← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 72 OF 121

Chapter 76

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Bayan motar tatsaya inda ake ajiyeta driver yafito yabude masa kofa Amman Sam hankalinsa baya jikinsa" saida yakirah sunansa sannan yafarga""

Yadan murja idon sa kamar Wanda yayi barcii"" dauko kayansa yayi da card din yama driver saida safe"" yawuce cikin gida jiki asanyaye

Koda yashiga bata falon kasa yasaukarda wata gajiyayyar ajiyar zuciya"" Allah yasama tayi barci sai inbari saigobe nikuwa abun ma dariya yabani to aikogoben kafada abunda kake gudu zaifaru bafasashi za aiba kaidai kawai kafada musam makomarmu

Ahankali yasoma hawan step din baima tsaya hawan na uraba zuwa sama tadaukeshi tsawon lokaci kafin yakai"" bangarensa yanakaiwa lubabatu tana kawowa dantayi mamaki yau yadawo dawuri

Dan tunda yahadu da khadija baya dawowa saiwajen karfe Tara alokacinne yake kiranta danbadama yayi agaban uwarguba! Au sorry🙊 uwargida tunda labila tace basuyardaba tasanie

Yana ganinta yatattaro sauran natsuwarsa yasamu yasakar mata lallausan murmushi itama tamiyar masa da martanin murmushinsa """

Tace sannu dazuwa yauwa yagidan yyi maganar yana turah kofar dakinsa tabishi abaya "" tace gida saitarin kadaici ai kwanan nan nakeson naje yawon kasa dani da su sajida"" yace ko??? Tace eh yamere baki baice komaiba

Tace bakace komaiba"" yana rage kayan jikinsa yace Toni menene nawa ??? Da inaso dabanaso inhar kinaso saikinyi ra ayinki nasanma kina fadamunne dankar naga bakyanan Amman banda haka watarana aisaidai nabuda ido bangankiba""""

Maganarsa saima tabata dariya ganin tana dariya kamar wacce kare yaciza yakalleta baki bude yace wannan dariyar haka kumafa???

Tatsagaita da dariyar tace tomekuma nayi dankawai nayi dariya??? Yace bakiyi komaiba Amman kisani ire iren wan nan dariyar batada kyau acikin addini manzon Allah yace tana kashe zuciya tanakuma rage imani" jibifa harda hawaye kike shaidanne yakee irin wan nan dariyar"""

Take annurin fuskar lubcy yagushe tace kana nufin nidin shaidance???? Yakwalalo ido yace wani banfadaba baza aji mutuwar sarki abakinaba""

Karki karagaba kifada Allah yabaki hakuri bahakan nake nufiba yadauki towel dinsa yashige bandaki yarufo kofa anan yabarta sai nanata maganarsa take aranta

Haryafito batako motsaba""" yana taje sumar kansa' yadan kalleta tajikin miro yaga yanayinta yasauya"" takowa yayi kusa da itah yazauna yana kallonta yace uwargidan Usman badai maganar da nayi dazuce tasosa rankiba????

Saurin kawarda damuwarta tayi takirkiro murmushi la bakomai dankawai kasanarda ni gaskiya dannakiyaye gaba

Aini nagode Allah dayahadani dimiji irinka wasu mazan zasuga matansu suna aikata badaidaiba Amman saisu kyalesu kodan kada ran matar yabaci kodan wani Abu
Tace nagode kashirya abincinka yana jiranka"""yamike bari nashirya amma kafin Naci abinci akwai wani albishir dazan baki

Nantake lubabatu tawashe baki tace toshikenan bari nakawo abincin nan"" tayi maganar tana mikewa tasauka waje bayan yashirya yazauna jiranta saigashi tashigo dauke da tiren abincin ta aje kasa""" cikin zumudi tacemasa tofadamun"""

Yace yanzu kuwa"" hannunta yajawo zuwa saman gadon yace zauna bamusu kuwa tazauna""yana fuskan tarta yace albishirinki

Tace goro fari kalkal"" ya murmusa Usman dinki yasamu wacce zai aurah!!! Kamar saukar aradu haka taji maganar batayi saurin saita natsuwarta ba cikin tashin hankali Wanda batasan yabayyana afuskar taba tace ban ban banfahimcekaba wane Usman din????

Yace kinada wani Usman dinne bayan wannan Wanda yake gabanki??? yakalleta damamaki ganin yanda har idonta yasauya"" yace yadai lubabatu kobakiji dadin furucinaba ne??? Kefa kike matsamun kullum akan nanemi mata na aurah inaki kinmanta harfushi kikeyi idan nace nida aure har abada yalokaci daya nafadamaki abunda nai tunanin zaisanyaki nishadi saikuma naga sabanin hakan???

Saiyanzu lubabatu tasan taso tabka kuskure dayake yarduniyace ta iyah tsara magana "" tayi saurin boye damuwarta takirkiro murmushi tace wlh nafika jindadin wannan ranar abunda yasa kaga nashiga damuwa inatausayin Kane dakuma kaina danakasa biyawa mijina da bukatarsa tsayin shekaru

Tanisa inajin tsoron Karka auro wacce zatazo ta tayarmaka da hankali narantse danaga tashin hankalinka nagwammace naga mutuwata!!!!

Wani dadine ya lullube Usman baisan sanda yamannata jikinsaba yana sakamata albarka"" tace bakomai dadyn Abdul"" nidai fatana Allah yabaka wacce zatadauki nauyin lalurarka kamar yanda kakeso Allah yabaka tagarii yace ameeen ameeen kamardai yanda yabani ke

Ta murmusa wanne gari yarinyar take??? batareda fargabar komaiba yacemata kano"" aranta tace munafuki 🙄yanzu dama zuwanda yake kano soyayya yake"" kafin tatambayi sunanta yacigaba sunanta khadija marainiyace
tace Allah sarki Allah yajikan iyaye yace Ameen jiki asanyaye

Tace inafatardai yan uwanta sunyarda dankar ayimana kamar nasauran dakanema saimunsarai da aure saikuma Abu ya lalace""

Yace ah ah sukam bazasuyi hakaba"" kafin tayi magana yadauko card din duka yamika mata yanacewa sauran kwana biyar daurin auren

Saura kadan lubabatu takundumo ashar"" takarbi card din jikinta harrawa yakeyi takurawa card din ido kamar maisabuwar makanta"""

Ga rubutu nan taryen taryen takaici baibarta karasa karantawaba"" tamika masa " Yace harkin kare??? Tace ah Allah yasanya alkhairi yace Ameen"" yakarbi katin""

Yace saikiyi list din abunda kikeso duka zanje dakaina insiyomaki"" dakayan dazakici biki"" tace habadai dawainiyar tayi yawa ai" gana fatenda amare zasuyi kuma gahidimarsu aisaina karamaka nauyi

Nadaigode babu abunda nanema narasa agidan nan"" yamurmusa nasanda haka Amman nasan baxaki rasa abunda kikesoba

Tace wlh bakomai saidai kayanda kawai za a baiwa yanbiki""" yamike daga saman gadon yace barma maganarsu nidagayau nakashe taron biki agidana

Damacen banaso Dan bidia ce kece kike kafewa saikinyi kuma dagakarshe kafin awatse sai anyimaki sata kidawo kinafada bance kigayyaci kowaba

Idankuma Mace takawo kanta nasa aka koreta karkiga laifina

Tace waishi wannan wanne irin tsarine yazodashi meyake nufi dahakan??? Ko anyisata aini akaiwa bashiba

Yazauna yasoma cin abincinsa baidamu data yardaba kobata yardaba danshi yasan matakinda zaidauka maigadi zaifadawa karyabar kowa yashiga gidan koda kuwa lubabatu ce tazo dakanta

Haryagama cin abinsa tana zaune saida yagama tamike zatadauki kayan yace xakidawo ko??? Tace meyafaru kana bukatar wani abune???

Yalangwashe kai kamar karamin yaro yalumshe ido yabude alamar ah""
Murmushi tayi tace tome kakeso??? Yace goron albishir dina mana"" kuma kinsan abunda nafi bukata ayanzu"" tagane inda maganarsa tadosa tace ayya gashi inafashin sallah""" yace kash!!! Tokitaimaka koyan dubarune kiyimun Dan Allah"""

Tace please baban Abdul wlh harda Dan zazzabi nakeji kafin zuwankane nadansha maganie kabari basaura kwana biyarba aini namatsuma amaryar nan tazo nahuta

Yayi dariya lallaima matar nan watakan harma gajiya kikai dani saikace wani maye"""😾 tana dariya itama tace kafadi sunanka aikai mayene Amman bamaicin mutaneba mayen........😂😂😂


Bata karasaba tasoma dariya yace najidai Amman babu Wanda yasan dahakan saike bayanke bawanda zaiganni yace inada lalurah saifa idan kece kika sanarda kawayenki

Tarike baki waceni dazanbude sirrina agun wasu banzayen kawaye"" ai idan nafada watama saita kwacemun kai""" yace kedai fadi ainasan kumata tunaninku ragaggene dazaran kunhadu waku waku mata zakuta bararda zance

Kuyita fadin sirrin mijinku mijinki koda katuwar loma yake wajen cin abinci baidace wata tasan yanda yakecin abinciba

Shimadayake bakomaiba ballantana abunda akeso yatsaya dagake saishi waihar kina iyah sanarda wasu kawayenki bakyako jin kunya waike wautarki aimatane yan uwanki

Allah yasanda hakan Amman ya la anci matarda take barbada sirrin mijinta gawasu mutanen"" haba Yar uwa lubabatu ma tasanda haka tana boyewa bata taba sanarda kawayentaba toballaike wacce bahalinku daya da lubabatu ba

Kodai kiyarda dahakan kidaina fadawa kowa sirrin mijinki kokuma muce lubabatu ma tafiki wlh"" karkimanta anason mace maikunya

Duk matarda batada kunya da itah da dabbobi daya saboda sune suke yawo tsirara suyi komai agaban kowa basajin kunya


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 72 · 0% Book details