← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 71 OF 121

Chapter 74

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Ahankali tataka harzuwa wajenda yake tsaye shikuwa haryanzu baidauke idonsa daga kantaba tafiyarta tamkar dawisu natsuwarta kalamanta komai natadai yana matukar burgeshi

Ko amafarki baitaba tunanin wai zaitaba soyayya dawataba saigashi kwatsam ya afka kogin so kuma yayi nitso tayanda baxai iyah fitaba

Da tsadadden murmushinta Wanda yake matukar dimautarda Usman tayi sallama dakyar ya tattaro sauran natsuwarsa wajen amsa mata sallamarta

Tace inawuni dad"" yadan gyara tsayuwa sanann yace lafiya qalau mom" dasauri tadago takalleshi batareda tayi maganaba"" yadaga mata gira yace yes indai bazaki kirani Usman ba nikuma mom zandinga kiranki dashi

Bakinta tadafe 🙊Dan Allah dad karufamun asiri dawanne bakin zankiraka aikuwa danayi rashin kunya takai karshen maganar tana kallon kasa

Murmushi yayi maidan sautii yasake gyara tsayuwarsa yace yayammu yace bakida lfy??? Kaita gyadamasa yace shine jiya akaki daga wayata wlh duk hankalina yatashi inata tunanin kobabu lafiya

Shiru tayi cikin tsokana yace khadija meyake damunki?? Shiru taimasa saida yasake tambayarta tace bakomaifa dad

Yace badaikiso insani ai yayanmu yafadamun"" baima karasa rufe bakinba tace nashiga uku mekuma yafadamaka???

Yanda tayi maganar tanaware ido tayi matukar burge Usman yasoma dariya haryana tafawa"" ido takuramasa talangwashe kai sai murmushi takeyi gaskiya dad kyakkyawane inama nice yafara aure danasan nahuce takaicin soyayya indai nasameshi

Yatsagaita da dariyar yana kallonta Sam batasanma yana kallontaba saida yakada yatsunsa sukai kara sannan tadan zaburah

Tanoke kanta tana Sosa kai alamar jinkunya sosai taji kunya dayakamata haka tana kallonsa""

Murmushi ya sakeyi yace toyajikin naki inafatardai kinji sauki??? Tasake gyada kanta yalurah sosai khadija tanada matukar kunya "" ganin firar tasu kamar atakure take saiyace tunda batada lafiya takoma gida shizai wuce wajen hajiya

Tace masa to Allah yakiyaye hanya"" tawuce gidan tsaye yake yana kallonta harta shige "" yasaukarda sassanyar ajiyar zuciya"" motarsa yabude yadauko siyayyarda yayi mata yabawa yaro yashigar matadasu

Yashiga motar sa yawuce "" koda yashiga gidan hajiya lokacin suke break yana yin sallama abdulmajeed yataso dasauri yarungumeshi yana gaidashi

Yashafa kansa cikin fara a yace katashi lafiya??? Kaiyagyada masa yace Amman jiya Anty saida akamata allurah yace dagaske?? Amman ba afadamun ba

Yayi maganar yana karasawa saman dinner yagaida hajiya ta amsa cikin sakin fuska labila ma tagaidashi ya amsa yayimata yajiki tace taji sauki sosai"" dama bawani ciwo bane hajiyace tatashi hankalinta hajiya tace yaunaji lalata nicema natashi hankalin nawa bayan kukanda kikaitayi kinacewa akiramaki dad"" dariya labila tayi tace aini bansan Yar tsohuwar nan tanasonaba sai ranar""

Abdul majeed yace tafisona danni idan nagirma mota zansiya mata!" Suka kwashe da dariya labila tace sannu sarkin soyayya kaikuma mezakayi da tsohuwa??? Kowa yana yayin sabon jinie
???

Yace nidai inason abuta tunda tanafita dani unguwa"" sukasake darawa "" hajiya tace kai maigidana kyaleta zauna kaci abincinka"" karka makara kara labila sai anjima kadan zata tafi""


Usman yace tonima asammun abincin banci komaiba wlh anayin sallar asuba nataso"" labilace tasoma zubamasa ""

Hajiya tace kaikuma lafiyarka wannan uban sammako??? Yakarbi cup din tea daga hannun labila yace hajiya wannan tambaya hakafa??? mutum yanada uwa sukutum agari atambayeshi danyayi sammako danyaganta""

Konayi laifine yayi maganar yana kallon labila tace inafa laifi dadyna ai zumuncine kasamu lada maitarin yawa

Hajiya tamere baki tace saikuje kufadawa wani badai niba kadaisan abunda yakawoka"" 'Usman yakurba tea yana dariya ciki ciki yace hajiya gaskiyar kenan

Yajuya wajen Abdul majeed kaiyi sauri kashanye inkaika dagacen inwuce yau wlh aikine dani office din nan"" hajiyadai batace komaiba""

Labila tace dad bazakaje wajen sahiba taba batada lafiya"fa" ashagwabe tayi maganar abdul yayi kududum yace me dady zaiyi wajen kawarki

Yakalli Usman yace nima jiya ai abokina baida lafiya Amman bakaje ganinsaba sai Kawar Anty"" kamar zaiyi kuka""

Usman yashafa kansa yace aibaka fadamunba danaje ko yarona maza dauko jakarka muje"" Abdul majeed yaruga shikuma yamike

Labila tabishi da kallo tace kai daddy yanzun bazakaba kabari driver yakaishi mana kaisaikaje"" yakalleta yana murmushi yace Ashe yayanta yazo???

Tace yakirakane""" daidai fitowar Abdul yamikamasa jakar yagoyamashi itah yace cen nafara zuwa ai"" yakai karshen maganar yana kallon hajiya takasan ido yana dariya kasa kasa

Murmushi kawai tayi tana girgiza kai yace mujeko nagoyamaka"" yarike hannunsa mujeto daddy"" yace haba Abdul aikanajirah nagama magana da hajiyata ko

Yakalloshi da sauri hajiyarka??? Wlh hajiyatace"" yace najito hajiyarka"" yayimasu sai anjima sukai masa Allah yakiyaye yawuce yana dariyar Abdul majeed


Da dare muktar yasanarda kawu ya amince khadija ta auri dadyn labila bakaramin jindadi yayiba""" yayita sakamasa albarka washe gari Yakama hanyarsa yakoma skull

Usman yanadan zuwa kano akai akai"" haryanzu uwar gayyar batasanda komaiba gefe daya sunfara zana jarabar karewa balaifi sunawaya duk da haryanzu batasakin jiki suyi firah""

Usman yaturoda magabatanshi anzauna akayanka sadaki yabiya ansaka rana wata biyu"" kenan bayan sati biyu da kammala jarabawarsu


Aisha✍🏼
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 71 · 0% Book details