← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 23 OF 121

chapter 26

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Murmushi yasaki maidan sautiii yace nashiga tara yanzun har ammanta dani ba aje ko inaba anya kinason zumuncin nan yadaure kuwa"""

Gabantane yafadi karfa garin jan ajinta ta lalata komai""" tayi saurin taran numfashinsa tace bahaka bane uncle kaga aibansan nomber nakaba kuma kasan waya yana sauyawa mutane murya dat way banganekaba!! Amman kayi hakuri

Ajiyar zuciya yasaukar wacce har lubcy tajiyota yace najisanyi araina"" itama murmushin tayi"" sukataba firah daganan sukai sallama

Lubcy tamkar tazuba ruwa akasa tasha Dan Murna"dole"yau taturàwa *hatsabibin boka* kayan aiki nagodiyà!"""
daren da itah dashi kasa barci sukayi kowa yana tunanin dayansa Usman jiyake tamkar kirjinsa yafaso zuciyarsa tafito saboda tsabarso nda yakeji nata yanahudashi"""

Kwance take cikin dakinta tana danne danne dawaya saiga kiran Usman yashigo"" da murmushi tadaga tareda sallama daya bangaren ya amsa""

Yace gani akofar gida"" tawaro ido harkazo??? Harararta yayi kamar tana ganinsa yace dolekice harnazo danke bakidamu da niba nida nadamu dake darenjiya kasa barci nayi"""

Tarike baki yihakuri uncle bawai haka nake nufiba ganinan fitowa"" takashe wayar akahau safe safe da feshe feshe saigata tafito das da itah tasaka hijabinta tafita""" mom dinta tanacikin falo zaune tace mom nayi bako kibawa kande kayansha takaemasa muna falon bakiii

Tawuce abunta" yanajingije jikin motarsa yakurawa kofar gidan ido yanaso kawai yaga bullowarta"" kirjinsa sai harbawa yakeyi dasauri dasauri yakuramata ido yanda take tafiya tamkar hawainiya komai nata tsaf

Kamar yanda yaraja.a akallonta itama haka shigarta yau Tayimasa kyau yau kananun kayane ajikinsa sabanin jiya dayasa manyan kaya idan kaganshi wlh koda anrantsemaka bazaka yarda yatabayin aureba sai idan kaganshi da matar kakuma tabbatar lallai itace

Damurmushi takaraso inda yake tagaidashi"" tace karaso ciki sukajerah harcikin falon bakin"" tazauna nesa dashi suka gaisa""" yace badadewa zanyiba zuwanayi kawai mugaisa zanwuce

Sam bataji dadiba Dan fuskar tama. Tanuna hakan cikin sanyin murya tace sai yaushe kenan?? Nasan dakyarne idan zakasake dawowa legos tunda bawajen zuwanka bane

Yayi murmushi yanawasa da key din motarsa yace zancen baya kikeyi aiyanzu zuwa legos yazama dole dankuwa nayi babbar mantuwa acikinta

Tace mantuwa?? togashi baka fitaba kakoma kadauko mana"" murmushi yasaki maidan sautiii yace kinaso ayimun ihu ace nasaci abunda banawaba!! zandauka Amman bayanzu zanjirah har abun yaxama mallakina

Tace inamaka fatan alkhairi""yace nagode daidai mai aikinsu tashigo dauke datire cike dakayan motsabaki na marmari dakuma danbun nama"" saida ta aje taduka tagaisheshi """

Ya amsa cikin skin fuska"" zatafita yakirata kudii yaxaro cikin aljihunsa zasukai dubu goma yabata"" taki karba saida yamatsa mata sannan takarba tayi godiya""

Bayan tafita bajimawa yaduba agogo yace yakamata intashi haka"" karnayi dare ahanya"" gashikuma ban gabatar maki dakainaba""

Nasandai bakimanta sunanaba"" inaxaune a kaduna yanzu haka anan nake tafiyarda harkokina Amman iyayena akano sukeda zama

Mahaifina Allah yamasa rasuwa inada kanne biyu kubra tayi aure sai Hafiz nataba aure karkiyi tunanin ni saurayine fuskarsa cikin murmushi yafurta hakan""

Yanisa Amman Allah yadauki abarsa tatafi tabarni dayarona daya kaleed tuni idanuwansa suka koma jajaye yace inasonsa sosai fiye dakomai arayuwa banajin zanso wani Abu samadashi

Idan naganshi yana debemun kewar meenal azuciyata"" banason abunda zaitabashi komai kankantar abun" wlh lubcy yaron tausayi yakebani

Yanzun yana hannun mahaifiyata "" inason narikajiñ dimin jikinsa akusa dani nasan mom bazata banishiba tunda bansan yanda zanrika kuladashiba aganinta zanraba hankalina gida biyu

Shine nakeson nayi aure" kozansamu wacce zatakula damu dannikaina inabukatar kulawar""" yadago yakalleta yace kinji takai taccen tarihina aranta tace duk nasan wannan"""

Afilikuwa tace Allah sarki Allah yajikanta""" yace Ameen toyanzu mekikace??? Tadanyi yake tace nikuma mezance???? Yasake gyara zamansa yace tomenene amfanin sanardake tarihina???

Takada kafada maybe kasanar danine as ur friend""" """ yace ya inatubka kina warwarewa"" dariya takwacemata ganin yanda yayi maganar

Yace dolekimuñ dariya danbakyajin abunda nakeji gamedake""basaina tsaya kwanakwanaba agaskiya lubabatu tunda naganki naji nakamu dasonki

Sobana wasaba""" kuma aurenki zanyi bansaniba kozaki iyah aurena amatsayina nawanda yataba yin aure yakai karshen maganar yana kallon fuskarta

Tadanyi Jim yace please lubcy"" tarausayarda kai tace tokabani lokaci inyi shawara"" yayi saurin tarar numfashinta yace yanada kyau hakan amman nanda gobeko????

Tawaro ido gobe kuma??? Nanda satidaya dai"" bakiyabude cikin mamaki yace um lallai dasaurana bansamu shigàba""bari nasamu wajen zama a legos

Dariya tasoma tanarufe bakinta tace lala nina isah nafurta hakan ayihakuri to abani nanda kwana uku"" yace biyudai koshidai sainakai zuciyatà nesa danzata iya bugawa!! tace to abarshi biyun
.
Yace yauwa amman please karkice baxaki aurenibà"!! Danzan iyah shigawani halin"" tayi murmushi saidai kajini kasha lemun mana tayimagana tareda nunamasa tirenda kedauke dakayan marmari"""

Yace banajin zan iyah cin wani Abu harsainaji matsayina yayi maganar yanamikewa"" tace Amman kasandai banji dadiba acekayi bako koruwan gidanku baishaba

Ahakan nasan iyah matsayinà"" yace yihakuri kinsan bansan yanda akeyin zancenba Ashe idan kazo dole kasharuwa

Zansha Amman bayanzuba sainasañ matsayiña


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 23 · 0% Book details