← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 65 OF 121

Chapter 68

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Maganin wannan layar kuwa dazaran kishiyarki tabuda baki daniyar yin magana wa mijinki wani mugun doyi zaiji kamar ya surnana hancinsa acikin shadda"" rukayya batasan sanda tayi dariyaba cikin jindadi tace tomenene ladar aikinka ??? Batareda ya kalletaba yace yar uwarki tasani saita sanardake tajuya daniyar yiwa Asma u tambaya yadaka mata tsawa wacce tahargitsamata kwanya yace ba anan zakiyi maganaba kibari saikun bar nan kubacemun daganie

Atsawace yayi maganar asmau tace saikirufe idonki rukayya dajikinta yaketa faman rawa tayi saurin rufe idonta saikuma akasuresu saibakin dajin

Ai rukayya. Tanabude idonta taganta bakin dajin tayanka dagudu daniyar komawa cikin dajin dantafirgita tuncikin fadar bokan saida Asma u tayi saurin riketa tajata dasauri sukabar wajen zuwa bakin hanya

Dakyar sukasamu motarda tamiyardasu gidan magajiya rukayya saida taganta gidan tasoma saukarda numfashi ko abinci batatsaya ciba takwanta barcin wahala yasureta su magajiya sai dariya suke Dan asmau tafadamata yanda sukayi da rukayya

Washe gari kasuwar garin sukaje tasiye dabbobin ta aikamasu dasu tacewa rukayya kinga yanda zakiyi duk lokacinda kikasake dawowa rukayya ta kwalalo ido tace wa???😳 Badainiba aiduk Wanda kikagani lafirah kaishi akayi wlh nishegen tsorone dani ni inama tsammanin sanda yadakamun tsawar nan anyama basuma nayiba?? 🤔

Gaskiya inhar aikin nan yayi aini shikenan banida wani buri aduniya indai tabarmun gidan to mezai miyardani"" ?? Asmau tace akwai kuwa Kawata kinmanta akan kishiyarki kawai akayi aiki to idankuma yasake auro wata anan gabafa??? Rukayya tanisa tace kumafa hakane Amman anya zan iyah zuwanidaya wlh natsorata sosai bantaba shiga tashin hankali irin wannan ba"' Asma"u tace nafarkone aibazaki sake jinhakanba

Tace shikenan garin suka sake kwana washe gari sukadawo gida "" saida tahuta gidan asmau sannan tawuce gida da sallamarta Tashiga gidan tasamu fateema zaune tanashan iska da itah da muktar Dan gwaggo takarbi faruq ..

Tana ganinta tasaki fara a la Anty sannu dazuwa wlh yanzun nan nakezancenki araina inatunanin kokin taso"" kujerah taja tazauna tanacire hijab tace wlh kuwa tunsafe mukataho yazaman gidan

Fateema tace babuwani dadi gashi abban faruq anturashi wajen wani aiki jiya Amman inajin gobe zaidawo duk zaman gidan ya isheni gashi ban tambaya ba dasainashiga makota

Rukayya tace Karma kisoma bakigani nikaina baburuwana dashiga makota yanzufa duniyar nan mutum akekiyo ba dabba ba

Fateema tace aibama zanfitaba"" rukayya tasaka hannu cikin Jakarta saikuwa ga mangwaro guda biyu tafitar tanacewa ga abunda kikafiso nasiyomaki ai fateema tanayin ido hudu damangwaro yawunta suka tsinke"" abunkada maiciki tanakarba batawankeba babu maganar bisimillah kawai takama gabtar mangwaro

Wani shu umin murmushi rukayya tasaki aranta tace taki takare fateema "" nantake tashanye dayan tadauko dayan tafasa sai muktar yaceshima sai tasammasa takilla tabashi kamar rukayya tahana saikuma takyale dankar fateema tadauka akwai wani abun

Ta sake gabtar mangwaro tana lunshe ido saboda dadi tace wai Anty ina kikasamu mangwaro alhalin yanzun balokacinsa bane???

Rukayya tadauko bokiti tace baridai inkara maki dankarki fadi tana dariya tace bafa santi nakeyiba kumama koda santin nayi aibalaifi kinkuwaji yanda mangwaron nan yakeda zaki???

Rukayya tace inazansani aikinsan nibanashan mangworo"" fateema tace hakane naman ta wlh hartashanye mangwaron bata ahamoba tacewa rukayya dakinsani deyawa kika siyomun

Tace ayya wlh nima akan hanya naganshi sauranshikawai danasan kina sonsa sosai nacewa driver yatsaya dakyarma nasamu yatsaya""

Fateema tace Allah sarki nagode Anty"" rukayya mikewa tayi tace baridai indan mike kafata kafin la asar barci nakeji wlh fateema tace tosaikin tashi tawuce dakinta tana murmushi

Washe gari tundasafe tajefa layar acikin masansu tazuba ruwa yabiruwa yafada cikin shaddar dadare koda Muhammad yadawo fateema tayi barci baiko kalli kofar dakintaba yashige bangarensa

Rukayya tana ganinsa tahau tsallen murna washegari dasafe tanadaki saiga fateema tashigo tana yakunar fuska tasamu guri tazauna tagaida itah ta amsa dasakin fuska

Saikuma tayi shiru rukayya tace yadai maman faruq??? Kamar tayi kuka tace Anty ashejiya abban faruq yadawo Amman baitasheniba

Rukayya tace ah watakil yalurah kinajin Da din barcinne"" tanisa Anty aibahakan yasababa sai idan yanzune zaisauya""

Rukayya tace toki kirashi mana"" nimadai jiyan banganshiba saidasafe danaga kaya afalo nasan yadawo

Fateema tace wlh nakirashi yafisau ashirin yaki dagawa bansan laifinda naimasaba"" rukayya tace kisake gwadawa dai haka fateema tayita gwadawa hartagaji takoma dakinta

Yinin ranar takasa cin komai harwashe gari kwanadaya rak hartasoma ramewa"" tana tsaka datunani kawai saiga Muhammad yafado dakin dasauri takalleshi kamar zatayi kuka

Yanayinda taganshi yamatukar furgitata kafin tamike yahau dukanta batasan hawaba batasan saukaba tuntana yunkurawa daniyar tatashi tagudu hartakasa tayi kwance shikuma gabadaya bayagani yasa kafa yahalbeta aruwan cikinta wata mugunyar karar wahala tasaki take jini yasoma fita takafafunta Muhammad baikyaletaba saida yaga bata numfashi sannan yayarda bulalar yafitaa fuuuuu

Saida yafita rukayya tasadado taga aika aikarda yayi damakuwa tanaganin zuwansa tashige dakinta ganin tanamasa magana yawuceta fuuuu dariya tasheke da itah tace inakuma soyayyar take ayanzu???

Muktar yana gefe yana kuka yanakirah amma rukayya tadaka masa tsawa tace munafuki rufewa mutane baki" muktar yasake bare bakinsa yacigaba dawani kukan saida tasake katsamasa tsawa wacce tafirgitashi shima atake yaja zuciya numfashinsa yai sama

Ta sake bushewa da dariya sannan tafita tadibo ruwa ta yayyafamusu kusan taresuka far fado muktar yashige jikin fateema yana kuka

Fateema bayan tagama nazarin abunda yafaru da itah Wanda take gani tamkar mafarki"" tasake fashewa da kuka"" mai tsuma zuciya

Takalli rukayya tace Anty me yake shirin faruwa danine haka?? menaiwa Muhammad yayimun wannan dukan kamardai Wanda bashida imani??

Rukayya tace waikina nufin shine yadakeki?? Toyanibanji shigowarsaba fateema tace wlh shine Anty

Rukayya tace kekuwa laifin mekikai masa??? Tace wanne irin laifi Anty wlh banyimasa komaiba"" rukayya tace to Allah ya kyauta tawuce abunta fateema tabita da kallon mamaki kamar bataga halinda take cikiba ""

Rukayya tanafita takirah asmau tanadauka tace yee Kawata aikifa yanakyau"" asmau tace banafada makiba

Tace ainagani yau Muhammad yalakadawa Yar iska shegen duka inajifa kamar tayima bari"" asmau tace toyanzu tana ina??? Rukayya tamere baki tace tanadakinta kwance inda yabarta

Asma u tace yazakiyi haka aizatayi saurin zarginki banafadamaki dakissa akehadawaba yanzu kidauketa kuje asibiti dagacen kicema ayimata wankin Mara idan akwai sauran Matsiyacin yayo waje""

Rukayya tace toshikenan dasauri takoma dakin tasamu fateema tasake suma" fita tayi dasauri tasamu Dan tax dataimakon wata makociyarsu aka kai fateema asivibiti

Likita yatambayi menene yayi sanadin zubewar cikin??? Rukayya tace aifaduwa tayi Amman ayimata wankin Mara karyazama ciwo ajikinta"" alokacin har anjona mata Karin ruwa

Suna nan harkusan la asar lokacin fateema tafarfado Amman bata bude idontaba"" tanata tunanin wannan lamarin""" kwananta uku asiviti Muhammad bailekoba gashi likitoci sunbar zuwa gurinda take kaibartasuma har wadanda sukejinya daki daya duk sun sauya daki

Aladole tasallami kanta tafito duk Dan adaidaitan da tatara baya tsayawa gashi jikinta baiyi kwariba tana tafiya tana tsayawa tana hutawa hartakai gida

Gashi tafiyace mainisa ajigace takarasa gidan tashige dakinta tafadi kwance tafasheda kuka muktar ne taji yadafata tadago takalleshi duk yayi damau damau cikin kashi tasake fashewa da kuka maitsuma zuciya saida tayi mai isarta tahakurah dankanta

Dakyar tatashi tashiga kichin dinta tasulala taliya sukaci bayan tawankemasa jikinsa haryanzu bataji duriyar rukayyabà Ashe tana makota tabar muktar shikadai cikin gidan

Wasa wasa fateema abusai gabayake batajin sanyi wajenkowa saiwajen rukayya danyanzu saitakwashe watadaya batasaka Muhammad a idontaba

Duk ranarda abun yacizoshi zaizo yayimata shegen duka gabada ya yan uwansama sundauke kafarsu daga gidan

Gashi tanada zurfin ciki ballantana takirah tasanarda su Anty hasana halinda takeciki saidai ciwo yayita cinta ahankali""


Kwanaki sunata tafiya sati haka watanni haka shekaru haka fateema ta lalace tayi bakiii kirin wacce takefara"" alokacin muktar shekaransa shida aduniya yayi wayo sosai hakazalika shine kawai kedan kwantarwà fateema dahankali

Watarana dadare tanakwance zafii yadameta tatashi tawatsa ruwa tadauro alwala"tanashirin kwanciya saiga Muhammad yafado kamar dagasama

Tatsorata daganinsa dantasan babu abunda zaikawoshi dakinta idandai badukanta zaiyiba


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 65 · 0% Book details