← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 116 OF 121

Chapter 015

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Bayan kamar mintuna goma labila takalli khadija tace kinga sahiba babu amfanie wannan jiran muci namu muje mukwanta

Murmushi kawai khadija tayi dankuwa ranta yasosu dawan nan abun Amman kuma batason nunawa labila dankartaji wani iri" Usman yasan girkinta ne Amman yaje dakin lubabatu yayi zamansa saikace ranar girkinta

Saida labila tasakeyin magana tukun Khadija tazuba masu tasan bawani cizatayi dayawaba Amman hakan tayita wasa da chokali har labila talura takirah sunanta

Sahiba khadija takalleta daguntun murmushinta tace yadai sahiba?? Labila tanisa tana aje tsokali tace kiyi hakuri" khadija tasake murmusawa tace da...akayi mekuma??

Labila tace nasan kinsani Amman kiyi hakuri nikaina abun nan baiyimun dadiba Dan gaskiya dad bai kyautaba duk danasan balaifinsa bane akwai sahannun mom

Khadija tayi Sako tana saurarenta kenan tana nufin maganie mom tayiwa Usman??? Komadai menene zataganie daga baya idan taga yacigaba dahakan tozargin gaskiyane

Tanisa tana kallon labila tace bandamuba sahiba bakisan menene yatsaidashi ba kirika yiwa Mutane kyakkyawar fahimta mana

Tasoma cin abincinta ganin hakan yasaka labilama tasoma cin nata harsuka gama usman bai saukoba sukayiwa juna saida safe kowa yawuce inda zaikwanta

Dayake labila bangaren lubabatu take kwana saida Usman yaji motsinta"" sannan yataso Dan lubabatu tadade dayin barciii

Kallo daya yayiwa labila yasan akwai Matsala Dan dauke kanta tayi tashige daki" yayi shiru waima meyasa yadade harhaka ??? Sam yamanta suna jiransa jiki sanyaye yasauka kasan baisamu khadija ba saiyawuce bangarenta

Itakam harta kwanta rigar jikinsa yacire yahau saman gadon yakwanta gabanta yanda zai iyah ganin fuskarta

Yajawota jikinsa Sam batacemasa komaiba kuma batayi kokarin jaye jikintaba"" andauki tsayin mintuna ashirin yakasa barci saijuyi yakeyi yasake kallonta idanuwanta arufe suke bazai iyah tantancewaba barci takeyi kokuwa idonta biyu

Sunanta yakirah Deejarh Na" bata amsaba saida yasake kiranta sannan ta amsa batareda tabude idonba

Yanisa kikalleni Dan Allah Deejarh na"" yamarairaice murya Dan murmushi tayi sannan tabude idonta ahankali takafa masa ido

Tuni yasanne kansa kasa Dan abunda yaganie acikin idon khadija "" baice komaiba tagajie dajin shirun tace kaci abincinka kakwanta nima barci nakeji tanakaiwa nan tasake gyara kwancinta Usman yarasa yazaiyi yace khadija maganafa zamuyi

Tace dad abar maganar nan saigobe barci nakeji yanzun" kafadarta yadafa yace tokiyi hakuri Dan Allah

Tasaki lallausan murmushi tace laifin me kayimun?? Ina anabada hakurine gawanda akayiwa laifi nibakamun komaiba karma kasadamuwa aranka

Yasake sukurkucewa yace Nina San nayi laifin ai tunda nanemi ayafemun wlh bazan iyah yin barciba inhar bakince kinyafemunba

Danaje kiranta nasamune batada lafiya aikisukai gidan kawarta jikinta yanamata ciwo shine nataimaka nadan daddannamata""

Khadija tace hakan yanada kyau Allah yahutarda gajiya ""😑 sosai Usman yasan khadija da ma ana biyu take yin magana yace bawan nan ba nidai kice kinyafemun""

Takalleshi tace tonayafe maka shikennan ko saida safe"" yasake bata fuska"" tace menene kuma?? Yace kincemun saida safe yanzun haka zakibarni

Tome zanyimaka nibarci nakeji" kenan baki hakuraba???

Wayafadamaka??? Aidakin hakurah dabazaki hanani abunda kikasan nafisonsa fiye dakomaiba

Hannu tasagalo masa awuya tace kafin nan yakamata taci abinci dannasan kanajin yunwa"" kaiyagirgiza yace bazan iyah cin komaiba yanzun kina wannan yanayin lumshe idonta tayi sannan tabude tana kallonsa sannan tamike tadaurah zanie tafita shima yamike yabiya abaya harkasa tazubamasa abincin tajuyo sukadawo tare

Dakanta tarika bashi abaki haryakoshi tamiyarda kayan yayi brush sannan suka kwanta
***********************
Washe gari tunsafe suka gama hada kayan break labila kam dataga khadija tasakewa Usman haushi tabata nikam nace baki iyah shiga tsakanin mata damiji

Taresuka zauna cin abincin Usman ne yafara tashi danyana sauri zaije company yau akwai bakinda suke saran zuwansu akan wani hadin guiwa""

khadija tarakashi harbakin mota tayimasa adawo lafiya tadawo sukacigaba dakarya warsu labila ma takoshi tadauki littafanta tawuce akabar khadija da lubabatu

Khadija takwashe kayanda suka bata tamiyar kitchen tadawo tahaye sama abunta lubabatu dadi yakumeta tatashi tahau saman tadauko battar takarasa bangaren khadija" da sanda tabude battar tabarbade maganin duka sannan takoma dabaya dakwallawa khadija Kira

Tana kwance kusa dasu anwar taji kamar mom takirata tamike zatafito kawai sapna tabare baki tasoma kuka"" nafitar hankali kamar wacce akaciza

Dasauri khadija tadawo tadauketa saitayi shiru "" lubabatu tasake kiranta dasauri tamike tareda sapna tawuce

Anwar da husna suka kata kusan atare harda sapna din dolenta khadija takoma tamarasa yazata daukesu duka

Lubabatu dataji shiru saita dauka khadija batajibane tadawo kofar dakin tasake kwalamata kirah kamar wani yaturata saikawai tazame tafadi dabas kafafuwanta suka tabi maganin saiga lubabatu tana mulmula akan maganie

Data hankalto damenene yasameta tafasa ihu nashiga uku na lalace🙆🏿 " wannan Kalmar da khadija taji yasaka tayi saurin ajesu anwar tafito dasauri wannan karon su anwar wasasuke dayatsun hannunsu basuyi kukaba

Ganin halinda mom takeciki yasa hankalin khadija yatashi tace hasbinallahu wa ni imal wakil mom meyasameki??? Sai lokacin akadaina jujuya lubabatu

Tayi saurin mikewa idanuwañtà zuru zuru tace bakomai dama zance idan kinyi ajiyar maganin ciwon jiki kibanie sainazame anan

Khadija tace Allah sarki wlh fitsari anwar yasaki dazu awurin shine nagoge daruwa Ashe akwai sauransu sannu gashikuma banida maganin Amman barinakirah baban sapna saiyaturo yaronsa yakawomaki

Lubabatu tace ah ah kinjifa yace sunada baki baridai nahakurah zuwa anjima khadija tace shikennan lubabatu tawuce tana dingishi khadija tabita dakallo cikin tausayawa tajuya dakinta

Lubabatu dasauri ta isah bangarenta tayarda battar tacire kayanta takulle daleda tafada toilet takwarawa jikinta ruwa

Tasa so so tayita darzar jikinta saida tayi sabi goma shabiyàr sanan tafito daure da towel tana tsane jikinta

Aranta tace shegen yaro yatsula fitsari gashi yabatamun tsari dole sainakarbo wani kuma taja tsaki badaihakan nasoba

Tasoma duba jikinta ainasan babu abunda zaisameni tunda nawanke tàsau kàrdà ajiyar zuciya saiyanzu tajisanyi aranta ganin tawanke maganin kuma bataji wani sauyinba"""
Ajikinta kwanciya tayi tanata yan tunani harbarci yadauketa" bata farkaba saikarfe biyu qalau tatashi tayi" wanka tasauka taci abinci alokacin labila tadawo tazauna cikin falon suna kallo har Dare bataga komai ba saikawai tasaki ranta dama tasan dakyarne idan aikin bokan nan zaiyi kawaidai yacimata kudine abanza

Taresukayi lunch dadare bayan suntaba yarfira kowa Yakoma dakinsa yakwanta""


Suna kwance Usman yana wasa da gashin kanta yakirah sunanta" ta amsa yace albishirinki"" tace goro fari Kal yace nashiryamaki tafiyarki Niger gobe kuma nasanarda"wani abokin kasuwancina dazaran jirginku yasauka zaizo yadaukeki duk inda zakuje taredashi zakuje banason kisha wahala kafin kugane inda take

Khadija tace kamanta gidan sarautane aibazai boyuba"" yace hakane Amman aikince batagidan tunda bayan barinta nandin bagida takomaba

Khadija tace hakane kam Amman najidadi sosai mijina""zanyi kewarka yace bakiji mamaki danasauya ra ayiba nantake??? Tace najimana Amman bankawo komai araiba

Yamurmusa tafiya takamani gobe kuma sati daya zanyi america zanje akan harkar da zamuyi dama banafadamaki munyi bakiba??? Khadija tace ah yace akwai tattaunawarda zamuyi sunason kafa company a kano shine zamuyi hadin guiwa komadai yamukayi idan nadawo zakiji tace to Allah yabada sa a yace Ameen Tonaso najedake saidaikuma wajen maza zasuyi yawa danba hotel za azaunaba shiyasa kawai nacebari nashirya maki kiwuce nima saina wuce""

Ammani saida yamma"" jirginmu zaitashi gobe warhaka kina niger ko???


Khadija tarungume usman cikin jindadi damurna tasomayimasa kiss tatonowa kanta dankuwa shimai gabadaya yayi"""

********************************lubabatu ta sakeyin wankatabi lafiyar gado

Misalin karfe dayan dare lubabatu tasomajin kaikayi Cikin barcinta tasoma sosawa cen kuma tasakejin wani gurin yasoma kaikayi cikin barcinta tahau soshe soshe cen taji kurji yafito"" aizunbur tamike zaune tasoma duban jikinta duk inda taji kaikayin tasosa ga kurjinan yafito hankalinta yayi mugun tashi tanajin wanigun yana kaikayi Amman taki sosawa kaikayin yayi yawa batasan sanda tahau sosawaba

Kuma idan tana susarsu wani dadi takeji gabadaya jikinta Yakama yam yam yam idan tasosa nan sainan yakama tazama kamar mahaukaciya dagudu tafada toilet ""'tahada ruwan zafie tawatsawa jikinta saitaji sauki sauki tagoge jikin tadawo takwanta
Kwanciyarta keda wuya gabadaya jikinta Yakama kaikayi"" harcikin kai"""

Lubabatu barci ya gagareta takoma gefe tanata kartar jiki kamar maiciwon kazwa""


Aisha✍🏼
[3/29, 8:28 PM] YAYA HAYAT: ☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 116 · 0% Book details