← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 66 OF 121

Chapter 70

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Yanisa yana kallonta yace kikwantarda hankalinki yata nine nan zankwatomaki yancinki"" tayi saurin kallonsa tace taya baba aikuma aikingama aiyagama""
Yace ninasan yanda zanyi zanmiyar mata da abunda taimaki"" inhar kin amince dahakan"??? Taja majina tana kallonsa tace idan har nayarda amiyar mata da abunda tamun menene banbancina da itah???

Tanisa ninabarta da Wanda yayi rana dakuma faduwarta koda nayarda amayarmata tunda babu aure tsakanina da Muhammad aikin banzane nikawai nabarta da mahaliccinta indai duniyace aigata ga duniyar niyauma zanwuce garinmu danba kinciki zai iyah kasheni anan idan inatunoshi

Malamin yayi murmushi yace hakane yata dama nayi tunanin hakan Amman tundakince kinbarta da Allah bariga Allah yafi" yagyara zama Amman kitsaya kikwana biyu akwai taimakonda zanbaki kafin kitafi""

Tashare hawaye tace kayi hakuri baba niyau gida zantafi"" banason sake kwana garidaya dashi malamin yace dolefa kiyi hakuri dantafiya bata samekiba. Kinkuwasan abunda ketare dake barta mijinki ko yan uwanki idan kikaje babuwanda zaikalleki dankuwa abunda yake ajikinki kokinfita babu mai motarda zaidauke ki kinkosan bazakije gida akafaba

Fateema tayi shiru kamar mai tunanin wani Abu saikuma tace shikenan zata zauna"" tundaga ranar malamin yasomayimata rubutu tanasha dawani garin maganie"" dayayiwa hadi da habbatus sauda da turaren miski dawadansu kalolin turare yahada dazuma farar saka akadama daruwan zanzan kullum dasafe saisunsha chokali daya

Da itah da mukhar harnatsawon sati daya"" bayan sati daya saigashi tasoma wani irin a mai baki kirin da gudajin mangwaro aciki hakashima muktar ammanshi bayawa sosai danshi baici dayawaba yanayin cizawa daya yaji tsami saiya Yar

Abunda tagani yanzu shine yasake tabbatarmata da gaskiyar lamarin"" saida tasake kwana biyu malamin yayimata kudin motar saida zata tafi tarambayesu sunansu

Matar tace sunanta khadija mijinta kuma ibraheem ta sake yimasu godiya harwajen shiga mota yasa aka Kaita tundasuka shiga motar tashiga duniyar tunani harsuka kawo kano

Tahau Dan adaidaita zuwa unguwarsu koda tashigo duk yawanci suna masallaci wajen sallar magrib dasallama tashiga gidan tasamu matar Yaya garba tana kada miya

Ta amsa sallamarta tataso taga kowacece tanaganinta tace yarbaba !! Kece da magribar nan lafiyadai??? Saikawai fateema tafashe dakuka tafada jikinta

Tace yau nabani nidiyar mutum biyu jikar mutun hudu menene kuma yafaru yarbaba"" ??? Fateema batace komaiba taci gaba dakukanta anahaka garba yashigo dasallama yayi tsaye yana kallonsu yace kukan wanakeji kamar yarbaba???

Bilkisu tace wlh itace malam niduk ta tayarmun dahankali "" jinta ambaci sunan yarbaba garba yazoda sauri shima yahau tambayarta jikinsa harrawa yakeyi danyana tsoron ace abunda mahaifiyarsa tayiwa mahaifiyar fateema shine aka sake maimaitawa

Fateema yanda taga hankalinsu yatashi saijikinta yayi sanyi anan take sanardasu aurenta yamutu sukai tambayar duniya tafadamusu meyafaru haryasaketa tace laifi tayimasa takisanar dasu komai harsuka gaji sukasamata ido

Dakin ta tashare takoma ciki washe gari su hasana sukazo suma babuyanda basuyiba Amman bandakuka datakemasu idan sun matsamata da tambaya dole suka kyaleta garba yaso yaje yola din

Fateema tace karyaje tunda saki uku yamata menene amfanin zuwan tunda koyahakurah bakomawa zatayiba

Aranta tace aikoda akwai sauran igiyar aurena dashi bazan komaba ballantana komai yakwabe yace shikenan

Ahakan tacigaba darainon cikinta haryafito batafirah dakowa inba muktar ba"" gashi ciwo yanacinta gayawan tunani"" cikinta yana shiga wata tara tasanarda matar garba in Allah yasauketa lafiya intahaifi mace khadija takeso asamata idankuma namijine ibraheem

Bilkisu tace banda abunki kibari saikinsauka mana saikifadawa yayanku"" murmushi tayi Wanda rabonta dayin irinsa andade tace inaso komenene nahaifa asakashi islamiyya inaso yayi karatun sosai kullum maganarta kenan

Ranar wata juma" a cikin dare tatashi da nakuda muktar ne yasheka yana bugawa su balkisu kofa dama bawani barci mainauyi takeyiba dasauri ta mike tafito waje

Dakin tashiga dasauri tarufo kofa fateema tayi matukar galabaita tafita hayyacinta saikusan asuba tahaihu

Kojuyowa batayi taga abunda tahaifaba raiyayi halinsa bilkisu taduka tadauki Yar tayankemata cibi tawanketa tagyara wajen garba yanakofa tsaye da muktar yana kuka

Saifita take tana dawowa tadaicemasu ansauka ansamu mace Amman batasanardasu. Yarbaba tarasuba saida tagyara wajen tashirya jaririyar takuramato ido yarinya tamkar uwarta babu abunda yarabasu
Hawayen tausayinta ne suka sauko akan fuskarta Allah Sarki kekuma taki jarabawar kenan fita tayi tabasu yarinyar takoma takimtsa fateema

Fuskarta tayi haske fayau tamkar tana murmushi kamar kayi magana ta amsa rayuwa kenan "" rayuwa bawani abubace dazaran anzaremaka rayuwa takomai takare

Duk kwanbonka komai kudinka saifa kadandani mutuwa menene abun dagawar ??? Dazaran anzaremaka rai yanda kasan mutum mutumi haka zaka koma shikenan taka kuma takare babu sauran jindadi masu bururruka aduniya Allah yasa mucika da imani Ameen

Tadade dakin sannan tafito garba yace yamai gejon tana lafiyadai ko ??? Tagyada masa kai kawai alokacin hawayenda take boyewa suka karasa sauko wa takauce idonta danta goge Amman haryagani dasauri yashiga dakin tana kwance inda tahaihu ahankali yataka zuwa inda take yaduka yashafo fuskarta yace Allah Akbar Allah yasa kinyi kyakkyawar tafiya yatofa mata addua sannan yamike alokacin ansoma Kiran asuba

Yakarbi yarinyar yayimata huduba da sunanda mahaifiyarta tace yamikawa bilkisu yakalli muktar yace muje kayi alwala muwuce masallaci bamusu yawuce yayi alwala shima yayi sukatafi masallaci

Bayan an idar yasanarda liman akayi sanarwa za ayi za na izarta da karfe goma muktar baisan meyake faruwaba saida yaga mutane sunsoma cika gidan sannan hankalinsa yatashi yatambayi garba meyake faruwa ne

Bawani boye boye yasanarda shi yayi tsammanin zaiyi kuka saiyaji kawai yace Allah yajikanta yamatukar bashi mamaki gashidai karamin yaro taredashi akai mata sallah har aka Kaita makwancinta

Tundaga ranar rainon khadija yadawo hannun muktar dayake matar garba yaranta biyu duk mazane batasake haihuwaba daga garesu madara akarika bawa khadija

Allah yarayata tuntana karama she gen wayo ne da itah makaran tarsu daya da muktar kowakuma yadakarmasa Kanwa kowaye saiya rama mata bayaso yaga kukanta kokadan

Shikeyimata wanka da kwalliya akanta yakoyi kalaba danbaya kaita wajen kitso tunda yakaita sodaya yace masu kitson mugayene kwarai suke kitsawa danmugunta "" shikuma ahankali yakemata anayi anashan minti kuma bata kuka

Tana primary 2 yagama makarantar yashiga babbar makaranta soyayya maikarfice atsakaninsu shine uwarta shine ubanta ko yayan inna balki suka daketa bayajin kunyar kowa zairama mata

Sannu kan hankali tanazuwa boko tanazuwa islamiyya Amman tafi bada karfi islamiyya datadawo boko tawuce islamiyya sai magrib ake tashinsu idankuma ranarda ba bokone karfe bakwai nasafe sukezuwa sai magrib

Tun tana yarshekara biyar takai hizif hudu kuma dazaran anyimata karatu nantake take daukesa akanta lokutta dai sunata tafiya khadija tanasake girma"" tanagama primary shikuma yanashiga ss 3 " tashiga itakuma jss 1 alokacin tanada shekara goma shabiyu"" yana gama secondary skull yashiga bayero university"" alokacin khadija takusan sauka alokacinne suka hadu da labila tadawo kano dazama saita shiga islamiyyar su waje daya suke zama Allah yahada soyayyar su waje daya saigashi kuma ashema makotane soyayarsu tayi nisa sosai kullum zakagansu tare alokacin muktar bagida yake kwanaba cen makaranta yake kwana idankuma bakaratu yakanshiga gari yayi aikin karfi yayiwa khadijar sa siyayya "" tuni tabashi labarin sahibarta dasuka hadu duk yakirah waya maganarta kenan sahibar ta"" su gwaggo hasana da Husaina duk sun hayayyafà kowace yaranta biyar duk sungirma Amman muktar shine babba sai yayan uncle garba sulaiman da dahiru suma suna bayero

Tana ss1 muktar yatafi kasar waje waje karatu dansosai yanaso yayi ilimi yazama maikudi bayason kanwarsa tayi kuka anan gaba Amman ranarda zaitafiii tasha kuka dakyar tabarshi yatafi

Tundayaje baidawoba saida yakwashe shekara biyu anyimasu walimar sauka dukda khadija tadade dasauka ba ayi walimarba akace sai ansamu kamar mutum dari duk dahaka sai aka kaita ajin hadda alokacin yazo yaga khadijarsa tasake girma kyanta yasake fitowa kamanninsu da mahaifiyarta yasake bayyana tana ss 2 lokacin suna shirin shiga ss 3 bangaren karatun islamiyya kuma hartakusa hardace alkur ani

Muktar baramin dadi yajiba yanda kanwarsa tazama hafiza suna zaune tana rubuta wani hadisi acikin littafinta muktar yakurah mata ido yanata faman murmushi

Ajikinta taji kamar ana kallonta tadago saisukai ido hudu itama murmushin tasakar masa tace Yayana meyafaru??? Murmushin yasakeyi yace idan ina kallonki nakan tunoda mahaifiyarmu

Kamanninku daya saidai kawai kindarata haske kadan dakuma wushiryar da kikeda itah bayan wannan bakuda banbanci hatta Dan abun nan naki dimpull tanadashi akowanne saitin kumatunta

Yanisa please Kanwata karkisa soyyya acikin rayuwarki kamar yanda nadade inasanardake mom tace tanaso kiyi karatun islamiyayya sosai yanisa banason kibiyewa abokai dannasan yanzu a skull kananun yarama zakagansu suna soyayya

Hawayene suka sauko akan fuskar khadija take muktar yarude yataso daga kan kujerar yaduka gabanta habarta yadago yace kuka farincikina

Maganatane tabata maki rai ¿kaita girgiza tace bahaka bane Yayana natunoda mom ne inama nima nayi rayuwa da itah inji diminta kamaryanda kowa yakejin dimin mahaifiyarsa

Kuka tafashe dashi maikarfi muktar baisan sanda shima yafashe dakukanba labila shigowarta Kenan tanufo dakin tajisu suna kuka duk dabaya yabata hakanne baisa taga fuskarsaba saida sukai mai isarsu sannan muktar yayi karfin halin soma lallashinta ganin zaimike labila tayi saurin juyawa tafita batareda sungantaba

Kwanansa biyu yakoma baisake dawowaba sai lokacinda khadija akaimasu walimar haddace al Qur ani

Dalilinda yasaka labila tacewa Usman sunan mahaifiyarta akasamata dan kawai taji yangidan suna cemata sapna wannan sunan kuma muktar ne yalakaba matashi yanajin dadin sunan idan khadija tace saboda mene bayakiran sunanta saiyace ai sunan umma ne to itama hakan tasanarda labila shine tarike

A Takaicedai wannan shine ainahin tarihin rayuwarta dakuma tushenta babukuma Wanda yasan wuyarda maman khadija tasha sai muktar danbaimanta komaiba shiyasa yakeganin anyama zaiyarda yabawa wani khadija???

*KYAWON TAFIYA DAWOWA*


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 66 · 0% Book details