← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 51 OF 121

Chapter 54

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Akasoma kiran masu harda" tundaga mataki nafarko masu hizifi biyar har akakai kan masu hizifii arba in labila Usman itace wacce akasoma kirah

Usman saiyanzu hankalinsa yadawo jikinsa jin ankirah gudan jininsa yasoma dube dube yaga ta inda zata bullo

Idanuwansa sundauke daga gunda labilar take tacewa sahiba kitayani addua please tana dariya tace kije kawai zakiyi nasara insha Allah"" labila tawuce cikin takunta ahankali saidai yaji tasoma kira a

Sosai yanatsu yana sauraren yarsa harta kammala akasomayi mata tambayoyi akan fikihu da kawa idi wasu hawayen dadine suka sauko akan idanuwansa yakaikaice yashafe yanamai sake godewa Allah daya nuna masa wannan ranar""

Bayan tagama akacigaba dakiran sauran har aka kai matakin hardar hizifi sittin akasoma kiransu dai bayan daya" karshe akakirah amerah wato khadija Muhammad tanacikin masu hardar hizifi sittin tunkafin tasoma karatu gabadaya wajen yakaure da kabbara!!

tasoma karatun fatiha acikin daddan sautiii maimatukar sanyi dakuma kashe jiki""tana kammalawa tasoma karanto suratul bakarah gabadaya wajen yayi tsit Usman sai lunshe idonsa yakeyi saboda dadin karatun kowanne harafi tanabasa hakkinsa wajen gunna tafitarda gunna kowanne harafi tana fadinsa daidai"" harwata kasala tasaukar masa""

Yayi nisa wajen tunani hartagama akasoma yimata tambayoyi tana bada amsa daidai bayan takammala takoma mazauninta""

Gabadaya wajen akasake kaurewa da kabbara kowayasaurari karatun khadija dole yayi kwadayin inama ace yarsace wannan kokuma yayi kwadayin yasamu mata kamarta

Usman yanadai dagacikin wadanda suka furta hakan azuciyarsu"" bayan ankammala akasoma rarraba kyauta dagukkan dalibai"" inda abangaren masu hardar hizifi sittin khadijace tazo tadaya tasamu kyauta maitarin yawa ciki kuwa harda kujerar makka"" sosai taburge kowa tayanda akabata kyautarta "" saitasoma kuka domin tunawa da mahaifiyarta inama tana raye taga yanda abunda tabari aduniya tazama

Labilace tafito tajata zuwa wani aji tasoma rarrashinta tace haba sahiba wannan fa ranar farincikice menene abun kuka kuma keda zakinuna farincikinki cikin kuka tace sahiba mamana!!

Labila tace Dan Allah kidaina kuka abun alfarine awajen mama ayaudin nan idan akanuna mata yanda kikazama bakuka zakiyiba sukarungume juna suna kuka saikuma akarasa Wanda zai rarrashi wani sunyi akalla mintuna ashirin awajen Amman basudako alamar daina kukan

Yana tsaye yana kallonsu yarungume hannuwa saidai sukaji muryarsa yace kukan ya isah haka shima yana goge guntun hawayenda suka saukomasa

kusan tare suka juya suna kallon kofa labila cikin muryar kuka tace kaiwaye???
Khadija takalleta cikin fara a tace sahiba Yayana nefa" ya muktar

Bakitarike tareda murmushi""tace afuwan yayanmu tamaida kallonta wajen khadija tace Amman bakifadamun yazoba ai"""

Takalleta tace nikaina bansan yazoba danmunyi waya jiya dashi dayakirah kawu cewa yayi baxaisamu zuwaba""

Takarasa wajensa cikin jindadi tafada jikinsa saikuma tasake fashewa dakuka""daya hannunsa yasaka yana bubbugar bayanta cikin tausayawa yana rarrashinta yace menene nakukan bagashi nazoba ???

Idankuma bazaki dainaba zantafi abuna baxansake zuwaba kinkuwa San aikinda yake gabana Amman nabarshi saboda kawai inga farincikinki"" tace nadaina Yayana karkatafi kabarni

Labila tayi tsuru tana kallonsu cikin soda Kauna murmushine kwance akan fuskarta sunbala in matukar burgeta
Sunanta taji anakirah aharabar waje khadija muhammad labila usman Hafsat m shareef "" yayi saurin jayeta daga jikinsa yace kije anakirah"" hawayenta takarasa sharewa tajuya wajen labila tareda murmushi tace mujeko sahiba

Murmushi itama tamiyar mata tariko hannunta sukafita muktar yabisu da kallo sosai yanason kanwarsa dama wannan itace sahibar tata tanayawan bashi labarinta duk da baiga fuskartaba yanaji ajikinsa kyakkyawace

Sunafita wajen yasake kaurewa da kabbara"" tare suka karasa wajenda aka kiraasu khadija takarbi lasifika tasoma yin addua sannan tasoma jawabin muhimmancin ilimin Islam cikin harshen larabci inda labila take fassarawa cikin harshen Hausa"" hafsat takeyi cikin harshen turanci daki daki sukebin komai

Hakika nayarda
Ilimi wani abune maidadi hakazalika maisanya nishadi azuciya"ilimi gishirine narayuwa"dukkan Wanda yakeda ilimin Islam bazaitaba tabewaba duniya da lahirah Allah yabamu ilimi mai amfani

Bayan sunkammala khadija tayi Yar takaitacciyar nasiha gameda muhimmancin bin iyaye cikin harshen Hausa wadansu sunyi mamakin jinyanda take magana dahausa Dan Sam basuyi tsammanin tanajin hausaba

Birrul walidaini"" wato biyayya ga iyaye "" Yakamata yan uwa musan mahimmancin iyaye arayuwarmu musaman uwa!! uwa!! uwa!!!

Kasani komai kazama aduniya karkasake kawulakanta iyayenka babban abunda yake damun al ummarmu ayanzu dayawa mutane basusan darajar iyayensuba

Baka daraja iyayenkaba toballantana kuma iyayen wani"" shinkokasan dukkan cigaba yana samuwane idan harkabi Allah da manzonsa sannan kuma kabi iyayenka""

wasu yayan babu ruwansu sudai kawai suyi abunda yake gabansu karkumanta wahalarda uwa takesha tunsanda kake cikinta ranarda zata haifeka wahala cikin wahala harkazo duniya tayi dawainiyar shayardakai sukabaka ilimi Amman dagakarshe saikayi tamkar bakasan dawainiyarda sukai dakaiba"" shinkayiwa kanka adalci kuwa??? Kokadauka basuda hakki akankane??? Kamar yanda akace matarka aljannarta tana karkashin kafarka haka kaima taka tana karkashin ta iyayenka inhar kasaba musu bazaka shiga aljannaba.

Sukuma iyaye Susan tarbiyarda zasu baiwa yayansu domin suyi alfahari dasu"" abun alfaharinkane kaji ance wannan Wanda yacinye gasar musabaka aidan wanene bazakaso kaji ance ankama danka yana kanta daureba kokaji ance aidanka babban danfashine
Ku kyautata atsakanin Yaya yenku

Manzon Allah yanacewa awani hadisi""
وقال صلی الله ءليه وسلم ساووا بين أولادكم kusasanta "atsakanin yayanku a

Awani hadisi manzon Allah yabacewa وقال صلى الله ءليه وسلم إن من حق الولد ءلى والده أن يعلمه الكتا به و أن يحسن اسمه و أن يزوجه إذا بلغ رواه النجار

Yanadaga hakkinda yarataya akan iyaye bisaga yayansu ya karantardashi littafinshi ma ana alqur ani maigirma "" kokai zaka karantardashi kokuma kakaishi islamiyaya la ba asan"" '' ka kyautata sunansa"" sannan ka aurardashi idan yabalaga""


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 51 · 0% Book details