← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 62 OF 121

Chapter 64

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Tana fitowa kana shigowa. Tace maka gidansu zataje kaikuwa kacemata bazataba takafe akan saita tafi shine kace totabaka yarka Tabaka tatafi dama shine rabuwarku ance bazaku sake Neman junaba

Nikuwa tundaga lokacin nayita ganawa fateema azaba naso tamutu harguba makociyata tabani tace nasakamata acikin abinci Amman dayake batada rabon hawala kwananta basu kareba saigashi akuyata uwar gargen da yayanta takunce daga daurinda naimata tafada madafa dayayanta sukacinye abincin alokacin tana wajen dibar ruwa

Koda tadawo saidai naji tanasalati tana kiran sunana koda nafito damasifa sainaga abunda yafaru ga dabbobina wannan shine asalin abunda yafaro ciwona domin dasu nadogara akuya bakwai duka sukai musai

Takaici yasakani nakilmawa fateema kashi nace itah tazubamasu guba dantana bakinciki da arzikina kaikuma saika yarda kasake dukanta taja majina kaji abunda yafaru tun alokacin naketa ganin i shara gashi Ya.yana sunyi aure abunda naiwa Hauwa suma anaimasu

Ninasan abunda nashukane nakegirba wlh nayi nadama Dan Allah kiyafemun fateema yarbaba tana kuka tashare hawayenta tace bakomai innah ninayafe maki duniya da lahirah

Buhari kam shiru yayi danyakasa magana saida tasake neman gafararsa yace nayafe naki sadiya bakece dalaifiba nine mailaifin tunfarko daban fifita son yarbaba akan sauran yayanaba dahakan batafaruba

Hakika nikaina na aikata babban laifi duka yayanane kowanne amanace agareni baidace kafifita danka akan wani danba koda kafisonsa aranka kadinga yin kawaici musamman idanma yaran ba uwarsu dayaba hakan zai iyah janyo rabuwar kan iyalinka kekuma dakinkirani kinyimun nasiha aibawani abubane

Amman kin aikata babban laifi wacce kika zalunta Hauwa inazakiganta kiroketa gafara kokinsan Allah baya yafe hakkin wani hakika hakkintane ke bibiyarki kamar yanda itama hakkin iyayenta yake binta

Mun aikata son zuciya munbiyewa soyayya hakan yasaka batayi rabuwar dadi da iyayentaba sunce tazaba kosu koni tazabeni rashin bin maganar iyaye shine yajawo mata haka harkuma yashafi yarta

Allah ya yafemana kura kuranmu suka amsa da amin tace malam taimako daya zakamun kaje Niger wajen danginta tayiyu takoma gidane idan kaganta kanemamun gafararta sannan kamaida matarka nasan haryanzu kanasonta ninasan ciwon nan nawa banatashi bane """

Yace nayimaki alkawari zantafi duk danasan abune mai wahala su saurareni dansuna ganin kamar nine silar rabasu dayarsu kidaina maganar mutuwa aicuta bamutuwa bace insha Allah zakisamu lafiya dakanki kinemi gafararta tace hmm kawai dan itah kawai tasan metakeji

ranar jikin kowa yayi sanyi sukuku suka wuni washe gari kodasuka farka saidai sukaga gawarta tacika cikin dare tashin hankali sunganshi bakamar garba yanaganin mahaifiyarshi tashuka abunda bazai barta kwanciyar kabariba

Sati biyu darasuwarta garba yamatsa aje Niger buhari yashirya suka dunguma hardasu hasana da Fateema"" Amman dasukaje gidansu Hauwa mahaifinta ko saurarenshi baiyiba yayimasa korar kare

Dayaki tafiya fateema kuma tahau kuka bindiga yadauko yace kosubarmasa gida koya dirkesu da bindiga dole suka futa fateema tanata waigen kakarta wacce taketa kuka" dankuwa babu abunda yaraba Hauwa da fateema

Agarin suka kwana buhari yayita tambaya koda tadawo garin akacemasa batadawoba tunda ta auri wani bahaushe tayafe gida aikowa yabargida gida yabarshi

Washe gari sukadawo Nigeria saikuma buhari yakwanta jinta danyanzu soyayyar Hauwa tadawomasa sabuwa watanshi daya shima yace ga garinku

Fateema takoma marainiya garba shike tallafe dagidan haryayi aure alokacinne Muhammad yafito daniyar auren fateema

Muhammad yanada mata daya sunanta rukayya sunyi auren saurayi da budurwa amman haryanzu bata tabayin koda batan wataba
Aurensu kuma wajen shekara takwas kuma shi yana masifar son Yaya Amman yanason matarsa hakan yasaka yakiya kara aure saigashi yakawowa wani abokinsa ziyara kano haryayi sati daya akasuwa yahaduda fateema an aiketa siyo kayan miya yabiyota haryaga gidansu kunji sanadin haduwarsu

Garba dayaji yanada mata kuma gashi zatayi nisa dasu saiyace tahakurah dashi tasamu wani itakuma tace shiitake so tarihidai yasake maimaita Kansa domin fateema takafe kaida fata saishi

Garba yanajin tausayinta dakuma halin kuncin rayuwa datashiga bayaso yatakurah mata sanin yanda soyayya take saiya amince Muhammad yaturo magabatansa akasarana suka biya sadaki suka kawo lefe akasa biki wata uku

Wata uku sunacika aka dauramasu aure matar garba balkisu macece wacce baruwanta itace komai na fateema su hassana ma suntaka rawargani sun nuna bajintarsu amatsayinsu Na antys dinta garba yahada kudinda za asiyamata kayan daki acen yola akasiya akajerah mata babu laifi sunyimata kaya kamar diyar maikudi

Ranarda za akaita har yola saida suka rakata sukaga gidan sun yaba sosai dahalin rakayya sai nan nan takedasu sunsan kanwarsu tayi dacen abokiyar zama

Saida suka kwana washe gari kuwa dazasu taso sunsha kukan rabuwa haka suka rabu suna kewar juna saidai rukayya tayita basu hakuri

Watan fateema uku saigaciki yabullu nawata uku danbata cilge wataba"" zokuga murna wajen rukayyya harma taso tafi Muhammad murna""batabarin fateema koda chokali taka war komai itah takemata hatta wankin kayanta

Saikuma dangi sukafara jefan rukayya da habaici dama anacemata juya toyanzu zance yatabbata itace juyar gashi Amarya tasamu ciki itakuma batada aiki saidai taci takasayar

Hasbinallahu wa ni imal wakil kalu innalillahi wa inna ilaihir rajiun waimenene amfanin yiwa wani gorin haihuwa???

Shinkeda kika haihu wani Abu kikayi yasaka kika haihu??? Wayonkine kokuma dabararkice??? Anasiyenta dakudi kokuma mulki zaibaki???

Itah dabata haihuba laifi tayiwa Allah ko anfada maki Allah bayasontane??? Waimeyasa mutane basuda tunani kisani duk wacce kikaiwa gorin haihuwa wlh hartamutu bazata manta dakeba kuma kema bakiwuce Allah yakarbe yayanda yabakiba sannan kidaina haihuwar aganina inhar wata acikin danginku matar yayanki ko matar babanki ko kanwarki kishiyarki inhar hakan yasameta saiki kwantarmata da hankali kice tacigaba dayin addua Allah maji rokon bawansane


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 62 · 0% Book details