← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 40 OF 121

chapter 43

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Yace Amman bakowacce mace tasan wannan ba ko??? Dankuwa dakowa yasani aida samrat kwata kwata bazatayi kishinkiba

Kodayake hali badayaba"" tamurmusa tace lokacintane taci yarintarta "" murmushi yayi yace yarinta da kishi aibazaiyiba yamike yadauko mata maganin ciwon kai yasauka kasa yahadamata tea tasha sannan yace sukoma cikin daki

Tace aikifa zakaje"" murmushi yasakar mata yace karkidamu dakinsamu barci zantafii yayi maganar yanajan hannunta suka shiga dakinta
.
Yakwantarda itah yanashafa bayanta ahankali"" cikin yan mintuna kalilan barci yashureta damakuwa barcin takeji

Bangaren samrat kuwa tanafita tayi bangarenta tanata darzar kuka"" abunda yake kasa gareta takwakwaloshi tayar tana hara rarsa tamkar shine yayimata laifi

Lallai tsuguno baikareba tana takamar tashigo gidan Usman asaukake ashebatayi komaiba yanda take tunanin yanason matarsa abunhar yazarta tunaninta

Wayarta tadauko takamo lanbar raliya tasoma kirah"" saida takatse tasake Kira sannan tadaga tafashemata da kuka

Cikin tashin hankali tace raliya inacikin matsala Dan Allah kije kifadawa mamana wlh aikin nan data bani baiyiba

Raliya tace bangane baiyiba wajenwa ta karbomaki maganin??? Tashare hawayenta tace wajen bokanta nima dai bansanshiba kuma wlh nayi duk yanda tace

Raliya tanisa tace tomenene nakuka kuma?? Kodai kinyi halin nakine nasanki dashegen kishin tsiya

Tashare majina tace haba raliya kinsan meyamun kuwa???? Tace inakuwa zansani basaikin fadamunba "" anan takwashe komai tasanarda itah

Tace haba aiko zuciyar dutsece dani dole inji haushi agabanafa yahau tsutsar bakinta kamar yasamu mintiii

Raliya tafashe da dariya hartana rike ciki abun yatunzurah samrat saitasake fashewa dakuka tace yanzun sakayyar dazakimun kenan duk irin abunda naimaki nikuma infadi bukatata kihauni da dariyar mahaukata bakomai nagode sai anjima

Tace please karki katse wlh badariyar mugunta nakemakiba ina mamakine kisamu mace damijinta harda yaranta Amman kifita kishi

Tace to aikishi halittace kikasani ko itah ba ahalicceta dakishinba""" tayi maganar tana harare harare kamar raliyar tanakusa da itah

Raliya tace kowacce mace dakikagani tanada kishi akan abunda take so damadai batasonshine zakifadi hakan
.
Amman kinsan tanasonsa tundahar tahaihu dashi kawaidai kishin watane yafinawata kuma bawai finshi yayibaa kawaidai akwai masu boyenasune

Wannan shine babbar matsalata dake rashin boye kishinki menene yakashe maki aure dafari bawannan mahaukacin kishin nakiba

Kisani komai maganinda kikeyi"" muddin kinada kishi sosai maganinki bazaiciba"" kishi yanarage karfin soyayya azuciyar miji

Bawaikuma kinuna bakya kishinba yasan kinayi Amman saikidanne kiga yanda matarsa tayi kincefa tana asiviti akayi aurenku Amman datadawo maimakon tatada fitina saimatace tayafemaku kwananta

Tabaku harsati biyu kusha amarci atunaninki tagaji damijinne??? Kodaya kawaidai tasan komai narayuwar tafiyada danamiji

Anan zandanyi magana akan mata masu shegen kishin tsiya watakishin nata kamar badiyar musulmaiba

Kisani kishi mafarin sakine domin duk macenda tafaye kishi dawuya kaga aurenta yarane ba asaketaba "" nikaina matanda nasan ansaka gameda mugun kishi bansan iyakarsuba

To kintada bakin kishinki adole kekawai zakizauna damiji kuma anfisamun haka awajen uwargida tunkinayi mijin yana lallabaki karshema yabuge iskanki
Ninasan wata wlh tanatare damijinta baida arxiki sunatare haryayi kudii lookacinda yadace tazauna taci arziki akan yakara aure kishi yaturata tahau bala I taki kwantarda hankalinta

Tundayayi aure baida kwanciyar hankali kullum cikin fadatake da amaryar tunyana lallashiñtà haryagaji yagano itace batason za man lafiya

Zancenda nakemaku yanzu wlh yasaketa saki daidai har uku dadaya daya akafara koda yasaketan takoma gida idan aka sulhunta tadawo maimakon tagyara hali saitadorah daga inda akatsaya

Abunda saki yakenuni jankunne ne idan anyimaki daya saikiyi hankali Amman ayimaki harbiyu sai ancike sannan kidora hannu aka🙆🏿 kice nabani Na lalace

Shin mezaisa kafin hakan tafaru kiyiwa kanki karatun tanatsu??? Ni mata kunabani mamaki dayawa sunsanifà Amman basa aiki dasanin saisuyi aiki dazuciya kusani duk wacce take aikida zuciya lallai zatakaita gahalaka imma mata imma mazà domin zuciya abokiyar shaidance bayada wajen zama facekusa da itah domin abukadan zairayamata yikaxa yikaxa

Kuma kunsan shaidan baya sanyawa ayi alkhairi saidai akasin hakan idankuwà haryasakà kayi toyanada manufaryin hakan zai darsamaka abun azuciyarka dukdanfa kakauce hanya

Ya Allah kakaremu damuda zuriarmu dagafadawa tarkon shaidàn kahana kunnuwanmu jinsautin kidansa Allah kakaremanà zukatanmu da imaniñmu Ameen


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 40 · 0% Book details