← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 36 OF 121

Chapter 40

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Bayan kamar mintuna talatin tadawo taturo kofar tareda sallama"" Usman yana ganinta yadago kansa"" kujerar kusa dashi taja tazauna

Tanafuskantar doctor Wanda shima ya aje alkalamin hannunsa yana saurarenta tace nadubata batada wata matsala""

Doctor yace shikenan kina iyah tafiya"" tace to tareda mikewa tafita" doctor yanisa yana kallonsa yace dama ninasan babu wannan ajikinta kamanta a hospital din nan tayi haihuwa biyu inda munga wannan matsalar aidatuni mun maganceta

Kodama tanada wannan karin ai a take zamucireshi basai andau wani dogon lokaciba haihuwa dabata iyah yidakanta yadanganta dayanayin jikinta sannan kuma yaranta sunada matukar girma kofar jikinta bazata ishesu fitaba

Idan munga kamar za arasa wani acikinsu shiyasa harmuke mata aiki"" yakai karshen maganar yana kallonsa

Usman yanisa yace nagamsu da bayaninka Amman meyasa doctor yasanardani hakan???

Yace wacce asiviti kenan??? Usman yace abuja"" doctor yanisa yace baxaicemaka hakanba inhar ba ita tace yasanarda kaiba ai itah tanajin yanayi ajikinta koda yafurta zata iyah karyatawa

Usman yadago da alamun damuwa afuskarsa yace meyasato zatamun haka??? Doctor yace to wannan amsar abakinta zakajita kabari idan tasamu sauki kuka koma gida saikaji abakinta akwaidai manufaryin hakan

Yanisa shikenan doctor nagode bari Nayi waya yabashi hannu suka gaisa sannan yafito hajiya yafara Kira yasanarda itah sannan gidansu lubcy din

Ranar hospital din yawuni sai marece su hajiya sukazo labila kinzuwa tayi waisunada harda islamiyya washe gari yangidansu lubabatu sukazo harda kanwar mamanta anan suka barta suka koma

Hajiya kwananta daya takoma washe gari aka kai kudin auren Usman gidansu samira mahaifin abdul tareda abokansa sune suka nema masa auren ko hajiya baisanar mawaba danyasan zatace yabari sai matarsa taji sauki shikuma yanason bata mamakine

Ranar litinin aka kai sadaki akasa bikin sati daya duk da bahakan Usman yasoba Amman sunce sunason yin shirye shiryene

Sai anasaura kwana biyu daurin auren yasanarda hajiya itadai fatan alkhairi kawai tayimasa"" labila dataji labari murna tahauyi harsaida hajiya tabuge ta tace waikinji abunda akafada kiketa faman tikar rawa??

Tace najimana hajiya ba dad ne zaiyi aureba??? To idan banji dadiba mekikeso nayi??? Sainafadawa sahiba muhada faty na musamman
.hajiya takaimata duka taruga tana dariya tace banda shashanci mahaifiyarki tana gadon asiviti harta faty kikeyi??

To naga yanda zakihada Fatyn labila tayi cikin daki tana dariya tace aikuwa zakigani"" tunda lubcy tafarfado tamatsa akaita gida batason zaman asiviti

Doctor yakibata sallama yace takara hakuri hartaji sauki"" saida kanwar mamanta ta rarrasheta akan takara hakuri Usman yanazuwa Amman bainuna mata yasan komaiba saiyayima kamar babu abunda yashiga tsakaninsu
.
Wata zuciya tana rayamata kodai yafasa aurenne watakuma tana karyata hakan dole tanason taga *hatsabibin boka* totaya gata agadon asiviti wazatace yadaukomata madubin

Takaicii yabi yadameta nan take jininta yahau saida akaimata allurar barci dantasamu natsuwa
Washe gari kuwa da azahar akadaura auren samira da Usman akan sadaki dubu Dari hudu lakadan

Ranar samira tamkar tazuba ruwa akasa tasha saboda murna"" wai itace matar Usman" mutumenda yace bazai auretaba hmm gaskiya dolene tagodewa aminiyarta datakaita gun bokanta

Gashi tasamu soyayyarsa acikin ruwan sanyi yanzu dazaran tashiga gidan saikuma tayi yakin fitarda kidahumar matarsa wani murmushin mugunta tasakii

Saina rabaka da itah yazamana bakowacce mace agabanka faceni tasakeyin murmushin jindadi

Da marece motocin kai Amarya suka dauko samrat zuwa gidan Usman ranar ko asibiti baikomaba tunda yaje dasafe
Ranar Usman kam yahuce takaici dankuwa samrat batahanashi kantaba saida yabarshi Dan kanshi koshima yatausaya matane ganin tawahala sosai

Bayan yayi wanka yayi sallah yanamai godiya ga Allah daya sharemasa hawayensa yabashi samrat

Lubabatu tana asiviti batasan wainarda ake toyawaba"" yakanje dasafe kuma yajemata da abinci sambata kawo yayi aurenba Amman tagayanzu kullum cikin fara a yake kamar tatambaya saidaikuma takama bakinta

Kachar tabari takara sati tamatsa dole aka sallameta ta tattara takoma gida ranar kanwar mamanta tatafi

Tunda Usman yafita baidawoba saidare"" lubabatu tana bangarenta kaitsaye bangarensa yanufa yayi wanka sannan yatafi bangaren samrat

Cikin falonta yasameta tachanchade cikin adonta tayi kyau tana ganinshi tamike tatarboshi kiss yamata akumatu yace Amarya Kinsha kamshi

Tayi farida ido tace andawo lafiya"" yace qalau dauko mayafinki muje bangaren maman majeed kidubata tace to tareda wucewa tadauko sannan tafito suka jerah sunayar firarsu ta ma aurata

Tunda lubabatu taji muryan mace gabanta yayanke yafadiii" shine gaba tanabayansa yaturah kofa da sallama lubabatu ta amsa fuskanta tanakan matar da sukashigo tare

Usman ne yanuna mata waje yace tazauna kusa dashi tazauna tareda gaidata Anty inawuni yajiki

Duk daharyanzu lubabatu takasa yarda dagaske usman aure yayi tanakan gadon asiviti tace qalau naji saukii yagidan

Tace Alhamdulillah "" usman ne yace maman majeed ga zainab amaryatace yajuya wajenda zainab take yace zainab ga matata kuma farincikina itace ni nine itah inasonta fiye dakomai banason abunda zaibata mata rai inafatar zakitayani wajen faranta mata rayuwaa

Baki tatabe cikin ranta tace basaika fadamun yanda kakeson matarkàba jinhakan bazaihana inrabakuba

Amman afili murmushi tasaki tace karkadamu zanyima fiyedakai murmushi yayi yace nagode yajuya wajen lubabatu yace ga kanwakinan dan Allah inhar tayi badaidaiba kitsawatarmata kiyita hakuri kuma dukda nibanida matsala ta bangarenki

Tasaki murmushin yake tace karkadamu bazantaba sauyawa ayanda kasanniba fatanadai Kanwata tarikeka amana""" takai karshen maganar tanajifartà dawani kallo nikam nace dàbiyu kenan

Kusa dàkunnenta yaradamatà magana kigodewa kanwarnan taki tanaji dani sosai nasamu abunda nakeso gaban lubcy yabada rass tace nashiga uku😳 ya akài hakan tafaru????gabadaya tashiga tashin hankali Amman dayake yarduniyace saita wayance


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 36 · 0% Book details