← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 118 OF 121

Chapter 017

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Mai martaba yajinjina kansa yace Amman kewayafada maki wannan labarin??? Ko wajensa kikaji???

Tagirgiza kai tace shiyanzu baimasan yanada yaro kaleed ba haka baisan yataba aureba kamar yanda suka mantardashi matarsa mahaifiyar kaleed

Nikaina hakan taso ayimun saidai Allah baicika mata burintaba"" mainartaba yace lallai nayarda haryanzun akwai sauran jahilai aduniyar nan kodayake bazasu kareba ai yanisa Amman taya zakifahimtar da yaron nan dantunda yake baitaba sanin basune suka haifeshiba yanada shekara biyar aikomai yamanta Amman bari akirah yayan kiji yakalli fulanie yace saka akirashi yanzun harda maidakinsa tace to sannan tamike tafita

Wata baiwa takirah tace tayimaza gidan sarkin fada tace anakiransa inji mai martaba"" tace angama rankiyadade dasaurinta tahanzarta domin cika umurnin uwar dakinta.


Ba adauki tsayin mintuna ashirinba sukashigo tareda sallama Sundaukama ciwon Hauwa ne yatashi da akace anakiransu yanzu yanzu

Ganinta zaune yasaka suka saukarda. Ajiyar zuciya"" mai martaba yanuna masu waje suka zauna " yakalleshi yace kokasan wannan??? Yayi nunida khadija

Da mamaki yace wannan kamar na ima Amman tafi na ima fari kodai itace idanuwana ne suka soma ganin buji buji gabadaya sukasa dariya"" yakalli Hauwa yace inna koban fadi gaskiyaba???

Mai martaba yace kafada kam Amman kamace kawai wannan ba na ima bace sunanta Khadija Yar fateema yayarka wacce hajiya tabaro a najeria

Zunbur yamike yace Allahu Akbar Allah maiyin yanda yaso ashedai darabon zanga jinin Yar uwata "" yamatsa yana kallon khadijar maimartaba yace bawan nan ba tazone akan maganar yaronka sultan

Yace tofa Allah yasa lafiya "" yace qalauma kuwa kalli wannan yaron"" yayimasa nuni da anwar dayake hannun Hauwa" hassan yace tsarki yatabbata ga mahaliccin kowa dakomai ai wannan photocopy din sultan ne""

Yayi maganar yana Daukar anwar yana kallonsa"" mai martaba yace wadan nan yaran Na khadijane

Mahaifin wadan nan yarankuma shine mahaifin kaleed tazone sabodashi tanaso tasanardashi ainahin tarihinsa ..gadai yartaka nan kaji daga bakinta"

Hassan yakalli khadija yace ikon Allah sanardani yata menene gaskiyar lamarin"" ?? Khadija tasake sanardashi komai kamar yanda tafadamasu takai karshen maganarta dacewa shikanshi Mahaifinsu baisan meyakawoni nandinba dankoda nafadamashi ma zaice baidawani yaro kaleed

Hassan yace babbar magana yata sultan baisan ainahin tarihinsaba nikaina naso sanardashi ganin yanda yakeson Zainab kamar me ammankuma yanaganin tunda iyayensu daya babu aure tsakaninsu

Amman dagashi har itah suna mutuwar son junansu duk dabasufito suka fadaba itah yanzunhaka takasa tsayawa dakowane saurayi shidinma yanzun yakeson yayi aure danyakaucewa soyayyarta

Naso infadamasa gaskiya mamanshi tahana waizantono masa miki tayiyuma idan yaji bamu muka haifeshiba yagudu yabarmu tunda bamusan inda zamuga iyayenshiba

Amman yanzun tunda kinsan asalinsa komai yazogidan sauki zuginda zaiji kadanne" Khadija tace hakane yanxun yana ina???


Hassan yace sarkin buga boll aiyana filin wasa bakyarabashi da kwallo yaro kamar Dan danbe sukasa dariya khadija tace shikenan idan yadawo zanso ganinsa

Wata baiwace tashigo taduka tace sarkin gida yace mutanenda suke tare da bakuwar hajiya sunce zasuwuce" khadija tamike Sam tamanta dasu

Mai martaba yace batare kuke dasubane zasuwuce tunyanzu???
Tace ah ah batare mukeba abokin babansune dayake kasuwanci anan shine yacemasa idan nazo yadaukeni yakawo nan bari nayimasa godiya.
Tayi maganar tanafira

Sam tama rasa hanyarda zatabi tamiyarda itah waje saida tatambayi wata acikin bayin gidan tanuna mata""" bakin kofar fadar tasamesu dafara a takarasa wajensu tace harzaka wuce ??? Yace ah maigidanki yakirah yace meyasa kika kashe wayarki yakirah yaji kinsauka

Nacemasa harkintsufa gidan sarauta murmushi tayi tace kaga kuwa wlh tunda nakasheta dazamu
shiga jirgi namanta inkunna nafa gode yace bakomai Allah yahutarda gajiya tace ameen
Sukai sallama takoma cikin gidan falon Hauwa u tasamu anjeramata kayan abinci da abubuwan motsa baki kayan marmari dasauransu""

sallah tafara gabatarwa tadan watsa ruwa taji sanyi jikinta sannan taci abincin saida takoshi tayi hamdala kuyangin gidan suka kwashe kayan dataci abincin

Wayarta tadauko takunna takamo lambar Usman takirah tanasoma ringing yadaga cikin murmushi tace amincin Allah yatabbata agareka dan autan maxa

Sosai tabashi dariya dansaida yadara yace kema aminci yatabbata agareki sarauniyar mata"" tace tofa yaukuma sarauniya nasamu yace sosai aikin koma gidan sarauta danhaka kedin sarauniyace

Tace ah ah kam kamanta bakunta nazo haryanxu inanan matsayina"" yagidan??? Yanisa gida yayi fadi sosai kamar Rabin gari

Tarausayarda idanuwanta tace bayan mom tana nan taya zaiyimaka fadi"?? Maganar kikeso kenan

Aimuddin bakece awajeba komaima fadi yakemun Deejarh na nakanga duhu ya yawaita koda kuwa ranace


Komai hasken waje banaganin komai kece pitilarda ke haskakamun gabana"" khadija tasake gyara kwanciya sosai kalaman mijinta suna isarda sakonda yakamata su Isar sunabin kowanne bango lungu dasako na zuciyarta

Tasaukarda ajiyar zuciya tace Nima hakanne hubbyna"" yagyara kwancinsa yace dagaske bayan kuma kedin kinacikin danginki anyama zakituna dani???


Wainikam zan iyah sati dayan nan bangankiba?? Wlh yanxun ma dabanajin motsinki wani iri nakeji "

Takwantarda murya karka damu nawan kaima ba anjima zakatafiba aizamudinga yin waya akai akai

Yayi shiru tace banjikace komaiba"??? Tomezance Deejarh na gaskiya zanyi hakuri nasatin nan daya dole asaka sunana cikin jarumai

Khadija tasoma dariya yace mekikewa dariya kuma??? Tace ah ah bakomai Kaine za asaka Cikin jarumai tosaika fadamun jarumtarda kayi ???

Murmushi yayi yagyara kwanciya yace jarumtar hakurin rashinki akusa danie mana kinsan bakaramin kokari zanyiba harsati daya banjini alallausar fatarkiba Haba dolema ayimun jaje bayan anbanie kyautar karramawa dajinjina

Tace hakane zakasamu shakuruminka "" Amman saikaje filin daga tukun"" yayi saurin Tatar nunfashinta yace dama ainidin jarumine nasaba zuwa yakiiii kobaki saniba


Dariya tayi tace habadai"" bakiyardaba kenan bari nafadamaki tace ah ah basaika fadaba nagane "" shima kanshi dariyar yakeyi

Yace ina yarana banji motsinsuba???

Wlh nikaina bansan inasukeba tunsanda mukashigo aka karbesu bansake ganinsuba"" dasauri yatashi zaune yace yaran nawa toke kina ina zakibarmun yara kowa yana dauka

Tace kwantar bawan Allah iyayena suka daukesu kokuma zuwa zan nakarbosu daga kawai anhutardanie

Yace hakanma zakice kinsan bazaki iyah dawainiyar suba meyasa kika tsiri tafiyar"" dariya take ciki ciki tace waikai saikace gareka farau yaya bayan kanada wasu bayansu

Yace nasanda haka Amman wadan nan namusammanne "" tace saboda???

Sunfito ta karkashin macenda nakeso fiye dakomai "" kuma jinin jikinta yagauraya da nasu kingane ai""

Tace hmm barci nakeji gashi sai hamma nake" yace badai yanzuba kyabari saidare"" tace hakane nikaina banda niyar yinsa yanzu sundan jima suna fira sannan sukai sallama taka she lambar ya muktar takirah


Aisha✍🏼
[3/30, 6:14 AM] YAYA HAYAT: ☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 118 · 0% Book details