← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 109 OF 121

Chapter 008

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Tanaji aranta inama Usman natane itakadai"" sundade suna faranta ran junansu sannan suka sake komawa barci

Wainikuwa nace Usman yamanta da lubabatu ne??? Hakanne kuwa wlh Sam yamanta da itah yadauka wata duniyar suke daban""

Zuwa kamar karfe takwas darabi khadija tafarka ahankali tajaye jikinta dagajikin Usman taturah masa filo ganin zaisake rungumeta

Tasauko ahankali takoma daya dakin tayi wanka kaya maras nauyi tasaka tasa karamin hijab tasauko kasan bakowa hanyar kitchen tanufa tasamu kukunda yake dafa abinci yazo yana jiran lubabatu tasanar dashi abunda za agirka

Saiyaga bakuwar fuska"" tashigo takalleshi tace morning"" yace morning Anty"" batareda tasake kallonsaba tasoma hada kayan da zatagirka abinci

Ganin hakan yamata magana anty me za ayi yau" tadan yatsina fuska tace katafi kawai idan mom tanada bukatarka Zata nemeka yace okay yasakai yafita abunshi

Khadija tasoma fire doya tadora awuta sannan tahau gyaran kayan ciki"" tacire anta daban tayankata kana na2" tadora tafasarta daban " tasamata magi da gishiri bamasu yawaba

Lubabatu tanacen dakinta tunjiya dadare taketa Shafa madubin tsafinta Amman shiru babu bayanie karshe madubin yana hannunta tana kuka barci yadauketa"" garin barci tasaki Dan madubin yafado kasa yawatse""

Batasan yafadiba sai kwasar barcinta takeyi abunta"" khadija kuwa doyar tanayin taushi tasaukar da itah"" tareda antar tayi lubus"" kwai tafasa tanika tattasai da tarugu kadan ta zuba ciki sannan taxuba antar aciki""takara murzashi yadargaje tasaka kayan dandano"" sannan tadorah ferfesun kayan cikin tadan matsamasu lemun tsami kadan tazuba ruwa dakayan miya batasa kayan kamshiba tamiyar tarufe

Tadorah tasar tuya tazuba mai"" dayayi zafi tarika tsoma doyar acikin ruwan kwan masu anta saita jujuyashi sannan tadibo daruwan kwan da hantar tazuba acikin tallen haka tayi hattallen yacika dayasoyu tajuya

Tuni kamshi yasoma gauraye gidan"" kayan cikin bayan sun taso sau biyu sannan tazuba kayan dandano Dana kamshi""

Usman yasake juyi yasake makale filo saiyaji yalotsa ahankali yasoma lalubar filon yatabbatar shidinne yadaukeshi yawurgar yasoma lalubar khadija baijitaba zunbur yatashi zaune yasoma saurare kotana toilet ne kuma baiji saukar ruwaba mikewa yayi yawatsa ruwa

3quarter baki yasaka dakaramar Riga ja mai karamin hannu"" yataje sumar kansa yafesa turare sannan yafito sauran dakunan yasoma lekawa ganin haryanzu bata dawoba Amman bataciki""

Sauka yayi kasa tunkafin yakai yasoma shakar kwamshin girki yalumshe idonsa"" Sam baiyima tunanin agidansa kamshin yake tashiba" yasauko falon baigantaba"" sai ya tunkari kitchen din"" bakin kofar yatsaya yajingina jikin kofar yarungume hannuwa yana kallonta Batasan da zuwansaba saida kamshin turarensaa yadaki hancinta

Tajuyo ido tadan turo tace badai harka tashiba"" ??? Harararta yayi cikin wasa yace aidole kice hakan""kintaso bada izininaba shine harda turamun filo ko anfadamaki jikinki daidai yake dafilo"" tace todakumafa??? Yace aijikinki yafishi taushi

Dariya tayi tajuya tana motsa ferfesun tace sorry hubbyna banaso katashine bangamaba"" takowa yayi zuwa indatake yadorah kansa akan wuyanta yashaki kamshin jikinta yalumshe ido yace kimmanta yau weakened ne bazanje ko inaba"" kodama ba weakened bane banajin zan iyah fita nabarki hutuma zanyi konasati biyune inmaida jikina

Dariya khadija tasamasa tace waikana nufin karame?? Ganin nawa zaisaka kamaida jikinka" murmushi yayi maidan sautiii yace sosaima kuwa aikinsan mutum yanacin abubuwan Gina jiki masudauke da vitamins calcium tyrosine dasauran abubuwanda suke gina jiki Toni kodanacisu abanzane danbasuda sinadarin

Kece kawai kikeda sinadarinda duka kayan marmari basudashi danni banga amfaninsu ajikinaba

Khadija tace kadai fada"" yace kuma dole ayardaba kusan taresuka sa dariya" tace kaganie kanaxuwa nasoma shiriricewa

Yace bakuma zantafiba saidai mukwana anan munayi nimafa na iyah girkin nan bari kiganie "" tace kabarshi karka bata jikinka yace aiga kayan aikinan baki sakaba kema yajawo wata drawer saiga rigunan dayawa wasuma cikin ledarsu ba ataba sakawaba"" yadauko biyu yacirosu aledar yasaka daya

Itama yadauramata tanacewa dama kabarshi nida nakusan gamawa"" yaharareta yace munkusan gamawa dai ina taremukai girkin nan

Tace hakane kam munkusa gamawa da surutunka ba yayi dariya yace aiyau zakuci abinci maidadi tunda nasaka hannuna"" baridai inhadamana tea dannaga bakiyiba"" yayi maganar yana kunna wani gas yawanko tukunya yadorah yazuba kayan yaji daruwa da Lipton yarufe tana gefe tana kallonsa

Yajuyo yakalleta yadaga mata girah yadai kallo haka waikindauka nidin ban iyah komaiba babu abunda mace zata nunamun sai Abu daya"" yayi maganar yana dariya kasa kasa tasan abunda yake nufi dariyar itama tayi tace aiho ashedai akwai abunda zamu nuna maka dasauki to

Yace hakane kam bazanyi jayayya ananba" yace wainikuwa ina kukun gidan nan dakika shigo kitchen bakiga yanda momyn Abdul takeyiba""

Tace naganie tomenene ranar hannuwana idan nakasa dafawa mijina abunda zaici banason kanacin abincin kukun nan dakaina zandinga yimaka """

Kallonta yake yanasakin murmushi karasawa yayi wajenta dasauri yarike kugunta yadagata yana juyi da itah yasakar mata kiss yace ashedai nidin dan lelene bansaniba Amman naji dadi sosai shiyasa nake kara sonki

Dariya tasomayimasa shima dariya yake lubabatu wacce tunda tafarka tsarabar kamshi yadaki hancinta tataso afusace dantadauka kukune yadorah abincin kuma tafadamasa karya sake yadorah girki inba ita tace ga abunda takesoba

Tana kawowa kafarta taji talake ganin Usman dinta yana juyi da khadija acikin kitchen suna dariya wasu hawayene masu zafi suka saukomata gashi jiya tasha kuka fuskarta duk ta kunburah nikam nace yi aniyar hawayenki sukare

Ganin kamar zasu juyo taja kafarta dakyar takoma falon tazauna tadafe kantaa"" tanajiyo dariyarsu harcikin ranta""ga takaichin madubin ta yafashe gakuma takaichin Usman da Khadija dayarufeta harsuka gama girkin suka zuba komai acikin kula sukadauko sunafirah ta soyayya suka jerah saman dinner Sam basu gama lubabatu ba khadija tagyara kitchen din Usman yana gogewa

Kitchen din yayi tsaf kamar ba ayi aiki acikinsaba"" sukacire rigunan suka fito yana rike dahannunta harzasu wuce yaga lubabatu zaune tadafe kai hannun khadija yasaki yace yasalam meyake damunki yayi maganar yana zama kusa da itah yadago fuskarta ganin yanda takumbure

Yace meyasamu idonki haka lubcy"??? Murmushin yake tayi tace bakomai kainane yakeyimun ciwo tunjiya" Usman yace haba lubcy shine bakisanar daniba

Tasake murmusawa tace bakomai naga kanatareda Amarya kuma kundade Baku haduba banaso nakatsemaku jindadinku""

Yayi murmushi Allah sarki matata shiyasa nake kara sonki yayi maganar yana janta jikinsa "" khadija juyarda kanta tayi gefe saboda takaici Usman yalurah dahakan yamike yace bari muyi wanka kema kishirya sainakaiki asiviti

Tace ah ah dama kabarshi yace kinsanfa banason musu kitashi tace to yajuya wajen khadija yanayin yanda tajuya kanta yabashi dariya saidai bayaso yadara yasakata kuka

Hannunta yariko yace mujeko harararsa tayi tawuce yabita dasauri taruga tana dariya yana cinmata yadauketa yahau mataka zuwa bangarenshi

Lubabatu tabisu dakallo jitakeyi kamar taje tarufesu da duka"" saida suka dade dawucewa sannan tamike tahau saman tayi wanka tashiryo hartadawo dasu fitoba tazauna jiransu gashi tanajin yunwa

Ajima a jima saitakalli hanyarda zasufito tajatsakie tanajiyo dariyarsu asaman"" takai akalla mintuna goma zaune sannan suka sauko shigar shadda sukayi iri daya tunna aurensu

Itama lubabatu shaddace Amman ba irinsu dayaba khadija rigarta doguwace anfitarmata da shefdin jikinta tamkar ajikinta aka kero rigar""

Suna zuba kamshi khadija tace mom sorry mundan Dade gashi bakida lafiya"" tayi yake bakomai khadija tayi maganar tana mikewa suka karasa saman dinner khadija tazuba kowa nashi itakam da Usman tahade nasu

Sukasoma ci babu Wanda yasake magana harsuka gama khadija takwashe kayan "" yace tadauko mayafinta tarakasu

Tace ah ah katafi nizanyi aikine"" yace tarezamu dake kibari idan mukadawo natayaki aikin"" batasom sutsaya musu tajuya tahau saman

Lubabatu tace meyasa kakesoñ tilas tamata abunda batayi niyaba"" yamatso kusa da itàa yace lubabatu bakisan yanda nakejinta ajikinaba banajin dadi idan banajinta kusadanie

Lubabatu tarufe idonta tabude saboda radadin maganarsa tayi danasanin tambayarsa"" shikuwa Usman baidauka wai zataji haushiba

Shikam iyakar gaskiyarsa yadauka bataji komaiba har khadija tafito lubabatu tayi gaba shikuma yatsaya kallon khadija tare suka jerah koda suka kai yabude kofar gaba lubabatu tace khadija tazauna itah tazauna baya

Khadija tace ah ah mom bayan nakeso kafin lubabatu tasake yin magana har khadija tabude baya tashigà


Aisha✍🏼
[3/26, 8:34 PM] Nabila Elharun Q: ☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 109 · 0% Book details