← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 114

Sashe 52

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 3 ADU'A Alhamdulilahi lazi ahyana ba'adama amatana wa ilaika nushur asbahnaa wa 'asbahal-mulkulillahi walhamdu lillahi, laailaha 'illallahu wahdahu laa shareka lahu, lahul-mulku wa lahul-humdu wa huwa 'alaa kulli shay'in qadeer. Rabbi 'as'aluka khayra maa fee haazal-yawmi wa khayra maa ba'dahu wa'a'oozu bika min sharri maa fee haazal-yawmi wa sharri maa ba'dahu, Rabbi 'a'oozu bika-minal kasali, wa soo'il kibari,Rabbi 'a'oozu bika min 'aazabi fin naari wa 'azaabin fil qabri. Wannann itace addu ar tanada muhimmanci sosai da sosai dumin kuwa kanemi alkhairin dake cikin yau dama kuma gaba sannan kanemi kariya da sharrin dake cikinta dama kuma gaba kanemi tsari daga azabar wuta sannan kuma daga axabar kabri kasani duk wanda ya karanta wannan addu ar yayin da ya tashi daga bacci to tabbas baxai wuni cikin kasala ba xakaga da akwai dayawanmu da idan muntashi daga bacci da zarar munyi sallahr asuba sai mukoma bacci wannan ba daidai bane dan yin hakan yakan haifarwa da mutum ciwon kai da kuma ya danga jin laziness ma ana kasala a jikin sa adukkan wuni ranar wasu ma xaku dinga jin suna cewa duniyar yau ta dai na yimusu dadi dama makamanta su to wannan duk aikin shaidan ne to amma in mutum ya lixamci yin wannan addu ar a kuma ya dage da yinta kullum to tabbas xai rage jin dukkan wani kalasa da yake yawanji kullum sannan Allah xai kare shi da dukkan sharrin dake cikin wannna ranar.....TUNATARWA CE YAN Uwa Tabas abin nasa ciwo ne, baban balaki ne , ko nace abu ne da ya ba gaskiya Watau Hanja haka ya sadaki yan matan nan daya bayan daya aman ba a tare ba , kafin yake mikewa kan kafafuwansa ya daina jin juwa Lale sun zo sun sadu da baban gayen da ya zamo burin yan matan garin matasa da manya, sun caji kudi na mamaki, aman kuma sun sha bakar wahalar da ta basu mugun mamaki harma suke tunanin kai du infa Princ dinsu yake yana hadiyar magannin karfi, sun yarda da karfin nada sun kuma yi saranda , danma harka ce ta aikinsu da ba zasu kuma yin fatan haduwa da irin wannan soldier din Hanja kam bayan tafiyarsu wanka ya yi ya tsaftace jikinsa , abinda yake bashi haushi da zina yana yinta gabansa na faduwa, a cikin tarawa da mata da yake yi abu daya ne yake cin ribarsa shine rage nauyin mara Haushin kansa yake ji idan yana yi iyayensa na fado masa a ransa Gaba daya a yanzun da ya gama eh lale ya ji ya daku da mugun ciwon dake damunsa na tsayin kwanaki , aman kuma zuciyarsa ta cinkushe Da sauri sauri ya fito ya koma dayan dakin nasa ya dauko wayar dake saman table dinsa warau telephone ya zauna ya shiga bugawa bangaren mahaifinsa domin ya tabata du inda take yanzun tana tare da Abih dinsa, so yake ya ji muryarsu , so yake kawai su daga ya ji koda iya salamar tsaftatacen bakinsu ne Ta yi ringin har ta gama ba'a dafa ba, hakan ya saka shi yin tsai da ransa tare da tunanin yanda zai yi Mah dake zaune saman bed kusa da Pah bayan an yi kira daga dakin tatar kiran dake shigo masu an shaida mata Hanja ne ke kira sai ta kife kiran ta koma kusa da Pah ta tsura mada ido Pah ya yi murmushi yana dan girgiza kansa ya ce" Bana so kina saka damuwar nan a Ranki, to wai meye shaidarki cewar ga abinda zai je ya yi a gidan?" Mah ta sada kanta a hankali hawaye ya tarun mata a cikin idannuwanta kafin ta ce" Na san a yanzu ta rigaya ta zama gama gari, ba garin musulmai ba na kafurai, a kasashen musulmai nema ake dan boyewa aman a kasar nan da ya zamana wa'inda ba musulman ba sun fi yawa gashi a bayane ake aikata ta, da zarar yarinya ta kai shekara goma sha takwas ta samu yancin da zata tsarawa kanta irin rayuwar da zata yi , wa'inda babu daya da zaka gani ace maka wai ba zaune take da saurayinta ba, domin tun a kananun shekarun nan suke raba gida da iyayen nasu, da yawa su tare da saurayin nasu.....kuma wannan nrml ne? Habiby kaina ke daukan zafi idan na tuna tsayuwa bayan dogon kwoncin kabari a gaban Allah, Habiby ta yaya kake so hankali ya kwonta da wannan lamari na yarona? Na san a wajenku wannan din ba wani baban matsala bane, namiji ne shi ya yi bukatar hakan ya sauke...... Aman kuma idan ba ga musulmai kuke fa sai abin ya zo min wani kala, Habiby dan Allah fada min a haka kake so na kwontar da hankalina? Ya ki ya yi auren kwata kwata, kuma ka ga yanzun kiran da yake ko na meye? Na tabata ya gama ne yana so ya ji ko na gane!" Murmushi ya kuma yi mai daci yana girgiza kansa ya ce" Bama kamar auren nan, Gamu a kasa ta daurin aure gaban alkali, shin idan na daura masa na nan cikin gida ta yaya zan tisa keyarsa ya sakawa matar zobe?, ..... Yaron nan sai ya laluba ta ji bana nan na san zai yi hankali!" Shiru ta yi na dan lokaci jin abinda ya fada kafin ta girgiza kanta ta juyar da kan nata gefe , sai kuma ta juyo da dan sauri tana kallon kansa Da sauri ta mike ta kara matsawa kusa da shi sosai ta zauna a bayansa ta dira hannayenta tana kallon kan nasa da kyau kafin da mamaki ta ce" Habiby gashi ne ke fitowa a kanka?" Idannuwansa ya lumshe jin tana shafa kan nasa ya yi murmushi a hankali ya ce" haka nake ji idan na zo shafa ruwan alwallah, aman ban duba ba na san kalar jan nan ne marar kyau ko?" Da sauri ta sauko kasa ta je ta dauko madubi karami ta zo tana ta kokarin daidaita masa ya ga kansa, dan shi fa ya daina kallon madubi kwata kwata tana fadin" Kalli, bakin gashi ne mai laushi, aman doctern nan ba cewa ya yi ba zaka kuma samun gashin kai ba da zarar ya fara zubewa da kansa shikenan ? Yaya aka yi yanzun yake fitowa?" Fuskarta ya tsurawa ido yanda take neman amsa ido rufe kafin ya saka hannunsa ya janyota jikinsa gaba dayanta ya rungumeta yana shafa bayanta a hankali ya ce" Baki da wani aikin da ya fi wannan mahinmanci ne?" Kanta ta dago a hankali tana kallonsa, idan har da gaske abinda take kokarin ganewa kamar yannayi ne na bukatuwa ke nuna kansa a kan mijinta,wani irin farin cikin da ta jima bata nuna irinsa bane ke daukaka a kyakyawar fuskarta Tabas tana gannin cenji, rabonsa da ya samu bukata irin ta kowani namiji har ta manta, yakan yi kokari dan karantawa sai dai ya sada kansa cike da dacin zuciya ya furta cewa kamar yadda dukan kwayoyin jikinsa masu karfi suka mutu hakama wannan lamarii A hankali ta ringa dadage har ta hade bakinta da nasa, wanda ya amsheta da hannu bibiyu kafin cikin raunin zuciya ya shiga furta mata" So kike a maimaita abinda ake yi?" Yana nufin so take sai ta kai wajen da take da bukatarsa shi kuwa ya gaza?, Ko ba komai shekarunsa sun ja, itanema da dan sauranta domin bata cike hamsin ba arba'in da kai ne, shi yasa yake cike da tausayinta, ya yi yinkurin sama mata mafita sau uku tana yi masa hauka tuburan da ihun ita zai ce ya salamawa wani dan sex?, Yakan ji kunyarta ya nuna mata akoy shiga haki mace take mai rai da lafia, bata da matsakar dake hanna mata jin bukatar namiji, ba zai so ta gajiya ba..............sai da ta masa fushi na mamaki domin bai san fitarta ba sai dai jin labarinta a saudiya ya rikita masa lisafi ya so ya ringa barin zance da tsufansa da kyar Hanja ya dawo da ita ya saka su gaba ya masu fada tas kamar shine aban su kuwa y'ayan A takaice, lamari na samun sauki ya bayana kansa a wannan rana, hakan ya saka Mah zubar da hawaye tana rike da mijinta, Shima hawayen yake a kasan zuciyarsa ya ajiye hakan a matsayin sauki ne Allah ya bashi na lokacin da ya rage masa dan ya samu ya mora rayuwa da iyalinsa cikin farin ciki, hakan ya saka shi godewa Allah a kasan zuciyarsa bai yi a bayane ba dan kar ta hau kukan nata, shi kam yana gannin shagwaba a wajen maman Hanja kamar ba ita ce mamansa ba idan tana gabansa zata ringa zuba shagwabarta ne ............................................ Barci mai rai da lafia ta yi, tana farkawa kuwa ta kimtsa kanta ta saka warta jar riga mai dan kwali fari domin tana da wani sharrr fari kal har kasa Dan yana dan kwalin ta yi kafin ta dauko wayarta da Mah ta bata ta fito ta rufe dakin nata tana baza sansanyan kanshin nan ta nufi wajen accenceur dan ta sada kanta da bangaren wajen Mah domin ta san Iman na cen Gannin kamar mutun ne ya shiga zai rufe da gudu ta karasa ta saka hannunta ta rike hakan ya sa ya kara budewa abin Gabanta ne ya tsinke ya fadi haka shima a lokacin da sukai ido hudu A hankali take kara takawa dan shiga domin ta rigaya ra rike ba zafa juya ba, shi kuwa a haka ta samu kansa da dan jimke hannunsa na hagu ya cire dubansa a kanta ya matsa gefe yana jira ya ga iya shege irin na yar nan A gabansa ra rsata tana tura bakinta, sosai ta samu zuciyarta da aiko mata da tambayoyin da suke iya sakata daria, irin tambayar nan da kai zaka yiwa kanka a kasan zuciyarka ka ji wata mahaukaciyar daria na son kubce maka a lokacin da baka shirya ba A hankali ta samu marar jin kanta na karkatawa dan kallon hannun nasa, Kwal uba to wai shi hala ba jijiyoyi ne irin na mutanr a jikinsa ba, mesa ce a jikinsa? .............hoton wani wada ne ya fado mata a rai wanda suke wajen babar
Chapter 52 · 0% Book details