← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 95 OF 121

Chapter 94

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Dasauri suka karasa inda yake habu ne yacewa muhd taimakamun da ruwa Dan Allah dasaurinsa yadibo ruwan yamika masa ya yayyafawa Usman Amman komotsi baiyiba"" aka yayyafawa lubabatu tana farka takwamtsa ihu nashiga uku zaku kasheni"" habu yace kwantarda hankalin hajiya aimune sai lokacin tabude idonta

Idanuwanta tasaukar akan Usman Wanda ko motsi bayaya dashi dagawa duk daya dasauri tamike tayi wajensa tace mesuka masa?? Kufadamun mesuka masa""

Habu yace bakomai muje asiviti muhd ne yadauko mota suka taimaka akasa Usman cikin Mota sai asiviti"" likito wajen biyar suka rufa kansa Amman ko motsi baiyiba""

Take hankalin lubabatu yasake tashi tarasa inama zata sanya ranta taji sanyi karfa aljanun *hatsabibin boka* sun tsotse masa jinie Amman aiba hakan mukai dashiba

Ganin harrana tayi daya saura bawani haske kawai habu yakirah hajiya yasanarda itah tace itama tana asiviti labila ce batada lafiya Amman tafarfado yanzun hankalinta atashe tace ayimaza azodashi kano khalifa teaching hospital tanajiransu Zata sanarda doctor dinsa

Amman basu fadamata musabbabin abunda yasameshiba""" sunsanarda doctor zasu daukeshi zuwa kano akabasu sallama suka kama hanya har kano

Koda suka shiga sunsamu hajiya bakin kofa takasa zama anaganin su akazoda gadon Daukar mara lafiya akaturashi zuwa dakin taimakon gaggawa

Duk iya kokarinda zasuyi wajen ganin yafargado abun yafaskara abunda yayi matukar basu mamaki gashidai baya nunfashi Amman zuciyarshi harbawa take dasauri dasauri


Al amarin aljanie hayyanul zairi kuwa kwananshi daya dayini daya yana gudu asararin samaniya harzuwa lokacin khadija bata farfado daga doguwar sumarda tayiba sakamakon bangazarta dayayi

Baisake sa a guda yana guduba khadija tafarfado ahankali tabude idonta Kalmar dabakinta yasoma ambata kalu innalillahi wa Inna ilaihirrajiun

Saiyanzu take tuno abunda yafaru ahankali tasoma kallon wani bakon al amari kamar anagudu da itah acikin iska bakinta ne yasoma Karanto a uzubikalimatil lahi tammat min sharrima halaka""

Aljanie hayyanul zairi baisan Khadija tafarka daga doguwar sumaba radadin da yasomaji akirginsa tamkar ya chachumo wuta ahannunsa sune suka ankarardashi

Kafin yayi aune tuni sun lankawo daga sararin samaniya zuwa kasa kafin sukawo tunie khadija iskan dake tashi sama yasake sumarda itah

Saurah baifi sa o i susauka kasaba akayi wuffff akatare khadija tafada hannun wata farar mata maicike da kwarjini sannu ahankali tasaukarda itah kasa yayi daidai da farkawar khadija

Ganinta awata duniyar daban yasaka tafara jadabaya daga zaune wata iskace mai karfiii sukaga tatunkarosu bayan tagama saukowa saiga aljanie hayyanul zairi yabayyana cikin siffar jemage

Wani irin wargajine girmansa zaikai tsayin daki fadinsa ma haka""" faratansa manyane masu dauke damanyan kumbuna

Bakinsa dauke yake da zakwazakwan hakorah masu matukar tsinie ko wanne daya tsininshi yakai tsinin mashii kaurinshi kuma kamar kaurin takobie

Idanuwansa kadai abun tsorone "" idan yayi huciii wutace take tartso abakinsaa

Daganin wannan halittar wani mugun tsoro yakama khadija hantar cikinta takada tunda take ko acikin fina finai bata tabayin arba dawata halitta maigirma dakuma firgitarwa irin wannan ba """ Amman wannan karamar aljannar

Datake gabansa kamar bera yatsaya agaban kurah Sam bata tsorata daganinsaba""" wata kururuwa yayi wacce tasaka khadija shedewar kunnnuwanta na dakiku arba in

Tsawarsa daidai take da tartsatsin wuta gaba daya dajin kansa saida yasauya launi sakamakon wannan karar yayi girgiza saigashi yasake zama wanie katon basamude"""

Kallon kallon sukafarayi da aljannar daga bisanie yabude bakinsa Cikin nuna isah dakuma takama yace yake wannan aljannar kisanie wannan kalacina ne kigaggauta barin wajen nan tunkafin fushina yasauka akanki

Cikin murmushi tace kai awa kuma kaiwanene dazanbaka itah"" inabaka shawarar Kayi saurin barin wajen nan tunkafin raina yakaiga bacii

Dariya yafashe da itah yace ke kinsan kodawa kike magana??? Tace bandamu dasanin kokai waye bane Amman nasan zaluncine zaka aikata kuma ni naharamta hakan acikin yankina

Wata kuru ruwa"" yayi yace yanadakyau yarinya kisan kodawa zakija kafin kifara fada! Nasan kaf duniyar nan babu wani aljaninda baisanda zaman"" jajirtaccen matsafi kuma gawurtacce Wanda yafi kowa sanin sirrukan sihiri wato *hatsabibin boka* wannan dakike ganie aikinsace kuma nine akabaiwa itah jininta amatsayin ladar aikina""

Aljannar tasakeyin murmushi akaro nabiyu tace bandamu dakaiba hakazalika fadar sunan bakin azzalumin shugabanka bazai tayarmun da hankaliba inamai baka shawara ka gaggauta barin wajen nan

Aljani hayyanul zairii yayi wani huciii saiga wutaa tayi tartsatsi dasauri wannan aljannar tasa hannu takare dazaran wutar tataba hannunta saikaga tamutu tamkar acikin ruwa take
Wannan yasake fusatashi yataso mata kamar zaicinye namanta danye take itama tayi girgiza saigashi tarikida takoma katuwar kada mai tsananin girma dakuma bantsoro

Hakoranta manya manya faratanta kamar fartanya kaifinsu da tsininsu yakai kaifin takobiii take itah ma tasoma kururuwa tayi girgiza saisuka fara kallon kallo dagabisani suka rugo dagudu nantake kura tatashi sama bakako ganin gabanka jikake kafff sukahade waje daya karar hadewarsu kaisaikace dutse da dutsene sukahadu


Hmmm wai ance fada inba ruwanka dadin kallo zamuga yanda fadan aljanu zaikaya shin ko aljani hayyanul zairi zaiyi nasarar kashe wannan aljanar yatafi da itah??? Kokuwa wannan aljanarce zataci galaba akansa??? Waishinma itah wannan aljannar wacece??? Ya al amarin Usman Wanda yasuma haryanzu bai farfadoba??? Shin labila tafarka daga barcin da aljani saaagakimu yasakata??? Duka amsoshin wadan nan tambayoyin suna cikin cigaban labarin saiku kasance taredanie


Kuyi hakuri banda chaji wannan kawai kukasamu


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 95 · 0% Book details