← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 114

Sashe 84

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 5 Marin da ya wankawa matar tasa tamkar wanda ya saka mata sakata a bakin nata ya gume mata Koda yake a kalamansa ta samu yaren shiru ta arawa kanta kafin da sauri ta juya ta nufo dakinta jikinta na bari ta rufo Zamewa ta yi nan kasa hannayenta na rawa baki daya ta kurawa waje daya ido Tabas an yi haka, a hankali ta shiga tunano ranakun da take shiryawa ta fita gari idan kucakin namijin da bai amsa sunnan namiji ba ya yi gigin tunkararta ya nuna mata so irin tizga ahin da take yi, ba zata manta ba har kara koyon karatun wulakanta namiji take yi Ba zata taba mantawa ba ranar da ya nuna yana sonta har ruwan bakinta ta furza masa domin a lokacin har kiransa ta yi da wani muninsa kamar gwogwon biri, ba zata manta tana masa diban albarka yana share zufa yana karra kallonta har ta dire aya ya ce da ita dan tana da kyau kuma tana yar mai kudi ne take masa irin wannan wulakancin ?, Shin shi ba dan adam bane ko ta ga alamun a halitarsa an rage shi da wani abu?, Dan ya zo ya nuna mata so sai ya kwashi kashi irin haka a hannunsa? Ba zata manta irin hucin da abokinsa ke yi ba yana fadin Oga ka barta a gidan nasu mu nuna mata muma irin namu ikon, aman sai ya ce da su wannan ta haramta wa irin haka a gare su, wannan din ajiyar oga ce, ta oga ce kuma sai ta haifawa Oga abin alfahari! Wani kukan ta kuma rushewa da shi na dana sannin mugun halaya irin na yan mata masu jiji da kai da neman fitina da tunanin su sun fi kowa Ashe ita ta janyowa kanta wannan rayuwa?, Gashi dai sanadiyar rashin lafiyar da ya yi ya karya abinda ya mata da kansa wanda yana da makarin tsayin shekarun nan wanda tamkar wace ta yi barci ta farka ta ganta da shekaru zagaye da ahalin gidan Oga masu wuyar fasara Hauka jajir ta zuba masa a sume ya kaita gidansu nan ta tarar da sai yayanta daya rak da iyalinsa mahaifinta ne dama ya rage mata shima ya rasu , bayan ta sanar masa komai ya karra yi mata nasiha ya lalabata kan a yanzu gidan mijinta shine kwonciyar hankalinta ta rungumi y'ayan da ta samu da shi ta yi kokarin basu tarbiyar da ita ta yi wasa da ita, koda kuwa Oga ya kasance mai baudaden hali da damansa a kan wani, tunda shi aurenta ya yi ya kilaceta , da wani ne a hakan zai aifata ya kuma murje ido ya mayar da ita dakin ziyararsa, duniya ta yi lalacewar da baka yiwa mutun komai bama yana son ya kasaraka bale ita din ta yi garaje da yawa, dan haka ta kula ta kiyaye ta yi hakuri Oga kansa tana iya mayar da shi yanda take so koda iya cikin gida zai dawo tausasashe wa su a waje kuwa a ogansa yake da kyau, dama shi rayuwarsa ta yan jagaliya ne shi ba barawo bane ba kuma mazinaci bane, da kyau a halayansa akoy na kirki tunda yana sallah ai a yi masa uzuri, shima kuruci ta saka shi aikatawa, duda hali na kuruci zafin sonki ya saka da ya maki hakan bai yarda makarin ba, a yanzu da lokacin ki dawo hayacinki ya yi kib ga ya karya gaki kuma da ranki da lafiyarki ,sai dai a karra yi masa adu'a Allah ya shirye shi, ya ahiryar masa da zuri'arsa Ta ringa rusa kuka a lokacin tana shaida masa batama san inda Muneerath ta shiga ba, ya ce Wai ta samu aikin Hostess aman bashi da tabas tunda bai je ya gani ba, wai a waya aka fada masa a waya, kuma yake zaune hankali kwonce y'a mace?, Ita kam ba zata iya zama da mutun irin Oga ba, zata koma aman da zarar yarta ta dawo zata kwaso y'ayanta ta dawo gidansu Shi dai rarashinta ya yi ta yi, a nan ya kwaso mara tsabar dukiyarta da aka raba gado ya jingine da takardun gidaje har kwaya biyar, da kudin dake banki milioyi na gadon da suka gada ita da shi a wajen mahaifinta, ya dora mata da fadin gadon Mahaifiyarsu bai taba zuwa inda suke ba, kasancewar kasa ce ta nasaru shi bama shi da ra'ayin bin kudin nan da dukiyar, wanda yake cikima sun ishe shi A hankali ta kara rike kanta dake sarra mata tana wani kukan na takaicin rayuwarta, tabas ta yiwa kanta ila, yanzun ta ina zata fara da tarbiyar y'ayanta?, Har yanzu ba wani jituwa suke da namijin ba, matan kuma su uku ne du a wani bambarakwai suke kallon cenjin da ya samu, aman ba komai kamar yadda datijuwar malamar islamiyar da take zuwa take fada mata cewar adu'a, da adu'a zata Wayi gari ta ga abinda yake impossible Allah ya mayar mata da shi possible, Oga kansa halita ne na Allah, akoy masu kashe kashe da suke dawowa su zamo tamkar basu taba yi ba, idan har ta jure kaima Allah kukanta kokowar da ya dace ta dankara a tunaninta tana barci Allah zai yi mata shi ta hanyar shiryar mata da zuri'arta baki daya Tuna wadinnan abubuwan ya sakata saurin mikewa ta shige bayin dakinta dan ta dauro alwallah ta hau salayarta har a yi kiran sallah Saudat dake tsaye a tsorace tana kallon Muneerath jira take ta fashe da kuka ta yadda otama zata samu ta fashe da shi na tsabagen tsagwaron tsoron dake cin zuciyarta na wannan hargitsi da aka yi A hankali ta dora hannunta dake rawa a hannun Muneerath a sanyaye ta ce" Munee kar ki yi kuka kin ji?, Dan Allah mu je idan ta huce sai mu dawo ki bata hakuri kin ga ba'a yima iyaye magana a haka, ki ga mu yan africa ne da mari iyayenmu ke nusar da mu ba da rarashi ba, mu je idan ta huce sai mi dawo ki yi hakuri" Da mamaki Muneerath ta juyo jin wai karta yi kuka tana kallon Saudat Me zata yi banda dariya, ai kam ta bushe da daria tana jan hannun Saudat da ta fara kokonton anya ba Allah ne ya hada ta da mahaukaciya kawance ba? Dakinta ta jata mai dauke da gadonta daya sai sif din kayanta Sunna shiga ta rufe ta saka hannunta ta kunce yalwatacen gashin kanta ta barbaza shi sosai ta zauna a kasa nan tana kara cusa hannunta cikin gashin kan nata kafin ta dago ta kuma yi yar dariya tana girgiza kanta tana kallon Saudat da ta kasa zama dan a tsorace take ta ce" Kin san me hakan yake nufi?, Kin san me wannan ranar take nufi a wajena?, Wannan ranar tana nufin babar ranar da ban taba riska ba mai dadi da farin ciki, wannan ranar itace ranar da nima zan fara tinkaho da kaina, kin kuwa gane me nake nufi?" A hankali saudat ta girgiza kai tana kallonta Muneerath ta nuna mata gefenta tana nufin ta zauna A hankali ta zauna a gefen na Munnerath din Muneerath ta kamo hannunta ta ce" Saudat, a da ba tafia ba idan namiji zan kawo a gaban Mamanmu walahil azim zata kare mana kallo ta cire kanta ne ba tare da ta fahimci jinsin namiji na kawo mata ko mace ba, ke bara na kare maki magana idan ana magana aka ce min yar iska sai ta daga kafada ta ce ita ina ruwanta in ina so na zama karuwama matsalata ce!, Saudat idan kin ga na yi doguwar magana da mahaifiyata to fa a kan kudi ne, shima kudin da take nema ido rufe dan kawai ta siyo maganin mata ko me? Ta kawo ta yi ta sha wanda ban san ko na menene ba, ita dai idan kin ga tana kwalkwaltu to fa dan ta gyarawa Oga ne, a kan Oga tana iya batawa da kowa, a kan Oga tana iya kisa, Saudat nakan yi kuka na tsayin wuni guda ina tambayar kaina me yasa ko irin na sauran yan uwana da zaki ga idan abu ne iyayensu sun shigar masu fada ne ko idan aka zagar masu y'aya iyayensu na tarewa ni tawa uwar sai dai ta taya mutanen a zage nin?, A lokacin da na kawo maganar ga wanda nake da burin aure watau sarki da mamana aka wuni ana min daria ana cewa mahaukaciya ce ni, daga karshe suka ce gwara na kama dogari marar galihu idan Allah ya tsaya min ya ji tausayina sai ya aureni, dan kuwa ba wanda zai so kirtitinar bak'a irina!, Saudat a dayan burina da na nuna ina son zama Hostess kishiyar mamana ta ce sai dai na zama karuwar yan gugan gidan jirgi idan na yi daraja, walahi a gaban Mamana ta fada sai kawai maman nawa ta yi daria tana fadin wa ya ga yar baka kirin, gaskiya Oga ya yi haihuwa a nan, a wannan ranar ce da abin ya min ciwo muka kidime da fada a gidan nan da yayuna domin aun samu abinda suke so, oga na zuwa ya raba mu aka fada masa komai ya ce du ubanda ya kara shiga harkata walahi zai iya yin komai, a ranar ne ya dauke ni ya biya min kudin koyon iyo, sannan yake bani yan kudade a kai a kai dan na yi yan bukatocina, ya ce koda ban zama ba na gwada" Muneerath ta dago da idannuwanta da suka cika da kwallah sosai tana kallon Saudat dake hawaye ta ce" Ashe nima zan ga ranar da mahaifiyata zata daga hannu ta dake ni dan gyarana? Ashe zan ga ranar da Umana zata titsiyeni kan na fada mata daga ina nake?, Ashe zan riski ranar da mamana zata daga dan yatsarta dan ina cikin damuwa?, Saudat a nan ake fada ni da fada mutun fiye da bakwai tana tsaye tana kallo ba zata yi magana ba bale ta shigar min , ashe dai mamana na cikin duhu ne ya sa na ga rayuwa irin wadda na gani.....? Ta karashe maganar da fashewa da
Chapter 84 · 0% Book details