← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 7 OF 121

Chapter 10

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Alokacinne akaraba girki" yakoma hannun lubabatu""
Habiba Sam takasa gane wanne irin aurene tayi gatadai batadawata makusa wacce zatasa namiji yaji baya sonta" batada matsala tabangaren kishiya saidai tabangaren miji"" sosai yakesonta kafin auren ammankuma gashi tunda tashigo gidan komai yadargwaje tarasa gane kuma dalilin yinhakan gashi tanada tsananin bukata zuwa yanzu tarame tafige tafita hayyacinta"""

Kwance take cikin falonta kasancewar yauma ranar hutuce yanagida Amman takasa fita domin ganinsa kawai zaisake tasomasa da bukatarta wacce tasan bazata samu maganintaba "" lallai tayarda akwai abunda yajefaruwa da itah cikinta taji yasoma juyawa tafara murkususu""

Tun tana kankujerah hartafado kasaa wata irin kara ta kwallah daidai shigowar hajiya lubabatu tazo kiranta suci abinci dasauri takarasa arude tadagota tana tambayar lafiya kafin tarufe bakinta jinine yasoma zubowa dakarfiii ta gabantaa""

Cikin tashin hankali lubabatu tace habiba dama bakida lafiyane???ina habiba tamatukar galabaita bata iyah kodaga kanta dasauri hajiya lubabatu ta kwantarda itah tafito dasauriii zuwa kasan

A firgice tana kuka yana ganinta yamike yana tambayarta lafiya hajia??? Cikin kaduwa yaji meyafaru tace munshiga uku habibace ba lafiya

Kafin tarufe bakinta tuni yahaurah saman baimabi takan na urarba tasaman benen yataka tuni hajiya lubabatu tabi bayansa koda suka karasa hartasuma ga jininan yanata malala"" gakuma wata karamar halitta wacce batawuce girma Dan kadan gareba"" take jikinsa yahau rawa duk da abunda yagani Amman hakan baisa yadamuba ya ciccibeta duk dajinin dasauri yasauko kasa hajiya lubabatu tana bayansu sai kuka takeyi

Tunkafin yafita yasoma kwalawa driver Kira"" dasauri yafito jinkiran jikinsa yanarawa Dan dagajin kiran yasan ba lafiyaba"" ganinshi damaidakinsa ahannu yasaka yabude masu Mota dama ashirye take"" akasakata taresuka dunguma har hajiya lubabatu zuwa hospital"" emergency akawuce da itah kaitsaye bakin kofa aka dakatar dasu aka hanasu shiga"""

Dagashi har hajiya kaikawo sukeyi awajen kowanne kagani kasan yanacikin tashin hankali tsayin awanni biyu likitan yafito dasaurii alhji yatareshi "" saidai yadagamasa hannu yawuce haryana hadawa dagudu""

Zuwacen yadawo yashiga dakin"" ansake shude wasu awannin saigashi yafito
Alhaji yatareshi tareda hajiya lubabatu harsuna hadabaki wajen tambayar yamaijikin???

Zufan kansa yashare yace kukwantarda hankalinku insha Allah zatasamu lafiya"" yanzudai muna bukatar jini cikin gaggawa"" kafinma yarufe bakinsa yace muje a auna idan nawa zaiyi"" hakan kuwa akayi saidai jininshi baiyiba

Adole akakirah yan uwanta mahaifiyarta "" dakuma yayyunta""" su ukune kowanne akadibi gorah biyu ajikinsa"" take akajonamata anasaka jini jinin yanafita"""

Harzuwa dare babuwani haske hakazalika sunkasa tsayarda zubar jinin"" yanda yakezuba zuba banawasaba hakan yasaka sukanemi Karin wani jinin"" duk dayana fita idan ansakamata""

Yan uwanta basuda wadataccen jinin gashi har andibi gorah biyu dagahakan baza sake dibaba"" gashi duka jininta ya tsiyaye"" hajiya lubabatu sai kuka take tace aduba konata zaiyi itakam bataso tarasa kanwarta

Likitan yatausaya mata sosai yace saidai hakuri hajiya ba adiban jinin mace"" cikin karaji ta chakumo wuyansa tace inaruwanka jininka konawa

Tasakeshi cikin kuka tahada hannuwanta gida biyu Dan Allah doctor kataimaka mana wlh koda zanrasa raina tasanadin dibar jinin nawa"" wlh nayarda Amman banaso kanwata tamutu

Jiki asanyaye yagyada kai ganin kowanawajen yazubamasa ido"" take aka auna jininta baidakomai"" akasoma diba anasakawa Habiba"""likitàn yafita mahaifinta dawani kaninsa sukabishi abaya"" zuwa office dinshi"" mahaifintane yasoma tambayarsà meyakedamuñ yarsa???
Yayishiru dagabisani yace barine tayi" cikin kaduwa mahaifinta yace barin lafiya watadaya da aurentafa??? Yajinjinà kai tareda turomasa takarda gabansa yace sakamàko yanuna tanashañ kwayoyin zubarda cikine babisa ka idaba shine yajawomàtà wannan matsalar

Kafin yarufe bakinsà alhaji yashigo dasauri yace doctor kataso jinin ya facce kusan taresukà mike dasauri zuwa dakin harsunà hadawa dagudu

Sannu ahankali tabude idonta takurawa gadonda hajiya lubabatu take kwance ido sirarun hawaye suka saukomata

Take tasoma Kalmar shahada"" idanuwanta sukai sama take Na urah tasoma kara"" daidai shigowar su doctor yakarasa wajentà yayi yan aune aunendà zaiyi yagirgizà kai

Yacire abun Karin jinin tareda Na hajiya lubabatu yarufe mata idonta yaja kallen yarufeta"" gabadaya dakin shisuke kallo Dan haryanzu basu fuskanci meyafaruba

Yajuyo dakallonsa wajen alhaji yace saidaifa kuyi hakuri Allah yakarbi abarshi""

Daga haka yajuya yafita hajiya lubabatu tasoma kururuwa tana wayyo itah tabani mahaifiyar habiba saman gadon lubabatu takoma tanabata hakuri suka rungume juna sunata kuka""" akarasa Wanda zai rarrashi waniii

Tsayin mintuna talatin mahaifin habiba dasauran yan uwa da sukazo dakyar akasamu su hajiya lubabatu sukai shiru

Kanin Mahaifiyarta yakalli alhaji yace waimenene musabbabin ciwon nata""??? Kodama tadade batada lafiya???

Ciikin sanyin murya yace shima baisaniba yadaifàdamasu iyah abunda yasani ahakan"" mahaifinta yace sai asamo mota suwuce gida babu wani bata lokaci akadauki gawar zuwa gidan iyayenta""


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 7 · 0% Book details