← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 121 OF 121

Chapter 020

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Khadija tasaki murmushi tace naji kitashi yanzun kikarya saikisha maganin kokinaso idan yadawo yasamu bakishaba yayi fushi dake


Tayi saurin girgiza kanta tace ah ah banaso wlh anty"" khadija tace yauwa kokefa tashi maza kikarya

Mikewa tayi Amman haryanzu batayarda ta aje wayartaba"" khadija kwanciya tayi akan gadon daidai kiran Usman yana shigowa

Cikin fara a tadauka "" tareda sallama daya bangaren aka amsa"" khadija tace tunjiya naso kiranka wlh wayar tana hannuna barci yadaukeni

Yayi dariya aishine dalilin dayasa bankiraba tunda naji kince barci kikeji"" tagyara kwanciyarta ya America din??

Yace ba dadi"" taturo ido saboda me kace babu dadi?? Danbakya kusa danie "" dariya khadija tayi Cikin jindadi tace bakada magana kullum sai wannan kamar gobenefa sati daya bagashi yanzun anyi kwana dayaba??

Yace saboda abun yadameni ai shiyasa banda magana sai itah" Amman naga alama kedin bakidamuba kinsan Allah sauri zanyi ingama komai nanda kwana uku zandawo kema kigaggauta kidawo

Tace un um""tana daga kafada yace please Deejarh na "" kinsan halin mijin naki tausayamun zakiyi "" tace mubar zancen nan

Tunda bakyaso anbarshi ina manyan gobe??? Tanisa suna wajen hajiya suna wasa nikuma inadaki kwance" toyar laushi koyarana saisunyi kewarki suma dasuke taredake

Zainab tea ne ahannunta Amman khadija take kallo yanda take firarta da alamu tanacikin jindadi wani ciwo taji yanacin zuciyarta

Waimeyasa haka dama akansamu Kanwa taso yayanta??? Kuma soyayya ta aure??? Kullum saitayiwa kanta irin wannan tambayar saidai batada amsa zuciyarta batayimata adalciba

Batason kowane danamiji aduniya inba yayantaba Wanda suke uwa daya uba daya"" tasan haukace takeyi danhar abada bazata taba samunsaba

Wasu hawaye masu zafine suka saukomata"" tayi saurin gogewa dankar khadija taganie Batasan tana kallontaba saida sukagama wayar tace yadai Zainab ko jikinne??/

Kaitagirgiza mata tacigaba da kurban tea kamar maishan madaci bayan tagama tasha maganie takwanta suna firah jefi Jefi harbarci yashureta"" tana rungume dawayarta

Khadija tagyaramata kwanciya tamike takoma wajen hajiya su sapna ma sunyi barci batajima da zamaba kaleed yashigo anwar yana hannunsa yana barci

Yayi sallama suka amsamasa yaduka ya ajeshi kusa da su sapna yayi hanyar bangarensu zainab""

Yasameta tana barcinta fuskarta sake murmushi yasaki yakaramata iskan ac sannan yafito"" yace mom zanwuce idan zainab tatashi kice tasha maganinta dazun danashigo nasamu tana barci yanzun ma haka banaso natasheta

Tace sultan zokazauna magana zamuyi dakai"" yace to sannan yadawo yazauna "" tana kallonsa tace tambayarka zanyi

Yana murmushi yace to mom tambayar saidakikasa nazauna"" tace saboda maganar tanada mahimmanci"" yace hakane saiyasake tankwashe kafarsa yana fuskantarta"" Tanisa akan maganar kanwarkace zainab"" gabansa yaji yabada rasss yakalleta jiki sanyaye yace mekuma yasameta???

Tace bakomai matsalarku dakai da itah tazo karshe"" dariya yayi har hakoransa sukabayyana yace mom bamudawata matsala dake da dad kunkasa ganewa

Nidai abar maganar nan yayi maganar yana yunkurawa zaitashi khadija tace kaleed kasan wannan pic Usman takamo awayarta Tamika masa"" yakurawa pic din ido kamarshi ammankuma bashida wadan nan kayan hasalima shidin ba ma aboci saka manyan kayabane Yakoma yazauna yanakallonta yana kallon pic din yace mom kalli wannan kiga kamarni sak kodai mubiyu kika haifa???
Kai ta girgiza tace kaleed"" dasauri yadago yakalleta dantunda yake da itah bata taba kiran sunansaba"" talura da mamaki yakamashi

Tace kanatsu kasaurareni yauzan sanardakai abunda bakasaniba "" zanfadamaka abunda mukadade muna boyemaka tsayon shekara ashirin da uku"" dam gabansa yayanke yafadi karfa mafarkin da yadade yanayi shine zaifaru dagaske??

Ta katsemasa tunaninsa dacewa magana tagaskiya bamune muka haifekaba?? Zunbur yamike jikinsa yasoma rawa yace wannan mafarkine bagaskiya bane meyasa nakeyawan yin irin wannan mafarkin Dan Allah mom kidaina fadarhaka

Tadago takalleshi tasake kiran sunansa akaro nabiyu yanakallonta idanuwansa harsun kada sunyi jajir tace ba mafarki kakeyiba"" wannan maganar gaskiyace kazauna kaji mezanfada maka

Jiki bakwari Yakoma yazauna tayidan jim sannan tace sanda mukai aure tareda mahaifinku muna son junanmu sosai duk da auren hadine munkwashe shekara uku muna tare bantabayin ko batan wataba abun yadameni sosai kullum sai inyita kuka nikadai tun inayi abayansa harnakai nakanyi agabansa ya shiga damuwa sosai watarana dadare muna kwance saimukaji ana bugamana kofa

Mahaifinku yamike yafita yanacewa waye akai shiru kuma baiga kowaba ta gefen kofa yaleka"" saikawai yaga guguwa tatashi sama zuwa yan mintuna yaga tabace harzai koma wata zuciya tace yabude kofardai yaganie

Yana budewa saiyaga wani yaro kwance shekarunsa bazasu haurah shida ba"" dakayansa agefensa saikuma farar takarda asaman kayan

Hassan yaduba gabas dayamma baiga kowaba yakarasa yadauki takardar abunda akasa aciki wannan yaron sunansa kaleed gashinan nabaku kurikeshi yazama danku watarana gaskiya zata bayyana

Yaninke takarda yaduka yadaukeshi tareda kayanshi lokacinda yafito nikuma danaga yajima sainabiyo sahunsa"" sainaganshi dayaro

Cikin kaduwa nace wannan kumadaga ina? Ina kasameshi??? Baicemun komaiba yawuce daki nabishi guiwa sake"" yashinfideshi nikuma inabinsa dakallo da tambaya abakina yamikamun takardar nakaranta tazube zaune ina taslima nace koyaron wanene kuma

Amman daganinsa nasan danmai kudine la akaridanayi dakayanda ke jikinsa"" washegari damuka kaiwa hajiya kai saitace murikeshi Allah ne yasharemana hawayenmu yabanie kai

Tundaga lokacin mukarika kiranka sultan"" yasakaka makaranta Sam bakataba kukan gidaba tamkar kamanta kowanaka shekaranka biyu anan nasamu cikin Zainab

Kayi murna sosai Wanda komu iyakar Wanda zamuyi kenan"" tunkana karami kakecewa ita zaka aurah dukda asanin kanka ba aure tsakaninku

Idankuma wani yaro yace yanasonta saikamasa dukan tsiya harkagirma akan wannan soyayyar tanisa babanku yaso sanardakai gaskiya dankarya haramta maka zainab nicenace karyafada danzaitado maka damiki kaji ainahin yanda muka sameka!

Kaleed Wanda hankalinshi yagama tashi yace yanzun mom dama bakune kuka haifeniba?? Tagyada masa kai yace Toni suwaye iyayena???


Tace wannan najikin pic din wayar hannunka shine mahaifinka"" kaleed yasake duban pic din damamaki "" yace wannan ne yahaifeni??? Yanisa Tayiyuma batahanyar aure suka sameniba shiyasa suka yardani""

Khadija tace karka ce hakan kaleed kaidan sunnane"" mahaifinku daya da anwar kamannin mahaifinku kukayi"" yayi saurin tarar nunfashinta yace bakida tabbacin haka yama akai kikasan shine mahaifina dankawai munakamà bashizaisa inyarda dahakanba kodama shine mahaifinnawa nibaruwana dashi natsaneshi tunkafin nasanshi

Ashe harzai iyah yarda dansa bayankuma tahanyar aure suka haifeshi shinzaiyi alfahari harma ya iya kiran kansa uba Sam baidace dawan nan sunanba banasonsa natsaneshi

Khadija ce tadakamasa tsawa tace yimun shiru kaleed Sam mahaifinka baichanchànci wadannan miyagun kalamanba ka adanasu saikafadawa lubabatu

Itace tadace dasu"" yace waye kuma hakan??? Mahaifiyatace??? Tagirgiza kai ba itah tahaifekaba matar babankace ita ya aurah bayan rasuwar mahaifiyarka

Amman duk abunda yasameka itace ummul haba isi tarabaka da mahaifiyarka Sannan taso akasheka daganan tasoma bashi labarinsa atakaice tunkafin tagama kaleed hawaye sukasoma sauka afuskarsa yasoma la antar lubabatu bayajin zaitaba yafemata idonsa idonta saiya nakkasata!!! Ashedai kaleed ma yanada zuciya""


Hmmmm anan nakawo karshen *hatsabibin boka* kashi nadaya* saikunjini akashi nabiyu

*shin lubabatu zatawarke daga wannan sihirin datasa akaiwa khadija saigashi itah tafada??*

*Shin kaleed zaiyarda yakoma wajen mahaifinsa???*

*Wai ina labarin hatsabibin boka???*

*ya makomar hatsabibin boka zata kasance???*

*Ko su hassan zasuci galaba akansa sufito da aljana murjanatu idan sukaje dajin???*

*ko aljana murjanatu zatayarda da hatsabibin boka???*

*Labila da muktar zasuyi aure kuwa???*

*Ya labarin kishiyar Fateema mahaifiyar khadija dakuma mahaifinta???*

*yalabarin soyayyar kaleed da Zainab???*

*ina Labarin garba dakuma matarsa huwaile wacce tayita ganawa maman kaleed azaba*

*faruq kanin muktar shinkoyana raye???*

*menene makomar lubabatu maikan doya???*


Duka amsoshin wadan nan tambayoyin sunacikin *hatsabinin boka* kashi nabiyu kubiyoni danjin cikakkun amsoshin tambayoyin taku mai kaunarku Aisha Ibraheem

Sakon gaisuwa zuwa gareku yan group din

*NISHADI GROUP*

*ZANGON LABARI*

*MUMBARIN HAUWA JABO*

*Clever's writer's*
*M khady novels*
*Littafan hausa*
*Feedy luv novels*
*Novels only*
*Zuhurah novels*
*Herwwerh Jeedah fans*

Inakaunarku kamar yanda kuke kaunata


Aisha✍🏼
Chapter 121 · 0% Book details