← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 9 OF 121

Chapter 12

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Malam garba kuwa dashi da babushi duk daya kobanza yana bala in tsoronta tunda ba banza tabarshiba""
Duk saurayinda yace yanason ameena har gigi yakaishi kofar gidansu huwaile ce zatafito tazageshi ta uwa ta uba"" hakan bazai ishetaba saita samu iyayensa tayi masu Tass kuma tace sujawa dansu kunne kartasake ganinshi kofar gidanta dayawa samari sunason ameena Amman balain huwaile suke gudu""
Tunranarda Usman yaganta yaji takwanta masa arai barinma lokacinda Abdul yasanardashi ainahin tarihinta saiyaji babu matarda yakeso aduniya sama da itah"""

Lokacinda mahaifiyarsa tayimasa maganar aure saida yafara neman shawarar abdul akan yasanarda itah"" dariya yasoma yimasa yace zakafara wautar taku ta yayanfari tomenene dankafada mata kokunyarta kakeji""

Dariya yayi yace wacce irin kunya Abdul tunani nayi yarinyar nan bataSanniba kawai dai saninda tamun inazuwa cin awararta lokacinda nake karatu" atunaninka itah zatasoni??? Nifa banaso nacutarda itah

Abdul yasake kwashewa da dariya yace kwantarda hankalinka mutumina indai ameena ce wlh bakada damuwa kasan sarai itama kamar akan kayatake agidansu yanda aka azabeta nikam hakan yayima kaga huwaile Batasan da soyayyar kuba ballantana ta fatattakeka

Tare suka kwashe da dariya yace fatattakadai abokina aitasan wadanda zatayiwa hakan sudinma rainasu tayi kodayake hakan datayi alhairi ne agareni dayanxu banine zansamu wannan kyakkyawarba"" sosai Usman yarude akan sonta cikinwai ma bata kwalliya Dan huwaile batabari waidan kartasamu samari

Ranarda yasanarda mahaifiyarsa tafadawa alhaji adamu yayi murna sosai Amman kafin yanema masa auren saida ya tabbatarda kasuwancinsa dayanda yasamu riba sosai fiye dakudinda yabashi

Bawani batalokaci yasanarda limamin unguwarsu dawasu abokansa sukaje kaduna sukanema masa auren ameena awajen mai unguwa

Saboda Usman yafadamasu komai akan matarsa""mai unguwa yaji dadi sosai yasa akakirah malam garba" agabansa akayi komai sunbada harda kayan nagani inaso dakuma kudin saka rana ahakan alhaji adamu yace asaka biki kusa kusa kumashi yaron yace basaitayi komaiba shizaimata kayan daki dakomai malam garba kam yayi murna duk dakasan zuciyarsa halbawa yakeyi shikawai yasan fitinarda zaihadu da itah agida"" mai unguwa yace totunda har hakane mezaihana adaurah auren ayanzuma idan ashirye kuke"" hakan bakaramin dadi yayiwa alhaji adamu ba babu bata lokaci yakirgo kudi dubu hamsin amatsayin sadakii

Goron saka rana shi akayita mikawa mutane mai unguwa shiyazama waliyin Amarya"" take akadaurah aure jama a suka shaida bayan yan gaishe gaishe"" alhaji adamu da tawagarsa suka kama hanyar kano cikin farinciki

Malam garba yanarike da sadakin ameena dagoro yatunkari kofar gidansa gabansa yanafaduwa"" yadade bakin kofar gidan dagabisani yashiga da sallama
Ameena tana tsakar gidan tana darzar wankin huwaile da fa Iza " ita kuma uwar ikon tana inuwa zaune tanayiwa fa Iza tsifar kaiii"" fa iza yartace Amman batareda malam tahaifetaba bayan tahaifetane tarabuda mahaifinta saita auri malam

Bagidan take zamaba saidai tanazuwa akai akai duk sanda tazokuwa kafin takoma komai ameena takemata duk dakuwa ameena tagirmeta""

malam yakalleta yadauke kansa aransa yace kinkusa hutawa da wahala ameena "" tunkafin yazauna huwaile tamike tanakallonsa yanda yake fara"a

Kujerah yaja yazauna yana mai fuskantar huwaile sannan yakwalowa ameenar Kira""
Huwaile tace haba malam yaxaka kirata bayankuma kana ganin wanki takeyi???

Cikin in inna yace ainaga ba wani abubane dannakirata badadewa zatayiba"" tace kaikasan wannan nidanakeso tagama dawuri tafita tuyar awara
Cikin malam yahau hautsinawa jin furucinta lallaikuwa akwai aiki jajir"" takatsemasa tunaninsa tahanyar karbe kudin hannunsa tana jujjuyasu tanakallonsa

Sunahada ido yaji zawo tamkar zaizubomasa"" tajefomasa tambaya kudin waye wannan??? Yace eyin eyin"" takatsamasa tsawa batambayarka nakeba""
Cikin kaduwa yace dama yarkice kinsan kwanaki kinacemun gashinan tagirma"" Amman"batada mabidi "" kinsan komai lokacine da"" katseshi tayi cikin karaji kamar mai magana da danta tace sai akayime??? Kafito kayimagana kadaina wani yan zagaye zagaye""

Saida yahade wasu yawu yace sadakin ameenà ne"" gakuma goro "" kafinma ya ajegoron tamike tafara liliyo ashar"" tawatsa masa kudin afuskarsa

Tace kayi gaggawar daukar sadakin nan kamiyar dasu inda suka fito nibantashi aurar da itah ba"" malam garba yashafo zufar goshinsa yace saidai kiyi hakurii Dan maigama tagama har andaurah auren

Wohoho inawuta tasakashi "" jitayi tamkar tarufeshi da Duka"" tace tabdijam wato Dan anunamun iyakata shine akaje waje aka kimtse magana tsofaffun munafukai dama ninadade dasanin duk yan unguwar nan munafukaine

Wato ana bakincikin yar tallarda nake doramata saida sukai kutunguilar samomata miji"" tonikuma sainaga wanne shafaffen damaine ya isah yashigo gidan nan yadauketa

Tallekuma yanzu akafara hartuwo tuwo zanfarà yimata tanazuwa kasuwa yan bakinçiki saidai su mutu kuma ko anki ko a anso ko anasonmu ko anakinmu dole aganmu akyale

Cikin sanyin murya yace kiyi hakuri nikainà badason raina akayi abunba aikin mai unguwane

Rufemun baki tsohon munafuki aikaine babban mailaifin kafadamun tareda mai unguwa kukayi cikinta dazaiñuñà maka iko akanta???


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 9 · 0% Book details