← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 101 OF 121

Chapter 100

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Bashida imani kokadan sannan kuma yashahara" harwadansu matsafan sukanje wajensa yakowaya masu siddabaru da bokanci azamaninsa babu wani wanda zaijadashi yanada aljanu dayawa wadanda sukaimasa hidima yanada yaro daya sunansa kanzaru"" yanakoya masa yanda akeyin tsafi

Lokacinda ciwon ajali Yakamashi"" yatattara dukkanin kayan tsafinsa yabashi amatsayin gado yakara dacemasa karike wannan aikin domin shine kawai abunda zanbarmaka gado

Kowanne da yakanyi tutiya dacewa ubansa yamutu yabarmasa gado kudine gidajene filayene dakuma kaddarori tonikuwa wannan din shine abunda nabarmaka kamardai yanda nima nagaji wannan awajen babana shima yagada awajen babansa danhaka karka kuskura kawatsarda wannan Sana a Dan acikinta aka haifeka

Lokacinda haiiiiiranu yamutu wadansu bokaye da matsafa sunyita murna saboda Ya addabesu gabadaya aljanunsu suna shakkar sa danhaka ba kasafai suke samun aikiba kowa yafiso yaje wajensa sunyi murna sosai da mutuwarsa aganinsu sunhuta zasu sake suci karensu babu babbaka saigashi kanzaru yazo yakere ubansa da mugunta iyah tsafi siddabaru zalunci harsuke ganin karama ubansa dashi

Lokacinda kanzaru yayi nisa yana damawa acikin tsafinsa saiyayi bincike yagano maciji shine zaiyi ajalinsa kuma bazai Dade aduniyaba

Yashiga Neman inda zaisamu matarda zatahaifamasa dan da danbayaso yamutu baibar wanda zaiyi gadonsaba""

Acikin bincikensa yagano wata diyar sarkin yan bori akasar Igbo kiristance sosai tayimasa aljannunsa kawai ya umurta suka daukomasa itah yacigaba da amfani da itah batareda andaura masu aureba

Saida tashekara biyu sannan tasamu ciki tun cikin yana karami yakeyin tsafi wacikin kuma baiyarda matarsa taci nama dafaffeba saidai danyen nama cikinta yana shiga wata tara"" tasoma nakuda"" yana ganin hakan yatsafeta tasandare dakansa yadayeta yafitarda jinjirin dake cikinta yakwashe jinin jikinta sannan yabawa aljanunsa masu cin nama suka cinye gangar jikin

Hikimaryin haka awajensa yanaso Dannasa karyayi tausayi danmuddin yasha nonon uwarsa zaizama maitausayi gawasu

Jininta shiyatsafe yadinga baiwa yaron yanasha amatsayin nono lokacinda yaron yasoma girma yalaka masa suna *hatsabibin boka* aikuwa yaci sunansa dankuwa tunyana danshekara biyar yakanyi wani kalar tsafinda ko ubansa bai iyah shiba alokacin yacika damurna danyasan koda yamutu yabar wanda zaicigaba da daukaka gadon gidansu

Ko ina na kogonsa akwai hadiman aljanu masu kulamasa dankar maciji yashigo tunda yaga maciji shizaisama ajalinsa yasa akashirya masa wani gado maikyau

Kullum zakasameshi akan gadon baya yarda yaje ko ina dangudun haduwa da ajalinsa abunda baisaniba dukkan abunda aka kaddara shine zaiyi ajalinka baka isa ka kaucemasaba

Shiwannan boka abincinsa nonon shanu Wanda aka tatsashi yanxu yanzu kuma baya yarda yasha nonon awani guri kohannun wani aljanie sai hayyanul zairi danshi kawai ya amin dashi watarana ya aiki hayyanul zairi diban madara bayan yadibo yanakan hanyar dajin zaikaimasa toshikuma yanajin yunwa saiyayi katari dawadansu fatake sunsamu hatsari akan hanya saiya yanke shawarar zuwa yasamu jininda zaisha

Yasamu guri yagirke kwaryar nonon yatafi bayan tafiyarsa da sa o i biyar saiga wani maciji yafito raminsa yanajin kishirwa yanaganin kwaryar nono kawai yakafa bakinsa yasha asheyazuba kuma dafinsa aciki

Yayi tafiyarsa hayyanul zairi yana dawowa yadauki nono yakaiwa shugabansa bawani tunani yakafa kai yasha

Bayan shudewar rabin awa saidafin maciji yasimayimasa aiki yanajin yanayinsa yasauya kawai yadauko madubin tsafinsa yasoma bincike yagakomai saninkuma ajalinsa Yakama yakirah *hatsabibin boka* yadamkamasa gadon

Kujerar mulkin bokanci yasake jaddada masa karyayi wasa dashi danshine zaiyi tinkaho kobayan ransa take yasoma shure shure bakinsa yana fitarda kumfa harrai yayi halinsa

Tanisa tana kallon khadija tace daga lokacin *hatsabibin boka* yafara shuka mulkin bokancinsa cikin zalunci dakuma cin amana

Bayajin tausayin kowaye akabashi yayiwa aiki saikuma akasamu mutanen yanzu sunada rauni sosai akan addu a karancin ilimi dakuma rashin tarbiya

Kezan iyah cemaki babu wani aiki daza abawa *hatsabibin boka* ya gagareshi babu wani aikinda yabashi Matsala samadanaki

Tanisa tanamai kallon hassan tace Ku mutane kunada sakaci yawanci sakacinku shine yake jawomaku matsala

Ansanardaku tayanda zakunemi kariyar Allah daga dukkan wani abun cutarda hakan yashafi aljanu da mutane irinsu *hatsabibin boka* dankuwa sharrinsa yakere duk wani sharrin aljani

Yayi nazari dakuma tunani Dan Adam baida tsawon rai kamarmu aljanu Dan adam duk dadewarda zaiyi yayi tsawon rai bazai haura shekara Dari da ashirin ba

Wannan dalilinne yasaka abincikensa yagano wata Yar sarkin aljanu tanahiyar kudancin Nigeria yaturah bakaken aljanunsa suka daukomasa itan

Yanaso yayi amfani da itah yahaifi danda zaigajeshi yazamana jinsin aljani yafi yawa atare dashi danhaka zai Dade aduniya yanashuka tsiyarsa

Itakuma taki aminta dahakan dankuwa musulmace duk da dagabaya takarbi musulunci tayiriko dashi sosai wannan dalilin yasaka yakaita kurkukunsa dayake karkashin kasa yana ganamata azaba harzuwa yanzu baisamu yardartaba

Kuma atsafinsa yagani aladole saida yardarta idanba hakaba bazaisamu danda yakesoba zaisamu yaron jinin bil adama yayi yawa ajikinsa

Yanzun haka tana tsare acikin kurkukunsa karkidauka itah kadaice akwai mutane da aljanu dayawa awajen wadanda yakeganawa azaba idan suka bijiremasa acikinsu harda bokaye babu Wanda yasan mabudan kurkukun saifa shi danbaiyarda dakowaba yakance shiko kansa baiyarda dashiba ballantana yayarda dawanie khadija tanisa tace ni wannan gimsasshen labarin ya isheni babu wani abun dadi acikinsa menene ribata tasauraren labarinsa tundashidin ba wani malamibane baikafa tarihin komaiba saina zalunci tanisa haryanzu banji amsar tambayataba saidai kawai cikamun kunne dakikai dawannan tatsuniyar banzar


Aljanar ta murmusa tace munkusa ai kisake hakurii

Dajinda yake acikin taraba yake Amman yatsafe dajin tayanda kodamutum yatafi bazaiganshiba
Saifa idan wajensa kikaje sannan zakisamu damar shiga
Shikuma dalilinda yasa yatsafe dajinda yake saboda yagano wadansu yara biyu shune zasu zama ajalinsa
Wadan nan yarankuwa sunzo duniya


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 101 · 0% Book details