← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 100 OF 121

Chapter 99

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Tana fitowa sukayi ido hudu da Usman bakinta tadafe tana kuka tana dariya alokaci daya shikuma murmushi yakeyi tace dad Kaine yaushe kazo nan wayafadama ina nan??? Yace haba Deejarh duk inda kike aidole zuciyata tasanardanie

Kizo maza mubar dajin nan mugun dajinie"" batareda shakkar komaiba tatunkaroshi gabanta taji yayanke yafadi saikuma tatsaya chak

Zuciyarta tanacewa wannan ba Usman bane kaitasoma girgizawa tana jadabaya """ cikin sansanyar murya yace menene kuma khadija kizo gareni mana kinkuwasan halinda nakeciki sanadin kewarki

Cikin daga murya tace karyane kaiba dady bane kaiwayee? Meyakawoka wajena "" meyasa kakeson cutardanie""

Jinhakan keda wuya kawai sai aljanie hayyanul zairi yarikida yakoma katon jemage"" mai fika fiki sosai yayi mamakin da khadija ta iyah ganeshi dariya yasoma kyakyatawa wacce tasaka khadija Dade kunnuwanta saboda karar muryarsa dakuma rukukinta yatsaya da dariyarsa yace ke yarinya baki isah kisan koni wayeba abudaya nakeso kisani kafin nashanye maki jini shine nine nan zanzamo ajalinki

Yau ina wacce zata taimakeki kikirata kokuma kikirah Wanda zai ceceki daga hannuna yauba makawa zakikwana lahirah

Aini taimakoma akamun yauzanyi murna bayan kema Ashe harda kari nasamu yau zanmore dajikinku

Khadija tace karyane jinina bazaitaba zama abincinkaba in Allah yayarda yaunice zanga karshenka Allah bazaitaba baka sa a akainaba

Tanagama fadin haka tajuya daniyar komawa cikin gidan kamar walkiya yasha gabanta babban kuskurenda yayi kenan shaf yamanta khadija tanayin azkar dasafe babu wani mahalukin aljaninda ya isah yarabi jikinta batareda yakoneba

Iska yazama tayanda bakaganin komai face iskan yakai hannunsa yadankota alokacin khadija tasomayin addua dakarfi

Hayyanul zairi yarigada yariketa wata wahalalliyar kara yasaki yafada gefe daya hannunsa yasoma dayewa kamar yasaka hannunsa jikin dalma tuni Dan fiffiken dayake gadara dashi yafincike

Hakan baisa ya daddaraba kawai yataso gabadaya yayi mata baran makauniya yasake kwamtsa wata uwar kururuwa cen nesa da ita akayi wurgidashi take dukkan ilahirin jikinsa yasoma cidawuta

Khadija haryanxu batadaina addua ba cen taji iska yana kadawa maidadi ahankali tabude idonta tayi Arba dashi cen yashe bayako motsi wasu hawaye masu zafii suka saukomata mararta taji tafara ciwo

Dakyar ta iyah daga kafa zuwa cikin gidan tanajan kafa tanashiga falo taduke tasoma kuka danciwonda bata tabajin irinshiba""" nantakama murkususu

Haryanzu bakinta baidaina ambaton sunan Allah ba""Allah yabata ikon yin numfashi maikarfi saiga kan danda yafito sallama tajiyo cikin gida duk da bushi bushi takeganie

Wata dattijuwa ce tashigo dasauri takaraso wajen tataimaka mata tajaye yaron saigakuma wata dabuwar nakuda bajimawa tasake suntulo wani Dan wannan tsohuwar tayanke cibi tawanke yaron tahadamata ruwa tayi wanka

Duk wani taimakonda za ayiwa maijego itah tayimata tea tahadamata maikauri tasha takwanta babu jimawa barci yadauketa

Saidai tafarka tana tunanin mafarkinda tayi wai wani aljani yaso kasheta Amman sunyi fada baici nasaraba kuma tahaihu harwata mata tataimaka mata tatuno damaganar aljanin dayake cewa yasamu Karin Jinie

Hannu tasaka tashafo cikinta kwalelen batagama rufe bakiba taji cikinta wayam dasauri tamike daga kangadon tace innalillahi badai shiru tayi saikuma tasoma dariya ganin jarirai guda biyu cikin shigarsu ta alfarma kowannensu hannunsa yana bakinsa yanata tsotsa

Dukawa tayi takuramasu ido kamarsu daya da sahiba kenan Usman sukabiyo murmushi tayi najin dadi kenan ba mafarki tayiba Alhamdulillah

Dayan tafara dauka takurama ido tsirarun hawaye suka sauko sai akan kumatunsa saiyabude idonsa yana kallonta yana lumshe ido kamar yasan dalilin kukanta

Saman gadon takoma takwanta tarungumesu tafashe dakuka kowanne uba zaiyi gurin a Haifa. Masà yaransa gabansa yakallesu yaga kyautarda Allah yayimasa

Tashare hawaye kutaku kaddarar haka tazodashi babanku baisan mada cikin kuba saiyanzu take tuna in tsohuwarda ta tai maketa kowacece

Tana kwance harkusan magrib saiga dattijuwar tadawo tasake hadamata ruwa tayiwa yaran wanka tashiryasu takawomata lafiyayyen abinci yaji kayan yajie saida tagama komai tatafi

Khadija dakanta tayiwa yaran huduba" takirasu da sunayensu hassan da husainie yaran akwai hakurin yunwa danko alama basuyi kukaba saiwashe gari da tsohuwar tadawo ta umurceta data basu nono

Kullum haka takezuwa harsukai sati ranarkuwa tana zaune dasafe tsohuwar tazo bayan tagama shiryasu khadija tace innah matar takalleta da murmushi tace na am"" tace inaso ingodemaki akan taimakonda kikamun

Tayi murmushi tace bakomai yata aiyiwa Kaine"" khadija tace innah wanne gida kike?? Tasake murmusawa tace Niger nake kokintaba zuwa cen ne???


Khadija tace ah ah kafin tasake jehomata tambaya hartafita hakadai sukacigàba dazama damatar hartayi arba in

Tasoma hadamata maganie akwai nasha nawanka dakuma nahayaki cikin sati biyu khadija tagoge tayi haske fatarta sai sheki takeyi

Su hassan sunada wata bakwai sannan dattijuwar nan tayiwa khadija sallama tace itah zatakoma khadija tatambayeta sunanta murmushi tayi tace Hauwa u kafin khadija tayi magana dattijuwar tafita khadija tanata nanata sunanta acikin ranta itakuma wannan aljanace ko mutum???

Amman naga aikinta kamardai irin na mutane sosai khadija tasaba da itah duk da bawai fira takeyi da itah ba Amman tanajin dadin zaman gidan tunda akwai mai tayata zama kuma koda yaran tana rikemata itakuma tayiwa daya wanka sa arta daya basuda kuiya basa kuka yanzun harsun soma tashi tsaye batareda sunrika wani abuba"" khadija idan tana karatun Qur anI saitaji sun natsu kamardai sunsan abunda take karantawa "" bayan watanni biyu datafiyar dattijuwar alokacin su hassan sun iyah tafiya idan kagansu zaka rantse da Allah sun shekara biyu domin jikin girmane dasu gakuma wayo dansun fara magana


Khadija Sam tasaba dazaman kadaicin itah Kadai acikin gidan zaune take cikin falon tazaunarda su hassan tanayimasu karatun qur ani

Sukaji anyi sallama Kusan tare suka kalli kofar danganin maiyin sallamar wannan aljanarce tashigo cikin murmushi dakuma fara a tanasanye cikin lifaya fara tayafa farar alkibba""" khadija bazata taba mantawa da fuskar taba ta amsa sallamarta tatashi dasauri ta isah inda take tarungumeta saikuma tafashe dakuka


Hannu tasaka tana bubbuga bayanta alamar rarrashi cikin kuka tace dan Allah kimiyardani gidan mijina nagaji dazama wajen nan "" tajayeta daga jikinta tariko hannunta suka dawo wajenda su hassan suke tazauna tana kallonsu sannan tayi murmushi tamiyarda kallonta kan khadija tace yagidan ya yaran""" ahanzarce tace qalau muke Dan Allah kifadamun yaushe zaki kaini gida bansan halinda yan uwana sukeba da mijina atakaice inason Yayana suga mahaifinsu

Tanisa tace hakane zaki iyah tambayata nikuma ashirye nake inbaki dukkanin amsoshin tambayarki"" Amman kidaure kiyimun tambaya daya daya domin insamu damar baki amsa gamsasshiya""

Khadija tace meyasa aka kawoni nan??? Aljanar tace ai ina tunanin kinsan wannan amsar Amman zansake tunamaki ankawoki nan ne domin akasheki hasalima banan yaso yakashekiba zaikaiki duniyar aljanune datake kasar Iraqi wajenda babu wani mahalukinda zaije cen yadawo daransa saiwanda Allah yanufa kuma yakeda Karin kwana anan gaba

Lokacinda yaratso tawannan jejin sakamakon Neman tsarinda kikayi ga Allah lokacinda kika farka shiyasa yafado daga sama kuka fado wannan jejin

Khadija tace nandin wacce kasace??? Tace kasar sin"" inajin kintabajin labarinta ko acikin tarihi"" khadija tagyada kai tace tome naimasu sukeson kasheni???

Aljanar tasake gyara zama tace yanadakyau kisan asalin tarihin shugaban wanan aljanin wato *hatsabibin boka*

Khadija tace menene alakar tambayata dakuma wannan bokan ina Neman tsarin Allah daga sharrinsa dashi da shaidanun aljanunsa

Aljanar tasake murmusawa tace tambayarki tanada alaka da labarinsa zaifi kyau kisaurareni kiji ainahin koshi waye daga cikin labarinsa zakisamu amsar tambayarki shiru khadija tayi batace komaiba

Aljanar tasoma kamar haka

Tarihin *hatsabibin boka* mukoma bayà wadansu shekaru Dari biyu baya anyi wani kasurgumin matsafi Wanda aduniyar lokacin babu wani boka mai tsananin tsafi dakuma siddabaru kamar shi sunan wanann bokan haiiiiranu wàsu suñamasa lakabida uban shaidanu👹👹👹


Aisha
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 100 · 0% Book details