaci daya dakin ya dauki dan sanyayan kida irin nasu na taken sarakan garinsu mai hade da wakar Happy birthday, sai kuma yan matan da suka shiga rawa su shida rawar iri daya ne da alamu cholegrafi suka shirya suka hardace abinsu Yan matan masu kyan gaske farare kal kal kal sunna takunsu cikin tsari sunna juyi hakan ya sa sauran suka kama tafi duka ana dan taya rawar ana taya wakar ta hapoy birthday din w HANJA wanda ya ja ya tsaya tunda ya shigo yana kalonsu baki daya fuskarsa bata bayana me yake ji game da da abinda ake yi ba, aman ga dukan alamu ya ji dadin hakan domin da bai birge shi ba da ya yi tafiyarsa A hankaki Muneerath ta fara gyada kai, dan lokaci daya ta ringa jin wakar na shigarta sai kuma ta ga rawar da suke sam ba haka ya dace su yita ba, rawar da ya dace su kada su juya su rakarkashe su kai dan idi idi su kara a gaban makadi sai wani jimke hannu suke maimakun su bada kala su saki jiki su tafki rawa ba A hankali ta janye hannunta daga cikin na saudat dake murmushi Ita kanta bata san abin ya debeta har ya karasa da ita tsaka tsakan rawar ba sai da ta yi kamar juyi hudu ta kula da ana tafa mata kamar yadda du wace ta yi abin bajinta ake tafa mata ana shan dariya da morewa ba sai da idannuwanta suka sauka a kan fuskarsa ne gabanta ya fadi lokaci daya kuma ta nemi tsayar da kanta rawar ta kasa a lokacin ne aka shiga turo katon cake din da aka yi masa mai yannayi da jirgi masu rawar na tikar rawarsu masu tafa gannin cake din na tafawa har aka kusan turowa gabansa inda yake tsaye kikam tamkar idan ya budi baki aman wuta zai yi na bacin rai da kuma jin haushin shirmen yarinyar nan da ya gama yiwa jawabin ta kama mutuncin Mah dinsa itace ta cire da rawa a cikin mutanen nan A hankali ya daga kafarsa zai karasa inda take, daidai wani lalausan hannu ya shiga cikin nasa , hannun mai dauke da sanyi da kuma laushi sai kamshin turaran da ya dakeshi hakan ya saka ya juyo da dan sauri dan gannin ko waye lokaci daya idannuwansa suka sauka a kanta, A hankali ya lumshe idannuwansa ya kuma budewa ya kai dubansa kan hannun kafin ya dagoda wani yannayin na ya shaka ya budi bakinsa ya ce" 11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*
Chapter 67 · 0% Book details