← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 121

Chapter 7

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Sautari talakawan anguwar suna matukar mamakinsa saidai shi Sam baidauki wai girmankai yadorawa kansaba girmankai Wanda mafiyawan masu kudi suka sakawa ransu" dazaran sunyi kudi zasufara daukar kai Sam sumanta da lokacinda suke fakiransu gabadaya abokanansu nabaya saidai idansuka wulgo cikin mota sudagamasu hannu wanikoma dagahannu bazaiyiba yama manta dayataba zama wata majalisa"" dazaran yaga Wanda yasani talaka saiya saki gilashin motarsa yakauda kai gefe tamkarma baiga mutumen ba

Wannan girman Kaine kuma duk Wanda yakedashi yasani yakama hanyar halakarsane saboda abunda kesauran halakarda bawa girman Kaine dagahakan zakafara hassada kanadaukar kanka wata tsiya bakaso wani yayi kudii kamarka kasani ko shaidan abunda yasakashi hassada girman Kaine haryakaishi ga fadawa halaka
. Allah yaciremana girman kai dakuma hassada acikin rayuwar mu Ameen"" saida yajirasu dukansu sukayi alwala sannan yawuce suma suka Mara masa baya "" zuwa masallacin unguwar

Babu nisa Dan gabangidansa kadan akagina masallacin Ku San babu kwadagar kowa wajen ginin shine yadauki nauyin komai masallacinda aka kawatashi ko acikin manyan unguwanni saikayi dakyar kafin kasamu mai kyansa"" Dan asalin wajen wata tsohuwar ginace akazagaye korufin kwano babu akarosheta akagina wannan masallacin Wanda fankoki da ac kamar suyi magana idan kashiga kamar karka fito sannan gatarin littafai nan idan kanason karantawa"" bayan an idarda sallah"" yakoma gefe yasoma karatu inda sauran ma aikatan wajen sukasoma karatun zuwa adanjima sukafita zuwa wajen aikinsu""

Dai daikun jama ar wajen suka soma fita ahankali haske yanagama wartsakewa shima yatashi yakarasa wajen liman sukai musabaha sannan yafita zuwa gidansa tun a hanya suketa gaisawa da makotansa haryakai gidan dashigarsa yasamu ma aikatan gidan sungama aiki shikawai suke jirah bayan sungaisa yawuce cikin gida sukuma sukawuce

Dayake yauranar lahadine babu aiki duk da yakeshidin dankasuwane yanada campani masu yawan gaske Amman yanayin tsarinsa tamkar aikin gomnaty dashi da ma aikatansa
Basazuwa aiki asabar da lahadi acewarsa takasance ranar Hutu gakowa saboda idan sukaje takwas nasafe basa tashi sai karfe takwas darabi

Ranar lahadi da asabar taxama ranar Hutu kowanne magidanci yafuskanci iyalansa yaji damuwarsu"" idankuma marar aurene yaje wajen budurwarsa idankuma yanada wata lalurah yayi koyayi ziyara"" musamman jumua dan ranar juma.a karfe hudu aketashi

Shikuma ranar asabar inhar yashiga gidansa bayafitowa bayan zuwa masallaci yanatare da matansa yakasance lokacinsune komai sukeso kosunada damuwa saisufadamasa duk da kafinsu kwanta kowanne darema suna ganinsa

Kaitsaye bangarensa yanufa yasakeyin wanka yakwanta kasancewar barcin jiya Yana nan a idonsa take barci yayi awon gaba dashi

Hajiya lubabatu ce tashigo dakin cikin takun kasaita balaifi yautayi kwalliya dass da itah fuskarta saifitarda sihirtaccen murmushi takeyi ahankali tataka zuwa saman gadon taxauna hannu tasaka tanashafo lallausar sumar kansa Wanda takwanta luf gwanin sha awa hakika tana matukar son mijinta dakuma kishinsa fiye da tunanin mai karatu hakaxalika tana mutuwar kaunarsa da begensa fiye da tunanin duk wani mai tunani taja gauron numfashi" atake talulaya wata duniyar daban

Sai farkawa yayi yasamu hajia lubabatu tasakashi gaba hannunta yanakan gashin kansa idanuwanta suna kallon saitin drawer yayi kuru yana kallonta daga bisani yasaka hannu yashafo fuskarta tadan zabura sannan tasaki murmushi hannu tasaka tajawo hannunsa daga kan fuskarta tace harkatashi ???

Murmushi yasakeyi akaro nabiyu yace ah tunanin mekikeyi??? Taware ido waini batunani nakeba
Yace bayan Wanda nagani"" tayi murmushi ah ah alhaji wai shin inakabar Kanwata??? Tayi saurin kawarda zancen dawannan tambayar"" yace tanadaki tanabarci mana""

Cikin zolaya tace barcin gajiyako nasan halinka basauki jiya bakabarta tahutaba duk da take yarinya batasaba sosaiba
Yayi murmushi yace kinfara ko lubabatu yayi kyau inhar nakama ki akoma zakiyi bayani

Aransa kuma yace hmm inakikasani saida ta talemun kaza tacinye sannan tasoma barci kamar kasa yayi maganar yana mikewa daga kan gadon yashiga toilet domin watsaruwa


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 4 · 0% Book details