← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 35 OF 121

Chapter 39

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Shirune yabiyo baya nayan dakiku sannan yakirah sunanta samrat tace na am"" yanisa maganafa nakeso muyidake bata wasaba

Tadan gyara kwanciyarta tace inajinka yace inaso gobe naturo gidanku maganar aure
Baki tarike tace dagaske tareda kalalo ido

Yalumshe ido yabude tamkar tana ganinsa wani nishadine yakeji aransa cen kasan makoshi yace dagaske kuma banaso auren nan yawuce sati daya inafatar dai ashirye kike
.tarausayarda kai sosaima kuwa"" indai katashi " yace wlh sosai natashi inamatukar bukatarki atare dani

Wani mugun dadi taji aranta tace maganina yayi aiki kenan"" dasannu zan mamaye zuciyarka"" yace yanaji kinyi shiru kodai barci kikeji???

Tace barcin lafiya inatare dakai kawai inaganin kamar mafarki nakeyi wainice zaka aurah"" yagyara kwanciyarsa yana fuskantar kasa yace kwarai dama kinsan kamai lokacine yanzun kokacin auren namu yayi bakiji yanda nakejinki arainaba

Lubcy wacce saboda tsabar tsurewa batasan sanda fitsarii yasoma bin kafartaba tunda Usman yasoma soyayya da suwaiba baitaba kiranta awayaba

Haka zakila baitaba furtamata wata Kalmar soyayya ba waisaigashi yautaji da kunnenta yana fadawa wata kalamai masu sanyaya zuciya Wanda rabon dayazauna yana koramata kalamai masu sanyi tun tana amarya

Nikuwa nace kece kiKajawo bakibashi abunda yakesoba taya zaibata lokacinsa wajen fadamaki kalamai bayankuma babu abunda kalaman zasu kareshi dashi

Shin mezaihana ke idan bakyada juriyar daukar lalurarsa kibarsa yayi aure mana yasamu wacce zata daukemasa lalurarsa

Amman kinhanashi kanki sannan kinhanashi aure kenan sokike yaje ya aikata zina bakyajin tsoron cutar zamanine???

Idan ma baikwaso maki cutaba wlh kincutardashi kinkuma zalunceshi saikisan amsarda zaki kare kanki ranar gobe kiyama agàbàñ mahaliççinmu

Dayawa akwai mata masu irin wannan halin musamman matanmu nayanzu inhar bazan baka farincikiba bazan hanaka aureba

Watafa tahanashi hakkinsa idankuma yace zaikara aure tace ba aimata adalciba"" aikoda yayi auren bazaiyi adalciba dan Allah jama a kunga laifinsa??? Wlh konine shi inda nakesamun kulawa nan zanmaida shekata kuma komai tanema zanyimata tunda nima tanabani abunda nakeso

Daga hakan saikuma tafara surutu tace anmaganceshi gashinan yanabin ta kamar bantee

Kullum yana manneda itah kamar jela dasafe bayafita aiki dawuri dadare kuma saiyadawo dawuri Amman bayahaka ranar girkina "" shinwai intambayeki wayajawo hakan??? Kome kikagani kece kikajawo kuma wlh dole kiga banbanciii
Kedakanki kinsan dole asamu banbanciii
Inakirah ga iyayena yayuna abokaina kannena mata muji tsoron Allah musan yanda zamutafida lalurar mazajenmu mukuma ji tsoron Allah musani komai mukayi sai antambayemu yazamanmu na aure gobe kiyama karmu manta da kwancin kabari tsallakar siradii sannan kuma karmu manta gida biyune alahirah akwai wuta akwai aljanna dole kasamu kanka adaya Allah yasamuna cikin tawagar yan aljanna Ameen Allah yasamufi karfin zukatanmu

Gabadaya hankalin lubcy yagama tashi jinyanda Usman yake furtawa wata Kalmar soba itaba wani wawan zagi tafurzar Wanda nikaina bansan ta iyashiba

Dasaurii tayunkura domin komawa aranta tana ayyana bamazata bari wannan tashigo gidan ba"" santsin tayes dakuma sanyin fitsarinda tasaki suka kwasheta tafadii jikake kuuuu

Tasaki wata kara wacce taisanadin dawoda hankalin Usman saman aikuwa dama bakin bene take hakan akafara gangaroda itah kamar kwallon magwaro sai ihu take tana kawowa kasa tabuga kanta dakarfe take tasuma kantaa yasoma fitarda jini daidai kawowar usman wajen

Sam baijiwani damuwa Aransaba kodan tabata masa raine oho"" atsanake yafita yakirah driver dakyar ya iya Kaita mota akawuce da itah hospital

Taji mugun rauni akai akayimatà gyara takuma goce akafa"akasamata Karin ruwa"" washe gari akagyara mata kafar

Usman yasanardà doctor idan dahali suwuce ayimata aiki kasar waje"" yace aikin mene ai matarka batada wata matsala
.
Yadubeshi darashin fahimta yace bakagane menake nufiba kwanaki sunsamu hatsarine akan hanya towajen gyaranne doctor yace tanada kari agabanta shine dalilindà yasaka takasa haihuwa dakanta

Yabata wadansu magani yace tayi amfani dasu kafin aimata aiki" doctor yayi murmushi yace tanada kari agabanta kuma harka kusanceta tasamu ciki???
.
Inhar agabanta yake bazaka iyah kusan tartaba Usman shiru yayi dankansa yadaure"" doctor yalura dahakan yace barinasa akoremaka kokonto

Nanyakirah wata nurse yace takiramasà doctor Asma.u tace to tafità babu jimawa sukadawo tare yayimata bayaniñ komai itama yanda doctor yafada hakan tafada

Yajuya wajen Usman yace kadaijiko"" yasake kallonta yace kije rum 11 kiduba mana saikizo kimana bayani tace okay tareda fita

Doctor yacigaba da rubuce rubucen shi Usman kuwa saisake sake yakeyi aransa yanata jinjina maganar doctor


Aisha✍🏼
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 35 · 0% Book details