← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 75 OF 121

Chapter 77

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Anason mace mai kunya hausawa sunacewa kunya adon yammata"" mace ballagaza itace batada kunya

Nidai shawarda zanbaki Yar uwa inhar mijinki yazama irin haka kokuma akasin hakan kisamu kuwarware matsalarku atsakaninku batareda kunyiwa juna tonon asiriba

Danwannan babu abunda yafishi zama tonon asiri "" shinwaima idan kinfadawa wata tanada maganinda. Zatabakine ??? Ninasan babu abunda zatacemaki saidai tace kiyi hakuri shine kawai

Shawarda zanbayar itace idan mijinki yakasance kinkasa biyamasa bukatarsa ta auratayya tokirika hadamasa da dubaru wadanda kikasan basu sabawa addiniba zaki iyah yin koma mene danyasamu gamsuwa ajikinki saidai banda waje daya Wanda Allah yamana iyaka dashi wato bayagamutum

Koya mijinki yakai kolokuwar bukata inhar yanuna maki yinhakan karkiyarda Amman bayan nan ko inane halal ne "" idankuma bukatarsa tawuce duk wata dabara dazaki masa tokibarsa yayi aure

Karkuma kitada hankalinki idan kikaga ya auro wacce take iyah hakuri da bukatarsa"" karkiga laifinsa bashine yayi kansaba haka Allah yagadamar yinsa saiki tausaya masa

Idankuma baida halin auren Yar uwa inkinada hali kibashi kudi yayi bawai faduwa kikaiba sakamakon aikinki yana wajen Allah" idankuma bakida hali kema tosaiki bashi shawara yarika hadawa da azzumie domin kare kansa daga fadawa ga aikata zina
Manzon Allah yanacewa awani hadishi dayake kwadai tarwa akan aure"

وقال صلى الله ءليه وسلم يا معشر الشباب من استطاع منكم الباءة فليتزوج فإنه أغض للبصر وأحصن للفدرخ ومن لم يستطع فعليه بالصوم فإنه وجاء رواه البخاري ومسلم
manzon Allah tsira da amincin Allah sutabbata agareshi yanacewa yaku taron samari masu iko daga cikinku tosuyi aure ma ana wadanda sukeda kudin auren kuma sunkai munzalin yin auren sunada bukatar mata "" cewashi aure yanakarewa daga ganie dakuma sha awa
" Wanda kuma bashida iko ma ana baida halinyin auren kokuma idan yayi auren bazai iyah daukar dukkanin hakkin matarba sai manzon Allah yace nahoreshi dayayi azumie sabodashi kariyace

Wannan hadishin basamariba harmai mata zai iyah aikidashi inhar yaga yakusa fadawa ga aikata zina

Yar uwa saikibashi shawara yafara azumie kema zaki iyah tayashi kinga yasamu ladabiyu galadar azumie kuma galadar kiyaye kansa dadi biyu kenan

Idankuma kece dayawan bukata shikuma bayada shima zai iyah wasadake danyaragemaki kamardai shidin saikuma kikara da hakuri idankuma kinji bazaki iyaba zaikaiki ga hakala saikisameshi kuzauna kifadamasa karkiboye komai

Tsakaninku kuwarware matsalarku idan baida lafiyane saiyanemi maganie idankuma haka Allah yayishi saiya sauwake maki kisamu daidaike kuyi rabuwar mutunci Amman gaskiya indai harzaki iyah hakuri tohakurin zaifi zakici ribarsa agobe kiyama Allah yasa mudace

Lubabatu tace wlh bayabon kaiba nikaina idan naji masu sakin baki sunafadawa wasu matan sirrin gidajensu haushi sukeban saikuma kaga wadanda sukafisu wayo subasa fadar nasu saidai su saurari naka

Usman yace aishine rashin hankalin nagode Allah da matata batacikin ire iren wadan nan matan"" nikuwa nace Allah yasa masu karatun wannan labarin basacikin wadan nan matan

Idankuma kinayi tokinji dagayau saikigyara rawarki kisauya taku wadanda kuma basuyi aurenba sukiyaye dangaba yayimasu amfanie

Zaki iyah turawa wata domin takaru kema kin isarda sako Allah yasa muzama masu rike sirrinmu Ameen

Lubabatu tamatsu tabar dakin danfayau tashiga rudanie

Tayakuna fuska nidai zankwanta kakula dakanka""" yace shikenan Allah yasauwake konazo natayaki barcin???

Tayi saurin cewa ah ah nagode nahutardakai saida safe tayi maganar tana bude kofa"" yace tosaida safe tafita taturo kofa"" wai wata sabuwa lubabatu harda gudu gudu take hadawa jitakeyi kamarma tazama iska takai kanta wajen *hatsabibin boka* tanashiga dakinta sauran kadan tafadi garin mugun saurinta""
Takulle kofa tafada dakinta wajen drawer tadauko akwatin tabude tafitoda karamin madubin sai walwalniya yakeyi tashafa cikinsa jikinta yana rawa tareda kiran sunan *hatsabibin boka* muryanta tanarawa kamar maikuka

Daka ganta kasan tanacikin tashin hankali shafawarta keda wuya saiga wani duhu gabadaya ya mamaye dakin abunda bata saba ganiba gabadaya dakin yayi baki kirin wutar dakin tadauke bataganin kotafin hannunta

Wani tashin hankali tasake shiga al amarinda yasoma saukarmata da faduwar gaba lallai wanann matar kilanta wajen boka takaishi shine abunda lubabatu tasoma rayawa aranta

Batagama tunaniba haske yasoma samuwa acikin dakin sannu ahankali haryagama mamaye dakin saiga *hatsabibin boka* yabayyana asaman tsafaffen zakie ido hudu kawai lubabatu tayi dazakin tasaki fitsari daga zaune ganinhakan yasaka *hatsabibin boka* yatintsire da dariya kamar bazai dainaba

Zuwa dakiku ashirin yatsuke fuskarsa tamkar Wanda baitaba dariyaba saiga idanuwansa masu munin gaske sunkoma koraye shar yasoma wani irin hucii kamar mesa hucinsa haryana fesowa lubabatu

Cikin tashin hankali tace yakai wannan hatsabibin matsafi kasani yauban kirakaba saida mummunan labari saiga hawaye sharrr akan kumatunta suna zarya

Tacigaba waini Usman zai ha inta??? Haryatashi aure baisanarda niba??? Sai anasaurah kwana biyar waiyama akai aikinda kaimasa baikama wannan shegiyar yarinyar ba

Haryanxu bokan kallonta kawai yakeyi baice uffanba saida takai karshen maganarta sannan yabushe da dariya yace wannan ranar batada sa a gareki

Tunkafin kisanardani gabadaya aljanuna sunce bazasu iyah jayayya dawan nan yarinyarba sanadinda yasaka kikaga batakishiba aljaninda yake yin wannan aikin yakasa shiga jikinta

Hasalima yanzun yanacen yanajinya sanadin rauninda yasameshi dayaso rike hannunta"" kozaisamu kafar shiga jikinta

Cikin rudani lubabatu tace nashiga uku boka wannan kuma wace irin hatsabibiyar yarinyace???

Wajen wane irin boka takaini Wanda yakeyiñ aikinda yagagari aljanunka su shafeta???

*hatsabibin boka* yasake kecewa da dariya yace nikaina yau banacikin yanayi maidadi lokacinda kika kiranie ina karkashin kurkukuna dayake kasan kasa"" ina ganawa wata aljana azaba!!!

Cikin lubabatu yaduri ruwa kamar tazunduma dagudu yacigaba kirankine yasaka nahau dokina nazo gareki kisani wanann yarinyar tasha banban da irin matanda mijinki yake soyayya dasu

Wannan takere duk wani tunaninki saboda hafizace kuma tanada yawan ibada narantsemaki da karfin tsafina dana gadà kaka da kakaññi babu wani aljani aduniya daya isah yatunkareta haryashiga jikinta batareda yakone kurmus ba yamutu

Kebarta mutuwama ko tokarsa ba azasamuba!!! Take lubabatu tasoma yarfe zufa tace togaskiya banaso ya auri wannan yarinyar danmuddin tashigo gidana zatayi wuyar fita "" kaiyagirgiza yace babu makawa saiya aureta!!!

Saidai kiyi hakuri idan akai auren kisake kirana kafin lokacin ninasan hanyarda zanbi domin mukasheta danwanann muddin tana raye tosaitaga karshenki

Lubabatu tadafe kirji tace wlh saidai naga karshenta Dan ubanta tafashe dakuka"" yanzun dole saitashigo gidan???

Yace tabbas kimadaina barnar hawayenki babu abunda zai gagari *hatsabibin boka* idankuwa har akwai wani aiki dazai gagareni tonikuwa banchan chanchi akirani *hatsabibin boka* ba

Kikwantarda hankalinki kamar tsumma aranda"😆😆😆" tace wane irin kwanciyar hankali zanyi bayan anashirin kawomun annoba!!

Waikunjitafa🙄 wai annoba! Bayankuma itace annobar😕


Masu karatu kuyi hakuri da iyah abunda kukesamu baidace kuna rainawaba inama laifina inayin wannan kullum karfa kumanta inada aikinyi bawai zaman remote nakeyiba kurika hakuri daduk abunda kukasamu kunsan typing dinnan kansa wuyane dashiii bawai yawan typing ba Allah yasa kuna amfani da abunda kuke karantawa

Idankuma kawai dannishadinku kuke karantawa babu amfanin inrika bata lokacina😒


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!!*☠
Chapter 75 · 0% Book details