← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 114

Sashe 41

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

zata dan adam yana da yanci shakar da ya yiwa yarinyar nan ban zata idan na shiga zan ganta a tsaye ba, tunda suka tafi kuma na kasa zaune na kasa tsaye, shin idan fa ya kasheta?". Madame joyceline ta fada bayan ta gama sauraron bayanan jujun dake kare yancin yara da matasan kampanin nasu Gaba daya ta kasa samun nutsuwa, ta sani sarai wannan abin da ta yi yana iya jaza mata baban balakin da ba zata iya kokowa da shi ba, aman ta jajirce ta dauki risk ba dan komai ba sai dan ta kuma san kasa suke ta yancin kai, yarinyar nan kuwa ko a musulmai ta shiga ranta sosai dan yarinya ce mai dadin zama, gudun nan da suke yi tare sosai ta ahiga ranta, a kasar nan kuwako uba ka kula yana takurawa dansa kana iya shunawa iko su kama shi ram a tuhume shi, idanma gaskiya ne kana iya yin kaso, ko tara mai yawa sanann a amshe rikon dan daga hannunka Murmushi ya mata bayan ya dan shafa kansa ya ce" meye hujarki na ita din yar kasa ce? Sannan menene hujarki na ba ainda ta yi masa?" Dan kikifta ido ta shiga kafin ta ce" ta nuna yannayi na innocent" Kansa ya girgiza ya ajiye byronsa ya ce" Aman yaya aka yi aka baki mukamin nan? Har yanzu baki daina anfani da yannayin mutun ba ba tare da kin yi bincike ba?, Madame da gaske kike saboda yannayinta kika dauki wannan baban risk din MR HANJA ba aiki yake da iko ba shine iko, kina magana da a je a tuhumi sarkin garinki na nan da dan watani kan abinda baki da tabas dinsa? Kin san da dole za'a ambaci sunnanki a gabansa? Kin san da idan lalube kike ba gaskiya bane ni da kaina da kika saka kin saka ni a matsala? Kin fi kowa sannin Me Hanja baya daya daga cikin wa'inda muke neman laifinsa ido rufe domin shi din shi ya fitar da hukunce hukuncen bima mai haki hakinsa , shin zai yi gangancin takewa kuwa? Na san dan adam kowa nada abinda yake boyewa, aman idan har wannan da zamu yi ba shine abinda yake boyewar ba kin san da mu zamu zama boyayu domin lauyansa sai ya yi yadda ba za'a kuma tunawa da mun rayu a duniya ba domin ina mai tabatar maki lauyansa Mockar sai ya goge harta da labarinmu dake cikin yanar gizo dan wasa muka yi da ZAKI!?" Ya karashe yana kallon yadda du ta rikice kafin ya ce" idan kuwa haka ne mun ciri tuta, zamu yi aunna sannan mu yi kudi, zamu samu mulki domin zamu kasance da masu mulkin, idan har kin yarda da maganarki ba damuwa sai mu fara shigar da kara da camerar abinda kuka dauka a lokacin " Sai a lokacin wara zufa ta fara tsatsafo mata, a hankali ta zauna cike da tsoro tana tuna kashedin da ya masu na su guji fitar da maganar hannunsa ya taba mace dan gargadi domin yana jin kunyar a ji mace ce ya taba da hannunsa ba namiji ba, Lokaci daya kuma ta tuna da baban sojan dake bashi kariya ya cire gaba daya vidion abinda camerar ta dauka Wani yawu ta hadiye da ta tuna Muneerath ta sanar mata cewa tun daga kasarsu ya daukota, a hankali ta shiga girgiza kanta kafin ta mike da sauri ta bar office din cike da dana sannin zuwa da wannan maganar da fatan kar ta je ko kunnen karen gidansu ne! ______________________________ "She look so so so ya rab she look tn a prncss khalb" ta fada a sanyaye a lokacin da ta kai masa kofin maganinsa ta surba masa a bakin nasa Murmushi sarki ya yi yana kallon HANJA da yake rike da kofi na kwalba wanda aka zuba wani dan tsurut din jus , hannunsa daya kuma rike da remot ya rage kukan TV din sosai ya maida kallonsa kan Mah ya ce" Yanzun y'ayanki mata biyu, to ita iyayenta suka baki ko cirowa kika yi?" Murmushi ta yi ta bude rubutun da take shafa masa a kansa mai hade da su ruwan zamzam da su jibda ta diba kadan ta ahiga shafa masa ta ce" Allah ne ya bani,kuma ka ga ka tambaye shi hala shuna mata Zakin nan nasa ya yi?" Yarinyar dake wajenta ce ta fito mai sunna Iman, sanye take da doguwar riga irin na dubai din nan, sai dai ba yane mayafin ta yi ba a kafadarta yake ta masa irin yadda indiyawa ke yiwa mayafi, ta tufke gashin kanta a bayanta ya mata lufluf abinka da jinnin larabawa Yarinyar ruwan kyau tana da shi, Tafe take a hankali gaba daya idannuwanta a kansa hakama tunaninta da hankalinta, ga hannunta dauke da butar shayi da ta dafo Percil din Sarki yana turiri Sam bata san har ta iso kusan dan table din dake dauke da litatafai irin na adini a sama ba, sai da kafarta ta daki wajen ana dayanta ta tafi wajen da Hanja yake zaune ta....... Comment dinku na kashe ni, ina ji da ku ainun 11/14/21, 12:48 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*
Chapter 41 · 0% Book details