← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 50 OF 121

Chapter 53

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Yanzukam Usman yafitarda rayuwar kara aure yabarwa Allah zabinsa yasan wannan jarabtace Allah yabashi ikon cinye wannan jarabawar

Zaicigaba da azumie yakumaci gaba dashan magani idankuma harciwon yacijikinsa inkwanansane yakare to Allah yajikansa

Tuni yakauda kai gadukkan abunda yasan zaitadomasa da sha awarsa gabadaya company nsa yasallami ma aikatansa mata baibar kodayaba bayan yabasu makudan kudi yace sunemi wani aikin daban sosai sunji bakinciki dankuwa babu inda ake biyan su albashi mai gwabigwabi sama da wannan company sosai maishi yasan darajar aiki dakuma biyan ma aikata kudinsu akan kari kuma amutunce


Baibar mace kodayaba yasaka duka maza"" duk satii saiyayi sadaka yana Neman Allah ya bashi lafiya" Yakuma yayemasa damuwàsa


Zaune yake cikin falonsa sama lubabatu tana gefensa suna kallo wayarsace tahau ringing"" tana gefensa yanadubawa yaga labila cikin fara a yadauka

Tareda sallama ta amsa adaya bangaren"" tace dad
Barka dadare??? Yace yauwa kina lafiya?? Tace qalau nake dad fatan kaima hakan??

Yanisa insha Allah "" yakaratun??? Shekaranjiya ainakirah akacemun kina makaranta wajen harda" tace wlh kuwa dad abunda yasakama nakiraka kenan

Yagyara zama wani abunne??? Tace ah maganar walimarda za ayi makarantarmu tawadanda suka hardace AlQur'ani dakuma wadanda suka sauke


Hardar mataki matakine akwai masu hizifi sittin akwai arba in akwai talatin akwai masu a shirin goma dakuma biyar

Daga kowanne aji ni inacikin masu arba in" yace masha Allah godiya tatabbata ga Allah madaukakin sarki

Allah yataimaka tace Ameen"" wlh naji dadi sosai labila yaushene walimar??? Tace saurah satii uku Amman Dan Allah dad wannan karon kazo yace karkidamu zanzo "" tamarairaice fuska kamar zatayi kuka race sanda nasauka bakazoba ai""

Yace sha kuruminki wannan karon koda tafiya takamani zansoke tafiyar indai zuwan nawa zaisa amanta dawancen laifinda nayi

Dariya tayi tace bakayi laifiba ai kawaidai naga kowacce mahaifinta yanazuwa mata"" yace aikema haka baga uncle Hafiz nanba

Taturo baki nidai dad ah ah kainafison kazo inaso naganka"" yamurmusa tokarki damu zanzo dame dame kike bukata zan aikomaki dakudi saiki siya""

Tace la dad damakabari wlh uncle yasiyamun komai harnakai ankon wijin dinkii"" yace duk dahaka ni ai yakamata nabada tawa kyautar

Tace hakane to dad kabani duk abunda Allah yahoremaka komenene zanji dadi"" yace dagaske??? Kaita gyada sosai

Yace shikenan ga mom dinki"" saida tadan yakuna fuska kamar wacce taji anfadi abun kazanta tace bata mugaisa yace to tareda mikawa lubabatu wayar

Damamaki take kallon wayar tamaida kallonta wajenshi tace wayene?? tasan labilace Amman kuma tundatake labila bata tabacewa abata wayaba shine takeson gazgata abunda taji

Usman yace kinajifa sanda nakirah sunanta to labilace zakugaisa"" Tamika hannu takarbi wayar takara akunnenta batareda tace komaiba

Labila takatsemata tunani tace mom kinyi mamakin jinnace abanike mugaisako??? Hmm bawani abubane kawaidai inason insanardake yarki tahardace hizifi arba in acikin littafi mai tsarkii za ayimasu walima

Yanadakyau kema kisamu kizo walimar kozaki tuba kidaina abunda kikeyi kumakinemi gafaran dad dankuwa kina cutardashi nabarki lafiya

Tanakaiwa nan takashe kiran"" lubabatu tayi murmushi tamikawa Usman wayarsa batace komaiba

Amman aranta tana jinjiina maganar labila

Usman yanisa yanamai kallonta yace waiku meyasa haryanzu bakwa barin wannan al adar taku waishikenan idan kanada darfari bazaka sakemasa fuskaba??

Saikanuna tamkarma bakasonsa alhalinkuma kanason sa wayezaihaifi dayace bayasonsa Amman abunda kuke nunawa yayan fari baidaceba hartakai sukansu basa sakinjiki daku"" lubabatu tasaukarda ajiyar zuciya tace to aihakan mukatashi mukaga anayi ai kunyace bawai rashin soyayyaba"" baki kawai yamere yacigaba da kallonsa

Itama batakoma kansaba tundadai basurutun takeson yiba"" washe gari kuwa ya mata siyayya kaya masu kyau ya aiki driver yakaimata tareda kudi takara wajen hidima


Tun anasauran sati daya walimar akasoma sanarwa kafafen yada labarai su labila ansha kyau anyi gyaran gashi da itah da sahiba anko sukayi komai nasu iri dayane"" hatta kunshi da akaimasu zanen iridayane

Anagobe walimar labila agidansu sahiba takwana saboda batakarisa hardartaba"" sahiba sai dariya take mata waitafaye son wasane takaimata dukan wasa tagoce tana dariya "" labila tace wlh bawasa bane kinsan baiwa kowa da irin tasa tace hakane"" yauwa sahiba banfadamaki ba gobedai babana zaizo inaso zannuna makishi kugaisa tunda baizoba sannan

Tace shikenan sahiba Amman kinsan wani abu??? Labila tace ah ah saikinfada"" tayi shiru daga bisani tace wlh tunsanda akacemaki saurah kwana biyu walimar nan gabana yaketa faduwa narasa dalilin faduwar gaban""

Labila takalleta saikuma takyalkyale da dariya tace Allah yasadai alkhairine"" mukam musha biki "" takalleta da harara tace dagafaduwar gaba kuma saikusha biki ?? Tobikin mene???

Labila tana linke kayansu tace kikasani ko wani kyakkyawa zakiyi gamodashi"" tace waini??? Haba sahiba ainayi kankanta dayin aure yanzu sainan gaba aikoke bazakiso nayi aure yanzuba


Labila tace saboda me?? aini tuni nazaba miki miji kawaidai inajiran hukuncin Allah ne yazabamun abunda yafi akhairi nasankuwa kowaye nazabawa sahibata bazataki amincewaba
Murmushi kawai tayi batasake cewa komaiba!!

Harabar islamiyyar cike take makil damutane bakako hangen karshensu gabas dayamma hangu da dama dandazon dalibaine wadanda suka sauke dakuma masu harda

Cen saman dandamali malaman makarantane""gefensu kuma wata babbar rumface shake take damanyan mutane yankasuwa suwagabanni harda sarkin kano yana cikin shigarsa ta alfarma"" gefensa fadawansane sukemasa fiffita gamnoni daga kasashe daban daban duka sun ziyarci wannan walimar domin taya daliban dakuma iyayensu Murnar wannan babban abudasu kasamu nahardace littafi mai tsarkii

Bayan annatsu aka kirah amirar makarantar wato khadija Muhammad domin tabude taro da addua""

Wata karamar yarinya naga tataso cikin shigarta ta alfarma tanasanye dahijab harkasa fuskarta lullube take cikin likab kafarta tanasanye da safa shekarunta bazasu haurah goma sha shida ba" tana tafiyarta cikin natsuwa idanuwanta suna kasaa

Takarasa inda malamin yake tadan gurfana takarbi lasifikar tasoma addua Cikin harshen larabcii gabadaya wajen kaji yayi tsitt bayan tagama bude taro da addua takoma mazauninta

Usman gabadaya yarasa natsuwarsa saibinta yakeda kallo tunsanda aka kirah sunanta yaketa nanata sunan aransa

Shikanshi tunsanda anasaura kwana hudu walimar yakejin matsanancin faduwar gaba"" saiyanzu dayaji muryanta yasakejin faduwar gaban tayawaitaa idanunsa suna kanta duk da akwai tazara maiyawa atsakaninsu

Kusada itah watace zaune itama cikin shigar kamar ta khadija tsayinsu zaizo kusan dayasam hankalin Usman bayawajenda ake gabatarda dalibai tundaga matakin sauka har aka kai matakin harda


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 50 · 0% Book details