← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 99 OF 121

Chapter 98

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Ganin hasken yasaka taji hankalinta yadan kwanta da agogo take amfanie idan lokacin sallah yayi sai wajen karfe dayan dare sannan barci barawo yadauketa

Washe gari bayan tayi sallar asuba taji cikinta yana murdawa saboda yunwa tarasa yazatayi inama zatasamu abinci tashi tayi tasoma zagayen gidan dakunanda suke gidan sunkai goma kowanne dakin Kalar kayanda suke cikinsa daban ne danadayan"" karshe tasamu kitchen dakayan ci gasunan kayanmiya gasunan jawur dasu saikuma kayan lambu kawai sutadibo tawanke tadawo falon tazauna tasoma sha takwantarda hankalinta dankuwa tasan baranar zuwanta gida abudaya take tunani Usman tambayoyinda suke cikin ranta sunada yawa kuma tarasa wazai amsamata amsar tambayoyinta


Bangaren Usman washe gari muktar yatafi hospital din tareda su malam yagaisa da Usman Wanda kansa yake done baicewa ko wa uffan" su hajiya suka jajantawa juna"" muryan Usman sukaji yace hajiya muje gida haka Dan Allah"

Kusan tare suka kalleshi hajiya tace gidakuma babangida aikanabari kasakejin karfin jikinka ko??? Yagirgiza kai hajiya bazan taba warkewaba muddin dagaskene andaukemun Deejarh na inaji ajikina tana gidan nan bakudai duba dakyauba

Hajiya tace haba babangida kazama mai tawakkali mana insha Allah khadijarka zatadawo gareka kadaina kukan nan kamar mace tunshekaranjiya haryanzu koruwa baka hadaba aikoyunwa kawai ta isah tasamaka ciwo

Murmushi yayi mai ciwo yace abinci hajiya aini nayi bankwana da abinci kamaryanda nayi bankwana da farincikina hajiya nifa bazan ma kwana ananba sainaga khadija


Muktar yanisa yace dad kayi hakuri kajirah kasake samun sauki saimuje kaduna gabadaya"" nikaina hankalina bakwance yakeba""

Usman yace wlh tana nan kusadani muktar gashi inaji tanakiran sunana Dan Allah kutashi mutafiii idan bantafiba hankalina sake tashi zaiyi ganindai Usman yakafe lallai sai sunje kaduna babu yanda zasuyi haka suka karbi sallama akarubuta masu magunguna suka kama hanyar kaduna hardasu inna

Suna Isowa kofar gidan habu yayi hon maigadi yabudemasu yakunna kan motar motarsu muhd suna baya Dan aciki su muktar sukashigo

Anatsayarda motar Usman yafito yayi cikin gidan dasauri kaitsaye hawa nahudu yahaye yabude dakinta anan yacikaroda bargonda ta lullube ahankali yakarashi ahancinsa yashaki kamshinta yalumshe ido jiyake tamkar yanzun khadija tayafashi saboda kamshinda yakeyi"" dakin yasoma dubawa yana kwalamata kirah harcikin toilet yagama bade bagarenta danema Amman baigantaba cikin falon Yakoma yarumgume bargon yafashe dakuka

Damadai Usman kuka bayayimasa wuya kamar mace su hajiya suna shigowa basu ganshiba hajiya tace to inakuma yayi lubabatu ce tace yana saman duk tare suka rankaya saman sukasameshi yana kuka

Labila takurah masa ido sannan takalli hajiya tace waimeyake faruwane haryanzu banga sahiba ba??? Meyasa dady yake kuka??? dukkansu takebi dakallo tanayimasu tambayar akarasa Wanda zaibata amsa Usman ne yamike kamar Wanda akatsakurah yayi waje hajiya tanakiransa yace policetetion zaitafi muktar ne yabi bayanshi waje sukasamu su habu suka dunguma zuwa opishin yansanda wajen abokinsa idris yatafi dayake DPO ne bayan sungaisa Usman yasanardashi

Yace wlh yasamu labari Amman sunanan sunayin iyah bakin kokarinsu kuma insha Allah duk inda take za aganta sundade cen anayiwa Usman tambaya tareda ma aikatan gidan Amman usman yace baya zarginsu dantare sukaje sallah

Towama za adorawa laifi haka sukadawo gida jiki sanyaye hajiya tace asanar masallaci domin atashi da addua Allah yabayyanàta duk inda take

Lubcy kam dagekawai take kallonsu saiyanzu labila tasan mekefaruwa taci kuka harma yasake jawomata wani zazzabin kullum cikin addua take Allah yabayyana sahibarta yanzukam Sam batadorawa lubcy wannan aikinba

Kawai tahakikance akan waninedai maijin haushin babanta"" rayuwa kenan Usman cikin sati biyu karkuso kuga yanda yazama kullum yazauna baidawata magana saita khadija saikuma yawan tunaninta
I

Kullum zakasameshi bangarenta yatasa kayanta agaba yana kallo watarana yayita surutu saikuma kasameshi yana kuka"" labila makusan hakan saida lubabatu tayita basu baki tuni muktar Yakoma sannu kan hankali labila taware Usman mahakan yasama mata admission tawuce London dantacigaba da karatunta Usman mayakoma bakin aikinsa!"

Khadija sannu sannu hartasoma sabawa dagidan abunda yake yawan bata mamaki kullum saitaji kamar anayimata motsi acikinta tun lokacinda tacika wata daya agidan takejin hakan

Saikuma yanzun taji motsin ya yawaita gashikuma mararta tasoma tasowa kamardai maiciki yanzun balaifi tanayin hargirki taci kuma dazaran kayan miya sunkare saikawai tasake ganin wasu

Bayan watanni uku alokacin kam khadija tasan cikine da itah tashiga tashin hankali ita dabakowa agidan towaye zai taimaka yakaita asiviti gashi bakowa agidan"" koma adadin watannin cikin batasaniba nidai inakan kirgamata watansu uku wajen yawon shakatawa yanzun tayi hudu anan cikinta Yakama kwata bakwai kenan

Karkuso kuga kirmansa kamar gobema zata haihu danyagirma sosai duk dayake cikin budurwane!"


Usman zaune cikin falonsa suna firah da lubabatu tanacewa yakamata yadauko Abdul majeed yadawo hannunta"! Yakalleta da mamaki yace yanzun kuma kefa kikace bakyason hayaniyar yara

Tarausayar dakai tace toyanzun gidan nan yamun fadi nidaya!! Shiru yayi daga bisanie yace shikenan zanyiwa hajiya magana kometace shikenan"" tace harsaika tambayeta haba usman to indai bazaka daukoshiba kasamamun Yar aiki wacce zanrika ganie kuma tana tayanie aiki


Yace shikenan kamar dayaushe kikeson ta??? Tace umm
Nifa tafiyama zamuyi namanta bansanar dakai ba Usman yakalleta kamar zaiyi magana saikuma yafasa kansa yajingina jikin kujerah yadafe saitin zuciyarsa dayakeyi masa ciwo lubabatu takalleshi tace yadai kociwonne??? Kaiyagyada mata tace sannu yadaga mata hannu alamar yauwa"" tace kai ni wlh ciwon nan naka yasoma isata ayi Abu bayajin maganie

Ya murmusa yana lumshe ido yace baisamu ingantaccen maganinda yadace daciwonba"" tace kamar wanne maganie kenan ai atunanina babu maganinda zai gagaremu siyensa komai tsadarsa

Yayi saurin tarar nunfashinta yace akwai mana ai maganin ciwona khadija ne muddin baxan gantaba ninasan nayi bankwana da lafiya harkarshen rayuwata Nina San sonta shine zaizama ajalina

Ahankali lubabatu taja siririn tsaki wannan abun na Usman yasoma Kaita makurah ko kwanciya sukayi duk ranarda yasamu tabashi hakkinsa babu sunan wacce yake ambata sai khadija

Idan yakwanta kwana saidaifa kowa nagidan yadade kunnuwansa dan sunanta yaketa kiran hargarin Allah yawaye abunda yakekuma bata mamaki Sam Usman yanzu baidamu dayakwanta da itah ba

Dantun bayan batan khadija yanzu tsayin wata hudu Usman saudaya yakwanta da itah koshi ita tajashi dankuwa haka kurum taji tana ra ayinsa ranar taci kuka Sam kashe khadija baiyimata ranaba tunda gashi haryanzu Usman baidaina sontaba

Kuma baimanta da itah ba dukda abunda boka yace Amman kamardai shidin abun baiyimasa aikiba"" Amman su labila kam aiyayi masu""

Mikewa tayi tahaura sama ranta abace Usman kam baidamuba saima yasake mirginawa yasoma tunanin ruhinsa duk da haryanzu yana tunaninta Amman baisan yazaiyiba Sam yakasa tuhumar kowa yabarwa Allah komai"""


Akwana atashi hasarar mai rai cikin khadija yashiga wata Tara komai dakyar takeyiwa kanta"" zaune"" take cikin falo" kamar""daga sama taji muryar Usman yana kwalamata kirah zunbur tamike tasoma waige " jin kiran yayi yawa kawai tafita harabar gidan tunda take bata taba kaiwa harabar gidan ba

Hartasa kafa zata fita tatunoda maganar wannan aljanar jiki bakwari tajuya zatakoma taji yasake kwallah mata kirah batareda shawarar komaiba tasakai tafitaa


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!!*☠
Chapter 99 · 0% Book details