← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 25 OF 121

chapter 28

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Bayan kwana biyu kamar yanda sukai da Usman saigashi yakirata"" cikin zumudi tadauka cikin rausaya"

Tace aminci yatabbata agareka annurin zuciyata"" wani sanyine yaràtsa sassan jikinsa yalumshe idonsa sannan yabude

Yace taredake ma abociya sassanyar murya

Dafatar kina lafiya??? Tasake rausayarda kai qalau nake tareda tarin dinbin soyayyarka

Yace wow Amman najidadin hakan sosai abisa dukkan alamu tarkona yakama tsuntsu

kanta tagyada tace aitunima "" yace Amman shine baki sanar daniba kikabarni inata shawagi duniyarda bakowa acikinta saitarin furanni da ababen more rayuwa. Tace to aikuwa hankali kwance tunda kasamu jindadi aduniyar

Yace kisani bazasu burgeniba matukar babu tauraruwa acikinta""

Zuciyata tayita jiran bakuwar soyayya wacce zata tallafeta zuciyata tazama fanko bakomai acikinta tana bukatar abokin zamanee

Cikin zolaya tace to ai akwai kaleed"" gakuma marganyiya mamarsa"" shiru yayi kamar maison tunawani Abu daga bisani yace makotanku suke??? Cikin rashin fahimta tace suwaye???

Yace kaleed danaji kin ambata mana"" takyalkyale da dariya tace kainifa danka nake magana akai""

Yace danakuma??? Wanda zakihaifamun inmunyi aure??? Tace dankadai nayanzu yace Wayafadamaki inada da??? Yaushe harnayi auren dazan haifi da??? Wani sanyine yaratsa zuciyarta lallai boka yagama aiki saitace bakaine kasanardaniba kanada yaro mamansa tamutu

Dariya yayi haryana rike ciki yace badainiba abunda nafadamaki kawai nacemaki nataba aure Amman fa ba azahiriba cikin mafarki mukai auren kuma munyi soyayya doguwa da itah Amman bata haihuba saitarasu tanarasuwa nafarka abarci wlh yanzu ko kamanninta bazan iyah kawomakiba kingakuwa shirmene

Tasake shekewa da dariya tace hakane" yace yanzu idan kin amince zansanarda mamana anemamun aurenki

Dannagaji dazama gauro abokina yayi aure nibanyiba nasan rashin auren ne yasaka naketa mafarkin nataba aure tace shikenan zan sanarda dad komai yace zakaji bayani yace yauwa tawan

Sunkwashe tsayin wata daya sunabuga soyayya usman yamaida legos tamkar dakin kwanansa bayawuce kwana biyu baijeba

Yasaba da ado maigadi sosai lubcy tagabatardashi ga mahaifinta a matsayin wanda zata aurah tasanardasu saurayine baitaba aureba

Baban lubcy yace yaturo magabatansa"" ranarda lubcy tasanar dashi ranar yayiwa kano tsinke"" tunda mom taganshi sai fara a yakeyi sunazaune cikin falo yatankashe kafarsa kasa yanashan kankana

Hafiz yana saman kujerah yanabuga game hajiya tace wainikuwa babangida wanne irin farinciki kakeciki nagatundazu saiwasar hakorah kakeyi???

Yasaka kankana cikin bakinsa yace hmmm mom albishirinki"" tace goro fari tasss tana gyara zamanta"" Allah yasa alkhairine

Yasake murmusawa yasosa kansa yace sosaima "" tace tofadamun inji"" yace nasamo maki suruka mom Allah yakarbi adduarki nasamu wacce nakeso

Aikuwa hajiya tarangada guda kai Amman najidadin wannan labari haba kokaifa duka abokanka sunyi aure Amman kai katsaya ganin garii inason nima insamu jika

Yasunan surukar tawa??? Yana murmushi maikunshe dajindadi yace lubabatu saiyanzu Hafiz yayi magana yace Allah yasanya alkhairi

Suka amsa da Ameen"" aikuwa hajiya tasanarda abokan mahaifinsa kasancewar yan uwan babansa bakusa sukeba"" Dan asalinsu buzayen Niger ne""

Cikin satii daya akagama komai anbiya sadaki dakudin angani anaso"" akasa bikin nanda wata daya""" ranar lubcy tasiye dabbobi guda goma ta aikawa *hatsabibin boka*

Usman dakansa yaje Dubai yahadomata lefe Wanda ya amsa sunan lefe akwati talatin kowanne akwatin shake yakeda kaya sannan dasabuwar mota hul duk acikin lefen

Lubcy saida tahada gagarumin farty gabadaya kawayenta sadiya.aneesa.rabiatu.larai.sajida"" suma saida kowaccensu tazo datata tawagar kawayen awani babban hotel sukayi fartyn kowannensu saida yagirgiza daganin kayanda akadirkowa lubcy amatsayin lefe

Ranar sun gwangwaje sosai saikusan magrib suka watse""

Cikin watadaya lubcy da Usman tamkar suhadiye Kansu Abdul ma saubiyu Usman yana zuwa dashi wajenta

Biki yakarato kowanne bangare sai shirye shirye ake kubra matazo da dankaramin cikinta ansoma hidimomi Usman yagyare gidansa an sake komai kuma anyisabon fenti

Bangaren lubcy kusan sati biyu sukayi suna program event itakanta tasan takere sa a ta auri mijin nunawa sa a

Bikinsu Na gogaggun yan boko ko ince yankarya Dan yanboko akwai karya kankanba danuna sudin wata tsiyane

Ranar lahadi dubban jama a suka shaida daurin auren lubabatu da Usman akan sadaki million 1
Karfe uku motochin Amarya sukadauki Amarya zuwa kano wajen mahaifiyar
Usman yankai Amarya censukà kwana tareda kawayenta

Washe garii akawuce da itah dakinta ai kawayenta basu tsureba saida sukayi arbada aljannar duniya acewarsu

Dan babuce kawai babu acikiñ wannan katafareñ gidan kowa sai santin gidan yakeyi saidare akawatse akabar amarya

Daren Usman ya angonce zokuga ririta tamkar zaimiyarda itah ciki sosai takemasa ladabi hartakan mantar dàshi kowa muddin yanatare da itah

Bayan wadansu watanni lubcy tafara gajiya dabukatarsà saitatsiri ciwon karya kofashin sallah"" lokacinne kubra tahaihu mace akasamata suna bilkisu hidimar kwana biyu tasaka lubcy tadan sarara


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 25 · 0% Book details